Abba Ibrahim Wada" />

Manchester United Za Ta Sayi ‘Yan Wasa A Karshen Kakar Wasan Bana

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Ole Gunner Solkjaer ya bayyana cewa shugabannin kungiyar koda yaushe a shirye suke su bayar da kudi domin sayan ‘yan wasa a kokarin da sukeyi na gina kungiyar kuma ya bayyana cewa zasu shiga kasuwa domin kara karfi.
A farkon wannan watan ne rahotanni suka tabbatar da cewar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United za ta sayar da dan wasanta na tsakiya, Paul Pogba mai shekara 27 a duniya a karshen kakar wasa ta bana bayan ya tabbatar da cewa ba zai saka hannu kan sabuwar yarjejeniya ba a kungiyar.
Wannan na zuwa ne duk da cewa a ‘yan kwanakin nan tauraruwar dan wasan tana haskawa inda a wasan da kungiyar ta fafata na karshe-karshe ya bayar da mamaki sosai har aka fara rade radin cewa zai iya ci gaba da zaman kungiyar.
Har wa yau, Manachester United din ta rasa abin yi game da dan wasan Ingila da Dortmund, Jadon Sancho mai shekara 20, yayin da Ole Gunnar Solskjaer ya fi son Erling Braut Haaland na Dortmund din mai shekara 20 shi ma.
Sai dai abune mai wahala kungiyar Dortmund ta sayar da dan wasa Haaland kuma dole ne kungiyar ta dage akan dan wasan duba da yadda manyan kungiyoyi irinsu Real Madrid da Barcelona da Bayern Munchen suke bibiyar matashin dan wasan dan kasar Norway.
Solkjaer ya bayyana cewa akwai kudi a kungiyar kuma idan suka samu dan wasan da zaiyi daidai ba muradun kungiyar zasu ko nawa ne domin daukarsa sai dai ya ce dole ne su nutsu saboda ba zasu kashe kudi a inda bai kamata ba

Exit mobile version