Connect with us

WASANNI

Manchester United Za Ta Siyi Nebil Fekir Daga Lyon

Published

on

Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United tana zawarcin dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Lyon, Nebil Fekir, dan kasar Faransa wanda a kwanakin baya kungiyar kwallon kafa ta Liberpool ta kusa siya.
A watan daya gabata ne kungiyar kwallon kafa ta Liberpool ta kusa daukan dan wasan sai dai daga baya cinikin ya rushe bayan da shugaban kungiyar ta Lyon yafito ya bayyana cewa sun fasa siyarwa da Liberpool dan wasan saboda tattaunawa tayi nisa.
Liberpool dai daga baya takoma domin sake tattaunawa akan dan wasan sannan tace daga kan fam miliyan 55 baza ta kara komai ba saboda tagano cewa dan wasan yanada ciwo a lokacin da take gwada lafiyarsa.
Rahotanni dai sun bayyana cewa kungiyar Lyon tace baza ta rage farashin dan wasan ba daga fam miliyan 65 inda kuma daga baya shugaban kungiyar ya bayyana cewa akwai kungiyoyi da yawa da suke zawarcin dan wasan dan asalin kasar Algeria.
Kungiyoyi irinsu Real Madrid da Bayern Munchen duk sun nuna sha’awarsu wajen siyan dan wasan wanda ya jefa kwallaye 24 cikin wasanni 40 daya buga a kungiyar ta Lyon ciki har da gasar Europa.
Ana tunanin dai kungiyar kwallon kafa ta Manchester United za tayi gaggawa domin kammala cinikin dan wasan sai dai Lyon ta bayyana cewa duk wata tattaunawa sai dai a hakura har sai an kammala gasar cin kofin duniya sakamakon dan wasan yana kasar Rasha inda yake wakiltar kasar Faransa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: