Connect with us

WASANNI

Manchester United Za Ta Taya Willian Fam Miliyan 60

Published

on

Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta shirya kai ta yin kudi fam miliyan 60 ga kungiyar Chelsea domin siyan dan wasa Willian wanda yakeson barin kungiyar.
Mai koyar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Jose Mourinho ne dai yakeson aiki tare da Willian bayan da suka taba aiki tare dashi a lokacin da Mourinho yana Chelsea kuma ko a kakar wasan data gabata sai da United ta nemi dan wasan.
Sai dai itama kungiyar kwallon kafa ta Chelsea tana zawarcin dan wasan gaba na Manchester United, Anthony Martial wanda shima a satin daya gabata ya bayyana cewa yana son barin kungiyar ta bakin wakilinsa.
Manchester United ta yiwa Martial kudi fam miliyan 75 ga duk kungiyar da take son siyan sa sai dai kuma duk da haka Manchester United din batason siyar da dan wasan ga kungiyar da take kasar Ingila.
Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ma tana zawarcin Martial sai dai farashin da Manchester United ta yiwa dan wasan ya yiwa Tottenham tsada hakan yasa zasu hakura da zawarcin Martial din mai shekaru 22 a duniya.
Manchester United ta siyi dan wasa Fred dan Brazil dan kungiyar Shakhtar ta kasar Ukraine kuma ana ganin sabon dan wasan zai iya jan hankalin Willian ya amince da komawa domin ci gaba da aiki da Mourinho.

Advertisement

labarai

%d bloggers like this: