Mane Da Salah Za Su Halarci Taron Gwarzon Africa A Ghana

Mai koyar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Jurgen Klop ya ce martabawa ce Mohamed Salah da Sadio Mane su halarci bikin gwarzon dan kwallon kafar Afirka da za a yi a Ghana.

Muhammad Salah, dan kasar Masar da Sadio Mane, dan asalin kasar Senegal suna cikin ‘yan wasa ukun da ke takarar kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na 2017 da hukumar kwallon kafar Afirka, CAF za ta karrama a ranar Alhamis.

‘Yan wasan biyu za su halarci taron ne awanni 24 kafin Liberpool ta fafata da Eberton a gasar cin kofin kalubale na FA.

Klopp ya ce ya san mahimmacin bikin da kyautar ga ‘yan wasan, domin a lokacin da yake Borussia Dortmund bai hana Pierre-Emerick Aubameyang zuwa taron da aka yi a Nigeria ba.

Za a yi bikin zabar gwarzon dan kwallon kafar Afirka na 2017 a babban birnin kasar Ghana, Accra, inda Sadio Mane da Mohamed Salah dukkan su daga Liberpool da Pierre-Emerick Aubameyang na Borussia Dortmund suke takara.

Acikin watan Disambar daya gabata ne dai na shekara ta 2017 Muhammad Salah ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafar yada labarai na BBC na nahiyar Africa

Exit mobile version