Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool za ta daukaka kara kan haramcin buga wasanni uku da aka yi wa dan wasanta Sadio Mane bayan an kore shi daga fili a wasan da kungiyar tasha kashi a hannun Manchester City da ci 5-0.
An kori Mane, mai shekarar 25, daga fili a daidai minti na 37 da fara wasa bayan ya shuri mai tsaron ragar City, Ederson, a fuska da kafarsa.
Dan wasan, wanda ya fito daga kasar Senegal ba zai buga wasan Firimiya da Liverpool za ta fafata da kungiyoyin Burnley da Leicester ba.
Za a iya rage haramcin da aka yi masa zuwa daya ko biyu idan suka yi nasara a karar da suka daukaka.
Ranar Asabar kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce da shi da takwaransa na City, Pep Guardiola ba su yi zaton za a kori Mane ba.