Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home Uncategorized

Manhajar Da Take Iya Gano Ƙwarin Gona

by Tayo Adelaja
October 16, 2017
in Uncategorized
3 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Manoma suna fuskantar matsaloli iri daban daban, kama daga fari, kwari da tsutsa da take lallata amfanin gona, da matsalolin da suka shafi na kayan aikin noman zamani, da faɗuwar farashin albarkatun gona, wanda hakan ba ƙaramin cikas bane ga manoma da ma ƙasa gaba ɗaya, duk shekara ana samun matsaloli da suke kawo cikasa matuƙa ga manoma.

Wannan manhajar da aka ƙirƙiro ta a ƙasar Indiya za ta taimaka wa manoma wajen gano irin tsutsar da take addabar gonakinsu har ma ta ba su shawarar hanya mai sauƙi da za su bi wajen magance tsutsar, wani manomi Ɓorugunti Surendra mai noman shinkafa, ya ce, shi da abokansa manoma suna amfani da manhajar kuma tana matuƙar taimakon su.

samndaads

Manhajar tana iya gano tsutsotsi masu yawa da suke addabar manoma kuma ta bada shawarar matakin da ya kamata a ɗauka wajen maganin matsalar, duk wasu cuttuka da suke shafar amfanin gona manhajar ta na iya gano su da maganinsu, sunan Manhajar ‘Plantiɗ’ wani masanin kimiyya ɗan ƙasar Jamus ne ya ƙirƙiro ta.

Bayan gwaji da masanin kimiyyar ya yi na watanni a yankunan ƙarƙarar ƙasar Indiya, ya gano manhajar za ta taimakawa manoma sosai musamman da yake a wayar hannu ake sauke manhajar kusan duk manoma za su iya amfana da manhajar, kowa ya san yadda manyan wayoyin hannu suke da sauƙin samuwa yanzu, a cikin kuɗi ƙalilan.

Manhajar ba tsutsa da cuttukan amfanin gona kaɗai take iya ganowa ba, ta na iya gano matsalolin da rashin taki ko rashin isasshen ruwa ya ke kawowa amfanin gona, misali a shukokin tumatir, alƙama, ayaba da sauransu, sannan za ta fadi matakin da ya kamata a bi wajen maganin matsalar, in matsalar ta gaggawa ce ma duk za ta yi bayanin hakan.

An ce manhajar ta na aiki tamkar ƙwaƙwalwar ‘yan adam, duk da a kan samu ‘yar matsalar gano wasu cuttuka wasu lokuta, misali cuta da tsutsa su haɗu a waje ɗaya a irin wannan yanayin dole sai masana sun duba menene takamamme abun da yake damun shuka.

Manhajar ta na amfani da yarukka fiye da ɗaya saboda manoman suna da sunayen daban daban da suke kiran tsutsotsi, kwari ko cuttukkan amfanin gona, akwai sunaye na kimiyya amma mafi yawan manoma ba su san waɗannan sunayen ba, don haka dole ya zama akwai yare da suke amfani da shi a kan manhajar, yanzu haka manhajar ta na zuwa da yarukka kusan guda takwas, amma mafi yawan sun a ƙasar indiya ne.

A nan nahiyar Afrika ma akwai wani babban kamfani da aka ba kwangilar bincike da gano yadda za’a samar wa manoman Afrika irin wannan manhajar, wacce ake ganin in aka cimma nasara za’a daura mata yarukka kusan 100 na yankunnan karkarar Afrika, wannan yunƙurin ana ganin ba ƙaramin taimakon manoman Afrika zai yi ba.

Wannan manhaja za ta zama wata kafa ta ƙara wayar da kan manoma musamman wanda suke zaune a yankunnan karkara, kuma ci gaba ne sosai a harkar noma, haka su ma ɗalibai masu koyan ayyukan noma za su ci moriyar wannan manhaja, sannan hukumomi za su ƙara samun bayanai na matsalolin manoma cikin ƙanƙanin lokaci daga bakin su manoman.

Sannan wannan zai bunƙasa fannonin noman zamani, ta inda zai yi sauƙi a gane mai aka fi noma a kowanne yanki, sannan wasu matsaloli mutanen yankin suka fi fuskanta da hanyoyi masu sauƙi na magance matsalolin.

Manhajar za ta taimaka wajen gano yanayin da ya fi dacewa da kowanne irin shuka musamman a noman zamani da ake yin ta cikin ko wanne yanayi ba sai lokaci damina ba, wannan ba ƙaramin taimako bane ga manoma da kamfanonin da suke samar da maganin ƙwari da takin zamani, da kwamfanonin samar da kayan abinci da sauran masu harkar noma.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

An ƙaddamar Da Yekuwar Alluran Rigakafi A Kebbi

Next Post

Za A Fara Nuna Fim Ɗin Tarihin Shehu Ɗan Fodiyo A Bauchi

RelatedPosts

Asibiti

Sanata Ya Raba Kayan Asibiti Na Milliyoyin Naira A Kebbi Ta Arewa

by Muhammad
2 days ago
0

Daga Jamil Gulma Birnin, A cikin shirin sa na inganta...

Mukabalar

Mukabalar Malamai: Ina Son Gwamnan Kano Ya Fara Ba Ni Damar Ganawa – Sheikh Kasiyuni

by Muhammad
2 days ago
0

Daga Mustapha Ibrahim, “Ganin yadda Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi...

Billiri

Yadda Rikicin Billiri Kan Zaben Sabon Sarki Ya Ta’azzara

by Muhammad
3 days ago
0

Gwamnan Gombe Ya Ziyarci Garin Don Duba Asarar Da Aka...

Next Post

Za A Fara Nuna Fim Ɗin Tarihin Shehu Ɗan Fodiyo A Bauchi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version