Daga Abubakar Abba
Don a kara habaka fannin aikin noma a jihar Legss shirin APPEALS na jihar zai samar da ayyukan kasuwancin noma guda 1,465 domin amfanin mata da matasa a 2021.
Jami’ar shirin a Jihar Uwargida Oluranti Sagoe-Obiebo ce ta bayyana hakan a yayin gabatar da kundin nasarorin da shirin ya samar a jihar a 2020.
Shirin na APPEALS hadaka ce a tsakanin Bankin Duniya, Gwamnatin Tarayya da kuma Gwamnatin jihar Legas kan yadda masu yin noma don riba a jihar za su samu rancen kudin aikin noma a fannonin noman Shinkafa da kiwon Kajin gidan gona.
Oluranti Sagoe-Obiebo ta kara da cewa, mata da matasa ne za su amfana da kuma nakasassu a daukacin fadin jihar, inda ta ci gaba da cewa, aikin za a ci gaba da dora shi ne 2020 daga shekarar 2020 bayan samu tsaiko a lokacin da annobar Korona ta billa a jihar ta kuma janyo dakatar da ayyuka a jihar.
A cewar Jami’ar shirin a Jihar Uwargida Oluranti Sagoe-Obieb, aikin zai kuma taimaka wa manoma dubi da kuma samar da wani daukin da ya kai sama da 12, 000 tare da bayar da horo Da kikirar ayyukan da da sauransu.
Jami’ar shirin a Jihar Uwargida Oluranti Sagoe-Obieb ta sanar da cewa, ayyuka guda 1,465 mata da matasa da kuma na masu buwata ta musamman zai taimaka masu matuka wajen inganta rayuwar su da ta iyalansu.
A cewar Jami’ar shirin a Jihar Uwargida Oluranti Sagoe-Obieb, za a kuma samar da tsari na domin rage asaar da masu kamun Kifi a jihar suke yi, musamman a yayin ambaliyar sama da kuma kara habaka fannin ma kamun Kifi a jihar .
Ta kara da cewa, za a kuma samar da wutar sola 20 domin a kara bunkasa aikin a gurare biyu da kuma 10 a cibiyoyi da ban da ban domin kara samar da kudaden shiga ga jihar .
A cewar Jami’ar shirin a Jihar Uwargida Oluranti Sagoe-Obieb, kanana da matsakaitan sana’oi guda 879 an ba su tallafin kayan aikin kai tsaye har da masu kiwon Kajin gidan gona, manoman Shinkafa da sauaransu .
Jami’ar shirin a Jihar Uwargida Oluranti Sagoe-Obieb ta kara da cewa, mutane guda 3, 516 ne suka amfanaz inda sama da manoma guda 8,500 suka sanu horo.
Jami’ar shirin a Jihar Uwargida Oluranti Sagoe-Obieb ta kara da cewa, ko da yake, annobar Korona ta janyo wa fannin aikin noma tsaiko a shekarar 2020, hakan bai dakatar da mu wajen aiwatar da nauyin da aka dora mana ba wajen samar da abinci mai gina jiki ta hanyar yin amfani da fasahar yin noma ta zamani.
A cewar Jami’ar shirin a Jihar Uwargida Oluranti Sagoe-Obieb, a yanzu, “ Mu na da guda 10, 000 da suka amfana kai tsaye da kuma guda 60,000 da suma suka amfana ba ta hanyar kai tsaye ba an kuma tantance manoma guda 9,942 a fannin noman Shinkafa kiwon Kaji gidan gona da kuma renon ‘ya’yan Itatuwa.”