Bello Hamza" />

Manoma 35,000 Suka Amfana Da Tallafin Kayan Aikin Gona A Jihar Jigawa

Ambaliyar Ruwa

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Jigawa ta bayyana cewa, ta samu nasarar bayar da tallafin kayan aikin noma ga manoma fiye 35,000 wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a damuna 2020.

Shugaban hukumar, Alhaji Yusif Sani, ya bayyana haka a tataunawarsa da manema labarai a garin Dutse, ya ce, kayan na daga cikin kayayyakin da suka ragu na tallafi ga manoma a shekarar 2018.

“Mun nemi gwamnatin tarayya da bar mana kayayyakin da suka ragu na tallafin da aka kawo a shekarar 2018 don mu yi amfani da su a nan gaba.

“Mun fara rabon kayan ne daga karamar hukumar Malammadori daga nan kuma za mu shiga rabon a sauran kananan hukumomin jihar 19 har sai duk wanda ambaliyar ta shafa ya samu tallafin,’’ inji shi.

Ya kuma kara a cewa, fiye da manoma 3,500 suka amfana da tallafin a karamar hukumar Malammadori a rabon da aka yi.

Ya bayyana cewa, kayan da aka raba sun hada da irin ridi da shinkafa da gero da dawa da kuma a masara da kuma kayan feshi ciyawa.

Ya kuma bukaci wadanda suka amfana su yi amfami da kayan yadda ya kamata.

 

Exit mobile version