Manoma Mata 6,000 Ne Za Su Amfana Da Shirin Horoswa Na ‘LINE Oxfam’ A Bauchi

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Uwar gidan gwamnan Bauchi, Hajiya Hadiza Muhammad Abubakar ta bayyana cewar, matan karkara da ke sassan jaha daban-daban guda dubu shida (6, 000) su ka samu horo kan koyan sana’oi domin dogaro da kai, ta yadda zasu bada tasu gudummawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasa.

Hajiya Hadiza Abubakar, wacce ta ce horon an gudanar da shi ne karkashin wata kungiya mai zaman kanta ‘LINE Odfam’ wacce ta bunkasa aikin gona kan tallafawa rayuwar manoman karkara kimanin dubu 10, 000, wanda kashi 60% cikin dari cikinsu mata ne.

Yayin da take jawabin bude bitar ta na kwana hudu mai lakabin ‘Mata, Bunkasa Tattali Basu Musu Kariya’, Hajiya Hadiza ta yi la’akarin cewar, ‘LINE Oxfam’ kungiyar kasa da kasa ce mai gambizar kungiyoyi 17 da ke aiki kafada da kafada domin yaki da manufofi marasa inganci a sassa na duniya.

Hadiza, wacce ta samu wakilcin matar mataimakin gwamna, Hajiya Fatima Nuhu Gidado, ta fadi cewa, LINE Odfam ya na daidaita tafiyar mata da maza, ta hanyar bunkasa tattalin matan bisa tafarkin adalci tsakanin su “Kamar yadda muka sani, talauci ya yiwa mata tarnaki kuma kwance, wannan tarnakin yana bukatar bijiro tsare-tsare daban-daban wadanda za su karfafa wa mata da matasa gwuiwa bisa aniyarsu ta dogaro da kai”.

Bisa wannan takidi ne, Hajiya Hadiza take jinjinawa gwamnatin jaha karkashin jagorancin mijinta, Gwamna Muhammad Abubakar, bisa kokarinta kan inganta rayuwar mata, tare da la’akarin cewar, mata sune iyayen al’umma, dan haka idan an tallafawa mata, an tagaza wa al’umma baki daya.

Ta kuma yi furucin cewar, bada horo ga manoma Karkara yana gudana ne a zababbun kananan hukumomi da ke jahar nan, dan haka ta yi kira ga mata dasu bada muhimmanci wa horarwa da suke samu domin hakar su ta cimma ruwa bisa koyon sana’oi da za su kaisu tudun na tsira.

Hajiya Hadiza Muhammad Abubakar ta kuma ya bawa kungiyar LINE Oxfam dangane da zabin Bauchi bisa wannan shiri mai albarka, tare da fatar cewa horaswar za ta kasance mai matukar amfani wa mata yadda zai kawo canji a gidaje da al’ummomin su.

Yayin da ya ke bada haske kan shirin, mai baiwa kungiyar ta Oxfam shawara, Mista Bidemi Olayemi Ajibola ya bayyana kalman ta ‘LINE’ da cewar, gamayya ce da ta hada rayuwa da cimaka, shirin da kuduri na zaman-takewa ta duniya da ke kasar Kanada ta  dauki nauyin gudanarwa a jahar Bauchi.

Mai bada shawara Ajibola, ya kuma bayyana cewar, shirin wanda ya ke da asalin tallafi kan aikin gona, musamman ma bisa hanyoyin noman ridi, masara, dawa, da samar da madara da mana ta hanyar kiwace-kiwacen dabbobi.

Karin hasken cewar, shirin ana gudanar da shi a jaha cikin kananan hukumomi shida wadanda suka hada da Shira da Gamawa a mazabar arewa, Ningi da Darazo a mazabar tsakiya, sai kuma Alkaleri da Tafawa Balewa a mazabar Bauchi ta kudu.

Ya kara da cewar, shirin yana hasashen raunanan manoma guda dubu 10, 000 wadanda kashi 60% za su kasance mata ne, yayin da tawagar farko na shirin wacce ta kunshi manoma dubu3, 165 za a yi wa rajista, wadanda kishi saba’in da biyu da digo uku (72.3%) cikin dari za su kasance mata ne “Mutane suna ta al’ajabin yadda muka cimma wadannan nasarori a wuraren da zaman-takewa da al’adu suka bambanta, sai muka mayar masu da martani cewa wannan shirrin mune, duk da cewa muna shirye da mu fahimtar da kungiyoyi ta yadda lamarin zai amfanar dasu”.

Ajibola ya kara da cewar, shirin wanda hori-na-horar ne, ya karfafa gwuiwa mahalarta ilmantuwa kan cimaka, da nufin bacin kara masu kuzari, zai kuma horar dasu kan cimma bukatun cimaka daga abubuwan suke nomawa.

Ya kuma furtawa mahalarta bitar cewa shirin ya rarraba kayayyakin gona wa dukkan mata da suka ci gajiya daidai gwargwadon bukatunsu, yana mai fadin cewar, bita cikin shirin mai dorewa ne.

Ajibola ya kara da cewar, shirin zai nausa zuwa jam’iyun gama kai, wadanda kimanin su ya kai dari biyu da goma sha shida (216), wadanda su kuma za su nausa shirin wa gamayyar al’ummomin su, yadda kowa da kowa zai amfana.

Exit mobile version