Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Manoma Sun Ɗaukaka Ƙara Kan Rikicinsu Da Janar Zamani Lekwot

by Tayo Adelaja
October 2, 2017
in LABARAI
3 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Abubakar Abba, Kaduna

Rikicin gonaki tsakanin tsohon  Gwamnan Soji na Jihar Ribas Manjo Janar Zamani Lekwot mai ritaya da mai unguwa Dogara da Manoma 225 da suke ƙauyen Rijana a ƙaramar hukumar Chikun dake Jihar Kaduna, manoman sun shigar da ƙara a gaban kotun ɗaukaka ƙara ta Jihar Kaduna, a bisa ƙin amincewa da hukuncin da Mai Shari’a ta Babbar Kotun jiha ta yanke na mallakawa Janar  Zamani gonakan.

Idan dai ba a manta ba, Zamani ne ya shigar da ƙarar a gaban kotu inda ya ke tuhumar manoman  sun shigar masa gonarsa dake ƙauyen na Rijana.

Wanda kuma tun a shekarar 2011 ake ta fafatawa akan Shari’ar, inda Babbar Kotun ta yanke hukunci a ranar 25 ga watan Janairun 2016 ta hanyar mallakawa Zamani gonakan.

Ya ce, “kamar yadda ka sani ne, kes ɗin mai lamba CA/K06/ 2016, tuni dama an shigar da takardar ɗaukaka ƙarar a kotun ta ɗaukaka ƙara akan ƙalubalantar hukuncin da Babbar Kotun ta jiha ta yanke. Ita Babbar Kotun ta ɗan ɓata mana lokaci wajen haɗa abin da ake cewa bayanai, domin lokacin da ya kamata su shigar da bayanan basu yi ba har sai da lokacin ya ƙure.”

Ya ƙara da cewa, “da muka fahimci haka sai muka shigar da roƙo a gaban kotun ɗaukaka ƙara, wato kamar wata dama ce muke nema a gaban kotun ta ɗaukaka ƙara. Kuma a ƙa’ida sai kotu ta baka dama domin idan bata baka ba, duk abin da ka shigar gabanta, kamar baka shigar ba ne, abin da ya kawo mu gaban kotun kenan, domin ta karɓi abubuwan da muka tattara daga Babbar kotun, inda a ciki muka bayyana ƙarara irin kura-kuren da aka yi a gaban Babbar kotun da ta yanke hukuncin.”

Aminu ya bayyana cewa, “wasu daga cikin kura-kuren da Babbar Kotun ta yi wajen yanke wancan hukuncin sun haɗa da rashin bayyana iyakar wurin da ta yanke hukunci akai, domin kuwa, kotu tana yanke hukunci ne akan wani abu da yake cikakke.”

Ya ci gaba da cewa, “sannan kuma akwai rashin halartar gonar da Mai Shari’ar ba ta yi ba, don tantance iyakar da ake taƙaddama a kai, da kuma wasu abu da muka fahimta kamar na sa son rai wajen yanke hukuncin, wanda har ya janyo muka shigar da ƙorafi gaban ita Babbar kotun na cewar, bamu gamsu da hukuncin data yanke ba, kuma muka ce bamu yarda ta ci gaba da shari’ar ba saboda muna ganin kamar ta shigo da son rai a ciki, wanda ta ƙi saurarenmu.”

Aminu ya bayyana cewa, dama a bisa ƙa’idar Shari’a, in akwai zargi akan yadda Alƙali ke tafiyar da shari’ar sa, aka kuma bayyana masa cewar yayi ya maida Shari’ar zuwa ga Alƙalin Alkalai na jiha shi kuma ya kaiwa wata kotun ta saurari ƙarar kuma Alƙalin bai yi hakan ba, yana ɗaya daga cikin abin da za ka iya yin ƙorafi akai.”

Lauyan yace, “wannan yana ɗaya daga cikin abin da muka tattara, muka taho dashi zuwa Kotun ta ɗauka ƙara.”

Da aka tambaye shi ko Kotun ta ɗaukaka ƙarar ta amince za ta saurari ƙarar tasu, ya ce,”ƙwarai da gaske yanzu ɗaukaka ƙarar na gabanta, yanzu kawai abin da ya rage mu zo mu yi jayayya da waɗanda muke shari’ar, sannan sai mu jira hukuncin kotun. Kotun ta ɗaukaka ƙarar bata sa rana ba tukunna, domin ita wannan kotun, akwai hanyoyi biyu da take bi kafin a sa rana, akwai abubuwan da za a ce ka yi, saboda ɗimbin shari’o’in da ke gabanta, kuma, akwai ranar da za su ce mana mu zo mu ci gaba da shari’a.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Rashin Biyan Bashin Banki Na Neman Zama Barazana Ga Tallafawa Manoma A Kano

Next Post

PDM Ta Nuna Goyon Bayanta Ga Shugabancin Nasko

RelatedPosts

An Yi Wa Buhari Da Osinbajo Allurar Rigakafin Korona

An Yi Wa Buhari Da Osinbajo Allurar Rigakafin Korona

by Sulaiman Ibrahim
3 hours ago
0

Daga Sulaiman Ibrahim An yi wa Shugaba Muhammadu Buhari da...

Mukabalar

Kotu Ta Dakatar Da Yin Mukabalar Sheikh Abduljabbar Da Malaman Kano.

by Muhammad
8 hours ago
0

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Wata kotu a Jihar Kano ta...

Ma'adanai

Masu Hakar Ma’adinai Ba Su Da Alaka a‘Yan Ta’adda -Shugaba

by Muhammad
9 hours ago
0

Daga Idris Aliyu Daudawa, Shugaban kungiyar masu hakar ma'adinai ta  Nijeriya...

Next Post

PDM Ta Nuna Goyon Bayanta Ga Shugabancin Nasko

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version