Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home NOMA

Manoma Sun Kalubalanci Jami’o’i Su Gudanar Da Bincike Kan Rubewar Albasa

by Muhammad
February 9, 2021
in NOMA
3 min read
Albasa
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Manoman Albasa a jihar Yobe sun kalubalanci mahukuntan Jami’oi da cibiyoyin gudanar da bincike a fannin noma dake fadin Nijeriya su samar da kayan aiki na zamani da za a dogara a kan su wajen adana Albasa don magance rubewa da yin asara da manoman suke yi.

Manoman sun gabatar da kalubalen ne a hirar su da kamfanin dillancin labaraia na kasa, inda suka ce matsalar rashin samar da kayan na zamani na adana Albasa, yana ci masu Tuwo a Kwarya wajen samun damar shuka Albasa mai yawa.

samndaads

A cewar daya daga cikin manoman na Albasa Malam Kyari Usman Geidam “ Muna shuka Albasa da dama, amma rashin kayan na kawo mana cikas, inda hakan ya sanya muke sayar da Albasar a cikin farashi mai sauki”.

Shi ma wani manomin na Albasar Danladi Mai-Lambu ya ce, “Muna sayar da Albasar da wuri in ta nuna don gudun rubewarta ko kuma gudun kada muyi asara kuma bamu da wata hanya ta gargajiya da zamu dinga adana Albasar in an girbe ta.”

Shi ma mai sayar da Albasa Alhaji Ali Mustapha ya ce, a yanzu ana sayar da Albasa akan farashi daga naira 3,000 zuwa naira 4,000 na ko wanne buhu daya, inda da an samar da kayan zamani na adana Albasar, manomi zai iya samun sama da ribar naira 25,000 na ko wanne buhu daya a shekara.

Ya yi nuni da cewa, babban kalubalen da manoman suke fuskanta shi ne na rashin samar da kayan zamani na adana Albasar, inda ya kara da cewa dole be sai an samar da waje mai sarari da za a dinga shanya ta son kada ta lalace da kuma yawan duba ta son ware wadanda suma fara rubewa.

Shi ma wani mai sayar da Albasar Haruna Bakura ya ce, idan aka samar da kayan na zamani manoman Albasar dake kasar nan, za su iya wadata kasar nan da yawan da Albasar da ake bukata a Nijeriya harda fitar da ita zuwa kasuwannanin dake kasashen duniya.

Shi kuwa Shugaba kula da hada-hadar kasuwancin Albasa na Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya, Musatapha Khadiri ya bayyana cewa, a duk shekara Nijeriya na bukatar tan miliyan 2.5 na Albasa, amma kasar, na noma tan miliyan 1.4 ne kacal a duk shekara.

Shugaban ya sanar da hakan ne a wajen taronsu da ya gudana a Sakkwato, inda ya kara da cewa, hakan ya janyo samun gibin, inda hakan ya janyo ake shigowa da ita daga wasu kasashen dake makwabtaka da Nijeriya a baya.

A cewar Shugaban, a duk shekara ana shigo da tan miliyan 1.1 na albasa, duk da cewa kasar nan ce ta biyu wajen noman albasa a Afirka a bayan kasar Masar.

Shugaban kula da hada-hadar kasuwancin Albasa na Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya, Musatapha Khadiri ya kara da cewa, a kowace shekara Nijeriya na bukatar tan miliyan 2.5, amma tana noma tan miliyan 1.4 a shekara abin da ya kawo mata gibin sauran ke nan da ake shigowa da su.

Shugaban kula da hada-hadar kasuwancin Albasa na Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya, Musatapha Khadiri ya yi nuni da cewa matakin abin yabawa ne ga kasa don hakan zai sanya kasar ta dogara da kanta musamman a harkar noman albasa

A cewar Shugaban kula da hada-hadar kasuwancin Albasa na Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya, Musatapha Khadiri, rufe ta watannin baya, a yanzu ta sa manoma mayar da hankali ga noma don ciyar da kansu, amma duk da haka akwai ’yan wahalhalu ga ’yan kasuwar albasa na Afirka.

Shi ma Sakataren kungiyar Manoma da ’Yan Kasuwar Albasa ta Nijeriya, Aliyu Isah Mai Tasamu a nasa jawabin a wurin taron ya ce, albasa za ta samu yanayi mai kyau za ta samar wa Nijeriya kudin shiga Dala miliyan hudu da ashirin.

SendShareTweetShare
Previous Post

Nijeriya Na Bukatar Naira Tiriliyan Biyu Don Yi Wa Mutanenta Rigakafin Korona

Next Post

Amfanin Wasu Tsirrai 13 A Jikin Mutum

RelatedPosts

Kiwon Shanu

Dalilinmu Na Son Bunkasa Tsarin Kiwo A Nijeriya – Phairah Agro

by Sulaiman Ibrahim
8 hours ago
0

Daga Abubakar Abba Kamfanin Phairah Agro bentures ya shelanta cewa,...

NIRSAL

Hukumar NIRSAL Na Shirin Kara Inshorar Manoma Zuwa Miliyan Uku Zuwa 2026

by Muhammad
1 day ago
0

Hukumar Tsari ta Aikin Noma a Nijeriya (NIRSAL) ta ce...

Nahiyar Afirka

Yadda Za A Samar Da Abinci Mai Yawa A Nahiyar Afirka

by Muhammad
1 day ago
0

Masu ba da agaji na Afirka da wadanda ba na...

Next Post
Tsirrai

Amfanin Wasu Tsirrai 13 A Jikin Mutum

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version