CRI Hausa" />

Manoma Sun Kara Samun Kudin Shiga A Kauyensu A Lokacin Cin Rani

A kwanakin baya, mutanen dake aiki a masana’antar samar da jakar leda na kamfanin masakar Anheng na jihar Xinjiang dake gundumar Xinhe dake yankin Aksu na jihar, wadanda manoma ne da suka zo wurin yin aiki a lokacin cin rani.

Tun daga karshen watan Oktoba, an kidaya yawan mutanen da ba su da aiki a lokacin cin rani a garin Tashairik, inda aka yi hadin gwiwa tare da wasu kamfanoni don sanin bukatunsu na neman ma’aikata. Kana an hora da mazauna kauyen tare da samar musu aiki, ta haka mazaunen kauyen da suke kulawa da gida, ba su da damar fita waje za su iya samun horo, da yin aiki a kauyensu.
Bayanai na nuna cewa, masakar Anheng ta jihar Xinjiang ta baiwa manoman garin 101 aiki, guda 77 daga cikinsu suna fama da talauci. A halin yanzu, yawan kudin shiga da suka samu a kowane wata, ya kai kimanin Yuan 2000. Bayan da suka samu kwarewa a kamfanin, kudin shigar su zai karu.
A shekarun baya, garin Tashairik ya samar da aiki ga manoma a lokacin cin rani, don kara kudin shigarsu ta hanyar ba su horo, da sa kaimi ga kamfanoni da su samar da aiki da sauransu, hakan ya aza tubalin kara kudin shigar manoman garin. (Zainab)

Exit mobile version