Abubakar Abba">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home NOMA

Manoman Albasa Sun Kuduri Aniyar Nomanta Da Yawa Don Karya Farashinta

by Abubakar Abba
December 9, 2020
in NOMA
3 min read
Manoman Albasa
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Wasu daga cikin manoman Albasa a jihohin Kano, Kebbi, Zamfara, Sakkwato da Katsina sun fara noman rani na Albasa bisa nufin karya farashinta a kasuwa a halin yanzu.
An ruwaito cewa, tsadar Albasa ta kai wani matsayi a bana tare da buhun da aka sayar a bara kan Naira 15,000 a yanzu ana sayar da shi kan Naira 51,000 a Jihar Kano, wanda har ma ana yi wa kallon mai rahusa fiye da sauran wurare kamar Legas, Fatakwal da Abuja.

Kamar yadda Albasa take da mahimmanci a girkin can Adam yawancin magidanta yanzu suna magana a kan yadda farashinta me ci gaba da hauhawa sama, inda kuma aka dantanta farashinta a yayin shukata a watan Nuwamba da Disamba.

samndaads

Malam Baba Bala Kubarachi, manomi ne a madatsar ban ruwa ta Kadawa da ke jihar Kano, ya bayyana cewa hauhawar farashin Albasa a halin yanzu shi ne sakamakon ruwan sama da ya dauke a bana.

Kubarachi ya ce, ayyukan noman, na yau da kullun suna da jadawalin lokaci da kuma tsare-tsaren da aka tsara, inda ya kara da cewa, wasu manoman galibi suna shukata zuwa karshen kowane lokacin damina, inda ya bayyana cewa, wannan Albasar ce za a girba yayin da duk wani mai noman Albasa yake shukawa a lokacin rani kuma ta haka ne za a rufe karancinta ba tare da matsala ba, ya bayyana cewa, amma a wannan shekarar, ruwan saman da ya dauke da wuri kuma manoma da yawa ba sa iya shuka, saboda haka karancin da ake fuskanta a halin yanzu.

An kuma gano cewa a shekarar da ta gabata, a wasu yankuna na al’umomin da ke noman Albasa a cikin Jihar ta Kebbi, noman albasa ya gamu da koma baya yayin da cututtuka suka afka wa amfanin gona, wanda ya rage yawan amfanin gonarsa.

An ruwaito cewa, za a yi hadin gwiwa tsakanin manomanta da wanda daga cikin dalilin, akwai tashin farashinta a yanzu da kuma irin kudin da ake kashewa na injinan ban ruwa.

Wani manominta a jihar Katsina, Mohammed Umar, ya alakanta tsadar kayan da ficewar manoma da yawa daga noman amfanin gona a yankin Faskari saboda rashin tsaro, inda ya kara da cewa, takin zamani, musamman NPK, wani ciwon kai ne ga manomanta, inda ya kara da cewa, farashinsa yana karuwa kowace shekara, inda ya bayyana cewa, a shekarar da ta gabata, buhun NPK ya kai kimanin Naira 7,000, amma a wannan shekarar ya karu da kashi 100 bisa 100 yayin da ake siyar da buhu kan farashin Naira 14,500.

Rahotanni daga Kebbi, Kano, Katsina, Sokoto, Jigawa, da sauran jihohin da ke noman albasa, sun nuna cewa manoma sun shiga dumbin amfanin gonar, inda kuma wasu rahotannin sun nuna cewa, a karamar hukumar Aliero ta jihar Kebbi, inda kusan dukkan manoman yankin ke aikin noman Albasa, sai ta lura cewa mazauna yankin, ciki har da wadanda suka yi watsi da nomanta, sun koma gona.

Wani manomi Mohammed Ibrahim, ya sanar da cewa, yawancin gonakin Albasa da aka yi watsi da su shekarun baya yanzu ana amfani da su kuma gonakin sun riga sun nuna kyakkyawan girbi.

SendShareTweetShare
Previous Post

PDP Da PRP Sun Ki Amincewa Da Sakamakon Zaben Cike Gurbin Dan Majalisar Bakori A Katsina

Next Post

Masu Kiwon Kaji A Akwa Ibom Sun Koka Kan Karancin ’Yan Tsaki

RelatedPosts

Rogo

Muna Bukatar Takin Zamani –Manoman Rogo A Kwara

by Abubakar Abba
14 hours ago
0

Manoman Rogo a jihar Kwara sun yi kira ga gwamnatin...

Kananan Manoma

Kananan Manoma Sun Bukaci Bashi Daga CBN

by Abubakar Abba
14 hours ago
0

Wasu daga cikin kananan manoman a kasar nan, sun bukaci...

Shirin Anchor Borrowers

Mun Ga Canji A Noman Kwakwar Manja Karkashin Shirin Anchor Borrowers, Cewar Cif Igwe

by Abubakar Abba
2 days ago
0

Shugaban Kungiyar Manoman Kwakwar Manja ta kasa Cif Igwe Hiliary...

Next Post
Kiwon Kaji

Masu Kiwon Kaji A Akwa Ibom Sun Koka Kan Karancin ’Yan Tsaki

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version