Abubakar Abba" />

Manoman Bana Ba Za Su Amfana Da Shirin Tarayya Ba – Nanono

Ganin cewar, an fara shirye-shiryen fara gudanar da kakar aikin noma ta daminar shekarar 2020, manoman kasar nan baza su amfana da shirin aikin noma na zamani na Gwamnatin Tarayya ba.

Hakan ya biyo bayan sanarwar da Ma’aikatar Aikin Gona ta kasa da Raya Karkara na cewar, manoman ba za su amafana da shirin na kayan noma na zamani ba a kakar aikin noman ta shekarar 2020 ba wanda za’a fara gudanar da shirin nan da watannin, takamaimai a watan Satumbar shekarar, 2020.

Akasari dai, watan na Satumba ne ake sa ran manoman kasar nan za su fara yin girbin amfanin gonakan su da suka shuka a daukacin fadin Nijeriya.

Ministan Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkara Alhaji Mohammed Sabo Nanono ne ya sanar da hakan a wani aikin noma da ya duba a yankin kudancin kasar da kuma gudanar da gana a garin Kalaba da ke a cikin jihar Koros Riba.

A cewar Ministan Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkara Alhaji Mohammed Sabo Nanono, wannan aikin na yin noma da kayan zamani za’a fara gudanar dashi ne a kananan hukumomi 632 nan da watanni shida masu zuwa a daukacin fadin kasar nan kuma za’a gusnar da aikin tare da fannin aikin noma masu zaman kansu.

Ministan Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkara Alhaji Mohammed Sabo Nanono ya kara jadda da mahimmancin da shirin yake dashi, inda kuma ministan ya bayar da tabbacin cin nasarar shirin da kuma samar da dauki daga bangaren gwamnatin tarayya din kwalliya ta biya kudin sabulu.

Ministan Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkara Alhaji Mohammed Sabo Nanono ya ci gaba da cewa, kasar nan ta na da alumma masu yawan gaske da kuma samun kasuwa mai mai yawa, inda ya yi nuni da cewa, ana kuma saran cimma burin da aka sanya a gaba kan shirin.

A cewar Ministan Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkara Alhaji Mohammed Sabo Nanono, masana’antaun dake sarrafa amfanin a kasar nan suka bayar da gagarumar gudanmawa wajen habaka tattalin arzikin kasar nan a bisa tsarin aikin noma na kasar.

A karshe, Ministan Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkara Alhaji Mohammed Sabo Nanono ya kara da cewa, shirin zai taimaka matuka wajen rage yawan yan kasar nan masu zaman kashe wando, bunkasa tattalin arzikin Nijeriya, samar da wadataccen abinci a kasar, zuba dimbin jari a fannin aikin noma na kasar da kuma samar da dabaru a fannin na aikin noman Nijeriya.

A wata sabuwa kuwa, Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya sanar da cewa, jihar ta Katsina kuma samo masu zuba kudade na fitar da kaya zuwa kasashen waje, musamman daga bankin NEDIM din habala fannin aikin noma a jihar.

A cewar Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya kara da cewa, babu wata dabara da tafi dacewa fiye da ianganta rayuwar alumma ta hanyar kasuwanci da kuma msana’antu.

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya sanar da cewa, baje kolin na bana yana da mahimmanci matuka, musamman ganin yadda gwamnatin jihar Katsina ta yi hadaka da sauran hukumomi don ta magance kalubalen da take fuskata a jihar.

 

Exit mobile version