Wadansu manoma a jihar Borno sun jinjinawa gwamnatin tarayya bisa kaddamar da shirin ‘Anchor Borrower’ wato ABP a takaice wanda gwamnatin ta samar domin tallafawa ayyukan noma.
Manoman sun shaidawa Kamfanin Dillanci Labaran Nijeriya a Maiduguri da karamar hukumar Jere a jihar Borno a ranar Juma’a, inda suka jaddada cewa; tallafin da gwamnatin tarayya ke bai wa manoma a jihar ta hanyar babban Bankin Nijeriya, wato CBN abin jinjinawa gwamnnatin ne.
Bankin CBN din sun tallafawa akalla manoma dubu 50 a jihar a bangaren da ya shafi ayyukan noma a karkashin shirin tallafin noman.