Abubakar Abba" />

Manoman Masara A Gombe Za Su Dara – Kwamishina 

Kwamishinan Gona da Dabbobi na Jihar Gombe Alhaji Muhammadu Magaji Gettado ya bayyana cewa, gwamnatin Jihar ta shirya samar wa manoman rani irin masara mai inganci da ya kai naira miliyan 20 domin karfafa noman rani a jihar.

A cewar Kwamishinan Gona da Dabbobi na Jihar, Alhaji Muhammadu Magaji Gettado, ma’aikatar ta zakulo manoman masara fiye da dubu daya domin cin gajiyar shirin.
Kwamishinan Gona da Dabbobi na Jihar, Alhaji Muhammadu Magaji Gettado ya bayyana haka lokacin da yake zantawa a jihar Gombe, a taron manoman rani na shinkafa da Babban Bankin Najeriya (CBN) da Bankin Unity da Hukumar Inshorar Noma ta Kasa (NAIC).
Alhaji Muhammadu Magaji Gettado ya ce, wannan tsari na Ma’aikatar Gona ya sha bamban da sauran tsare-tsare domin ba kayayyakin da za su bayar bashi ba ne za su sayar wa manoma ne a kan farashi mai sauki, inda manomi zai biya nan take ya dauka.
Kwamishinan Gona da Dabbobi na Jihar, Alhaji Muhammadu Magaji Gettado ya kara da cewa, irin masarar kyauta ce, domin a gwada shi a gani kuma manoman rani za a bai wa, inda ya kuma ja hankalin su da ka da su ajiye sai lokacin damina; su noma yanzu don ana so a gwada ingancinsa ne a gani kafin lokacin noman damina ya yi.
Kwamishinan ya ce Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Inuwa Yahaya ya kawo irin ne domin a taimaka wa manoma da makiyaya a jihar da nufin wadata kasa da abinci.
Ya yi kira ga shugabannin cewa duk kayayyakin da aka kayyade domin manoma a ba su ka da a ce a bai wa manomi taki buhu 10 wani ya rage ya ba shi biyar ko bakwai.
Ya kuma bayyana cewa, manoman shinkafar da shirin Anchor Borrowers zai bai wa rancen noma kuwa ya ce domin gudun ka da a cuce su kamar yadda ya faru a baya shi ne yanzu ake zama da su ana sanar da su farashin kayayyakin da sai sun yarda kafin a amince a kawo ma su.
Alhaji Magaji Gettado, ya ce idan aka gama zama aka amince za a bai wa kowane manomi kaya da kudi a kan lokaci, inda ya kara da cewa, idan kuma aka zo karshe aka ga idan an bai wa manoman kayan za su cutu to za su dakatar.
Ya ce duk manomin da aka bai wa kaya idan ya girbe amfanin gonarsa ba da kudi zai biya ba da amfanin da ya noma irin wanda aka ba shi zai biya.
A wata yayin da bukatar Nama da kayan da suka danganci Madara ke kara karuwa a wannan kakar, masu ruwa da tsaki a fannonin biyu sun sanar da cewa akwai bukatar a kara yin kokari don bunkasa fannin kiwo a daukacin fadin kasar nan.
Yan Nijeriyar da suka kagara suci Nama mai yawa da aka samar a Yankin Afirka Yamma, abin baya misaltuwa.
Wasu bayanai da aka samar daga wurare da ban-da-ban, sun nuna cewa, burin yan Nijeriya shine su ci Nama akalla a cikin sati uku wanda ya kai yawan kimanin nauyin kilogiram tara.
karuwar yawan alummar kasar nan da karin samun kudaden shigar su da kuma kara wayewarsu, ya kara nuna yadda ake da bukatar a kara samar da dabbobin kiwo a kasar nan.
Kimanin Shanu miliyan 1.3 ake yankawa a duk shekara don wadatar da yawan alummar Nijeriya su kimanin miliyan 170.
Naman shanu yana kaiwa yawan kimanin kashi 30 a cikin dari na yawan Naman da ake samarwa a kasar nan.
kididdiga ta nuna cewa, Nijeriya ta na fuskantar karancin wadataccen Nama saboda yadda ake da ake yawan cinsa natuka a kasar nan, inda hakan ya nuna cewa, wannan fannin babba hanya ce ta kasuwanci sosai a kasar nan idan aka yi la’akari da yadda ake da bukatar Nama a kasar nan.
Bugu da kari, hukumar aikin noma ta (FAO) ita ma ta tabbatar da hakan inda ta kiyasata cewa, daga shekarar 2010 zuwa shekarar 2050, Naman Shanu, Kiwo da kuma Madarar da ake sha a kasar nan, sun karu daga 117 zuwa 253, inda hakan ya kai kashi 577 a cikin dari.
A saboda hakannne, masu ruwan da tsaki suka bayar da shawarar akwai bukatar a zuba dimbin jari a fannin kiwo a kasar nan yadda za a samu nasarar samar da naman.

Exit mobile version