Abubakar Abba">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home NOMA

Manoman Masaran Kaduna Sun Samu Nasara A Karkashin Shirin APPEALS – Shugaba

by Abubakar Abba
February 2, 2021
in NOMA
2 min read
Matasa 60,000  Su Ka Yi Rajista Don Shiga Fannin Noma – Kwamishina
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Manoman Masara a jihar Kaduna da aka tallafa masu da ingantattun kayan aikin noma da kuma sabin dabarun yin noma ta hanyar yin amfani da fasahar zamani a kakashin shirin aikin noma na APPEALS da ke a jihar, sun samu gagarumin karin yawan amfanin gona a kakar noma da ta gabata a jihar.

Shugaban kungiyar manoman ta Biye a karamar hukumar Giwa a jihar Alhaji Adamu Aliyu Shika ne ya bayyana hakan a taron wanzar da shirin karo na shida da jami’in shirin na kasa Alhaji Mohammed Sani Jobdi ya jagoranci wata tawaga a makon da ya gabata.
Tawagar ta kuma kai ziyara ga alumma domin duba yadda aikin na ke gudana a yankunan da aka ware don wanzar da shirin.
Alhaji Adamu Aliyu ya sanar da cewa, akasarin wadanda suka amfana da shirin, sun girbe samu buhunhunan kusan fiye da amfanin gona da aka sa ran za su girbe.
A cewar Alhaji Adamu Aliyu, misali manoman yayan kungiyar ta Biye, sun girbe tan-tan 206 na Masara tan 156 kafin a kawo daukin shirin na aikin noma, inda ya kara da cewa, sun kuma hada kai da masu sayen Masarra da suka noma kan farashi mai kyau.
A na sa martanin jami’in shirin aikin noma na APPEALS na kasa Alhaji Sani Jobdi ya bayyana jin dadinsa kan nasarorin da manoman suka amfana da shirin suka samu a jihar.
Alhaji Sani Jobdi ya kara da cewa, bayananin da wadanda suka amfana da shirin suka yi kan nasarorin da suka samu fiye da na shekarar da ta gabata abu ne mai kyau.
Alhaji Sani Jobdi ya kuma yi kira ga a gare su kada su gajiya da yin amfanin da dabarun yin noma na zamani, inda ya yi nuni da cewa, shirin zai kuma tallafawa na nakasassun da ke a jihar Kaduna domin suma su amfana.
A cewar Alhaji Sani Jobdi, tuni shirin ya fara tallafawa nakasasuun da ke a jiha, inda kuma a wasu nakasassu guda 85 suka amfana da shirin a yankin Arewa maso Gabas na kasar nan, ya kara da cewa, aikin bankin duniya ne ya ke tallafawa, musamna domin wanzar da shirin a jihohi shida.
Shi ma a nasa jawabin, jami’in shirin na jihar Kaduna Dakta Yahaya Aminu, wanda wani jami’i Reuben Teddy ya wakilce shi a gurin taron ya sanar da cewa, an gudanar da ganawar da ke nuna cewa, shirin ya fara kankama a kaduna
Dakta Yahaya Aminu ya kara da cewa, ganawar an shirya ta ne bisa yin dubi ga bukatar yin nazari kan kundin wanzar da shirin, inda ya ci gaba da cewa, daga cikin nakasassun dubu cikin saba’in a jihar da suka nuna butarsu kan shirin a jihar, nakasassu dubu daya da dari shida da sha biyar suka nuna bukatar su, inda 85 suka samu nasarar shiga cikin shirin.
Dakta Yahaya Aminu ya ci gaba da cewa, an gudanar da ganawar ce domin yin dubi ga bukatun da jihohi suka gabatar, wuraren da ake wanzar da shirin da kuma yin dubi ga bukatun nasakassu kan amfana da shirin.
Jami’in shirin na jihar Kaduna Dakta Yahaya Aminu ya bayyana cewa, har ila yau kuma mata da matasa zasu amfana da shirin, musamman domin a inganta rayuwarsu da samar da abinda za su dogora da kawunansu.
A cewar Jami’in shirin na jihar Kaduna Dakta Yahaya Aminu, shirin zai kara taimaka wa wajen habaka aikin noma ba wai a jihar Kaduna kadai ba, harda kasa baki daya kuma zai kara bunkasa hada-hadar fannin aikin noma, musamman a jihohin Cross Riber, Enugu, Kaduna, Kano, Kogi da Lagos da aka fara wanzar da shirin.

samndaads
SendShareTweetShare
Previous Post

Dalilin NALDA Na daukar Matasa Masu Digiri 30,000

Next Post

Messi Ya Kafa Sabon Tarihi A Barcelona

RelatedPosts

Bankin Manoma Ya Tallafa Wa Masu Kiwon Zuma A Abuja 

Mun Shafe Shekaru Muna Hadaka Da Jihohi Don Bunkasa Noma – BOA

by Abubakar Abba
5 days ago
0

Daga Abubakar Abba Manajin Darakta na Bankin Manoma na kasa...

Noman Auduga A Nijeriya

Dole Sai Matakan Gwamnati Uku Sun Taimaka Kafin Noman Auduga Ya Bunkasa, Cewar Kungiya

by Abubakar Abba
5 days ago
0

Za a iya habaka noman Auduga a kasar nan ne...

Za Mu Yi Amfani Da Noma Don Bunkasa Arzikin Kwara – Gwamna Abdulrazak

Za Mu Yi Amfani Da Noma Don Bunkasa Arzikin Kwara – Gwamna Abdulrazak

by Abubakar Abba
5 days ago
0

Daga Abubakar Abba Jihar Kwara ta tashi tsaye don cika...

Next Post
Duk Duniya Ba Wanda Ya Kai Cristiano Zura Kwallo A Kungiya Da Kasarsa

Messi Ya Kafa Sabon Tarihi A Barcelona

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version