Kungiyar Manoman Shinkafa ta kasa RIFAN reshen Jihar Kano, ta ce kimanin manoman Shinkafa guda dubu 44 daga rukuni 11 ne suka samu wannan tallafi na noman damina a karkashin shirin aikin noma na Anchor Borrowers a jihar.
A cewar kungiyar har ila yau, kimanin manoman shinkafa dubu 90 ne suka amfana daga bashin noma na Babban Bankin Nijeriya CBN a cikin shekara uku, wato daga shekarar 2017 zuwa 2019 .
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Shugaban kungiyar, Alhaji Haruna Abubakar Aliyu, inda kuma ya musanta zargin cewa Jihar Kano ba ta amfana daga shirin tallafin noma na Gwamnatin Tarayya ba.
Ya ce, manoman shinkafa da suka hada da na rani da na damina duk sun samu bashin noman a jihar.
Ya kara da cewa, babu kanshin gaskiya mutum ya fito ya ce wai manoman Jihar Kano ba su samu bashin noma daga Gwamnatin Tarayya ba.
Ya sanar da cewa, a shekarar 2017 kimanin manoma dubu 24 ne daga rukuni takwas suka amfana, inda ya kara da cewa, haka a shekarar bara manoma dubu 44 daga rukuni 11 ne suka samu wannan tallafi na noman damina.
Shugabkn ya ce, a bana, manoma dubu 28 daga rukuni bakwai suka amfana daga tallafin.
Shugaban ya ce batun a ce mutum yana da kadada dubu 200 yana kuma girbar shinkafa buhu 250 daga kowace kadada ba tare da tallafin gwamnati ba wannan ba abu ne mai yiwuwa ba.
Ya ce, abu ne da ya fi kama da kambame, kungiyarmu ta girgiza da jin cewa wani mutum ya fadi cewa wai manoman shinkafa na Jihar Kano ba su amfana daga bashin na Gwamnatin Tarayya ba.
A wata sabuwa kuwa, masana’antar sarrafa shinkafa da ta kai mataki na hudu a duniya wadda kuma tafi duk wata masana’antar sarrafa shinkafa dake a nahiyar Afirka.
Mai bai wa Gwamnan jihar shawara ta musamman akan aikin fannin noma Abisola Olusanya ne ya sanar da hakan a lokacin da ya kai ziyarar aiki a masana’antar.
Sunan masana’antar shi ne, Imota Rice Mill wacce idan an kammala ta, zata dinga sarrafa buhunhunan shinkafa 650 mai nauyin kilo giram 50 a duk cikin awa daya.
Abisola Olusanya ta kuma nuna jin dadin ta akan yadda aikin ke tafiya, inda ta kara da cewa, masana’antar zata kuma dinga sarrafa shinkafa tan-tan 32 a duk cikin awa daya.
A cewar Abisola Olusanya, noma da kuma samar da wadataccen abinci sune ke akan gaba a kudurin gwamnatin jihar Abisola Olusanya ta kuma nuna jin dadin ta akan yadda gwamnatin jihar ta mayar da hankali wajen ganin an kammala aikin akan lokaci yadda za a cimma burin da ake dashi na wadata jihar da shinkafar da kuma kasa baki daya.
Mai bayar da shwarar Abisola Olusanya ta ce, masana’antar ta na akan aka 8.5 kuma ako wanne sarrafa shinkafar da za’a yi sau biyu za a iya samar da tan-tan 16 inda zata kaiga an samar da buhunhunan ahinkafa 650 masu nauyin kilogiram 50 ako wacce awa daya .
A cewar Abisola Olusanya, na tsara masana’antar ce da kuma wadata ta da kayan aikin da suka dace wadda kuma yan kwangila na cifkin gida aka bai wa aikin da kuma injiniyoyin cikin gida.
Mai bayar da shawarar Abisola Olusanya ta ce, aikin masana’antar ta sarrafa shinkafar zai samar da dimbin ayyukan yi kai tsaye da kima wanda ba na kai tsaye ba sama da 250,000 da kuma kara habaka tattalin arzinin jihar Legas harda na kasa bakidaya idan an kammala aikin, inda ta kara da cewa, masana’antar ta Imota zata kuma dinga wadata yankin Ikorodu da kuma daukacin jihar da shinkafar.