Abubakar Abba" />

Manoman Shinkafa Reshen Legas Sun Yi Hayar Gonaki Kadada 200 A Epe

Kungiyar Manoman Shinkafa ta kasa reshen jihar Lagos (AFAN) ta sanar da cewa, ta samu filin noma mai kadada 200 a jihar don yin noman Shinkafa a yankin Epe

Shugabanta Mista Femi Oke ne ya sanar da hakan a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa a jihar, inda ya ce, manufar ita ce itama kungiyar ta shiga cikin fannin na noman Shinkafar da kuma kara samar da ayyukan yi a jihar.

Shugaban Mista Femi Oke ya yi nuni da cewa, Gwamnatin Tarayya ta samar da damarmaki masu ximbin yawa, mussmman kan ci gaba da akyinda garkame iyakokinnkassr nan da gwamnatin a mwatannin baya ta bayar da umarnin ayi don dakile shigo da kaya ta hanyar fasakauri.

A cewar Shugaban Mista Femi Oke, kungiyar ta samu gilinnne a karkashin yarjejeniyar jingina ta tsawon shekaru biyar, inda Shugaban Mista Femi Oke ya kara da cewa, kungiyar reshen jihar ta yi shiga fannin na noman Shinkafar ce don ta bayar da nata gudunmawar wajen samar da wadataccen abinci, kasa baki xaya ta hanyar samar da tan-tan na Shinkafar da zata samar duk shekara.

Shugaban Mista Femi Oke ya ci gaba da cewa, munyi amanna cewar, zamu noma tamu Shinkafar a wannan kakar noman Shinkafar mai zuwa.

Shugaban Mista Femi Oke ya sanar da cewa, mun kuma baiwa yayan kungiyar mu kwarin gwaiwar dasu noma Shinkafar koda yar kaxan ce yadda muma zamu bayar da gudunwa wajen kara yawan tan-tan na Shinkafar da ake bukata a kasar nan.

Shugaban Mista Femi Oke ya kuma bayyana cewa, akwai mutane da dama da suke son su rungumi yin noman Shinkafar a yankin na Epe, inda Shugaban Mista Femi Oke ya kuma yi nuni da cewa, hakan zai taimaka matuka wajen kara wada kasar nan da abinci mai ximbin yawk wanda har za’a gitar dashi zuwa wasu kasashen duniya don siyarwa.

Shugaban Mista Femi Oke ya bayyana cewa, yayan kungiyar suna noma ko wanne irin amfanin gona, inda ya buga misali da cewa, yayan kungiyar ta AFAN suna yin sana’ar kiwo, noma kayan lambu, kiwon Aladu, noman Shinkafa da kuma sauran fannonin aikin noma.

Shugabanta Mista Femi Oke ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohin dake kasar nna dasu taimakawa manoman na Shnkfa da kayan aiki na zamani yadda zasu samu damar noma Shinkafar mai yawa a kasar nan wadda zata iya wadar kasar nan da kuma fitar da ita zuwa kasashen waje.

A cewar Shugabanta Mista Femi Oke, manoman kasar nan, musamman waxanda suke a karkara suna fuskantar matsalar rashin kyawawan hanyoyi, inda hakan yake zamar masu babbar matsala wajen safaffar amfanin gonar da suka noma zuwa gidanjen da kuma kasuwanni.

Shugaban Mista Femi Oke ya sanar akwai bukatar gwamnatin data buxe hanyoyin dake a karkara, waxanda kuma suke haxa kauye da kauye, kamar yadda kungiyar ta yi a kadada 200 da kungiyar ta samar a garin na Epe.

Shugaban Mista Femi Oke ya kara da cewa, kuxin buxe hanyoyin yana da tsada sosai, a saboda hakan, akwai bukatar gwamnatin data kawo mana xauki don kungiyar ta cimma burin da ta sanya a gaba na noman na Shnkfar a garin Epe.

A cewar Shugabanta Mista Femi Oke munyi hayar gonakan yanzu kuma abinda ya rage mana shine mu fara sharar gona, inda Shugaban Mista Femi Oke ya kara da cewa, mafi yawancin irin waxannan amfanin gonar, suna da wa’adin su adan hakan ne muke son mu fara gudanar da aikin da wuri.

Shugabanta Mista Femi Oke muna bukatar gwamnatin data taimaka mana da kayan aiki, musa,mna kamar taraktocin yin nomad a kuma sauran kayan don mu cimma burin da muka sanya a gaba.

A cewar Shugabanta Mista Femi Oke, mun biya wasu kuxaxe kuma an kulla yarjejeniya da iyalan masu gonakan kan basu jinginar gonakan su don fara aikin na noman Shnkfar a jihar har zuwa shekaru huxu.

Shugabanta Mista Femi Oke, ya yi nuni da cewa, abinda ya rage mana a yanzu shine, fara gudanar da shirye-shirye, inda a yanzu, muke yin kira ga gwamanti data agaza mana don cimma nasara kan abinda muka sanya a gaba.

Shugabanta Mista Femi Oke , muna bukatar Gwamnatin Tarayya ta sanya a share wuraren yin noma da kuma samarwa da manoman dake kasar nan, musamman waxanda ke zaune a karkara hanyoyi yadda zasu samu saukin jigilar amfanin gonakan su zuwa gidajen su da kuma kasuwanni.

A cewar Shugabanta Mista Femi Oke, muna son Gwamnatin Tarayya ta taimaka tanbuxe dukkan wuraren yin noma da muke dasu a xaukacin jihohin kassr nan.

A karshe, Shugabanta Mista Femi Oke, in har Gwamnatin Tarayya ta mayar da hankali kan noman rani, za’a iya wadata kasar nan da abinci mai yawa a shekarar 2020.

A wata sabuwa kuwa, anyi nuni da cewa, abinda a yanzu yake kara bunkasa mata da alummar da ke a karkara a wasu jihohin dake cikin kasar nan shine shigar su cikin shirin sarrafa shinkafa da a turance ake kira ‘Out grower ‘ inda hakan ya sanya abin ya kara janyo ra’ayin su na shiga noman shinkafa a xsukacin faxin Nijeriya.

Sashen samar da kuxaxe da ciyar da aikin noma gaba na Majalisar Xinkin Duniya (IFAD), wata haxaka ce da akayi tsakanin Gwamnayin Tarayya da kuma kamfanin Olam dake a Nijeriya inda suka samar da shirin a shekarar 2015.

Shirin na (BCDP) dabara ce ta sarrafa shinkfa a karkara inda manoman suka kafa kungoyoyin noma. Manoman zasu dinga tura ingantacciyar shinkafa su a kuma dinga basu damar samun kuxi da adana ta da safarar ta zuwa cibiyoyin da za’a dinga sayen ta waxanda kuma tuni an basu horo kan tsarin (GAP) da kuma sayen shinkafar tasu.

Har ila yau, Kamfanin sarrafa Tumatir na Xangote dake a cikin jihat Kano, ya yo irin wannan jarjejeniyar da manoman Tumatir dake a jijar Kano.

Yadda shirin na sarrafa shinkafar na out-grower yake yin aiki shine, kamfanin Olam dake a Nijeriya shine yake samarwa da manoman kayan aiki, inda su kuma manoman, zasu samu damar samun kuxi da adana shinkafar su da kayan da zasu yi jigilarta ta zuwa cibiyoyin da za’a sayi ta.

A na sayen shinkafar ta manoman a cibiyoyin daidai da yadda farashin kasuwa ya kama, inda kuma ake turawa manoman kuxin su a cikin asusun ajiyar su na bankuna a cikin awanni 48 bayan an gama ciniki.

A cewar Mataimakin shirin aikin noma na kamfanin Olam Mista Reji George, tsarwar da akayi ta sayen shinkafar, jami’an gonar Olam dake a cinkn surkukin kauyuka sune suke tafiyar da kungiyoyin.

Mataimakin shirin aikin noma na kamfanin Olam Mista Reji George, ya ci gaba da cewa, “Waxannan jami’an su 30, sun buxe asusuna a banki ga ko wanne manomi xaya, yadda za’a dinga adanawa da kuma samun damar tare da tura kaya da kuma horon da aka bayar ga manomin dake cikin kungiyoyin.”

“Su na taimakawa ne don kada a karkatar da amfanin da kuma kaucewa ayyukan yan na kama waxanda suke ci da gumin manoman.”

A cewar Mataimakin shirin aikin noma na kamfanin Olam Mista Reji George, shirin ya kama kwamitin kayyade farashi da kwamitin haxaka da ya kunshi xaukacin masu ruwa da tsaki harda walilan manoman da aka xorawa nauyin yanke farashi kan yadda kasuwa ta kasance.

Ya cigaba da cewa, manoman da suka shiga cikin shirin, sun amfana da tallafin kayan aikin gona na zamani da shirin ya tanadar ta hanyar xaukin kuxi daga shirin ofishin jakadanci na kasar Japan GGP.

Mataimakin shirin aikin noma na kamfanin Olam Mista Reji George, ya ce, shirin ya bunkasa tattalin arzikin manoman kuma an fara BCDP ne a shekarar 2015 da manima guda 475, amma a yanzu, sun kai yawan 22,734 idan aka yi dubi kan yadda su ka karu zuwa manoma 35,000 kafin nan da shekarar in year 2020.

Mataimakin shirin aikin noma na kamfanin Olam Mista Reji George, ya ci gaba da cewa, “yawan manoman da suka shiga cikin kungiyoyin, su ma sun karu zuwa 1,164 daga 30 a shekarar 2015 kuma ayyukan na BCDP, an ga yadda sarrafa shinkafar ya karu zuwa 3.68MT/Ha sabanin kamar yadda a ka tsara a 2MT a shekarar 2015.”

Exit mobile version