Jakar Magori Tare da Nasir Chiromawa 07030863933 (Tes kawai)
Malaman tarihi sun ce, kafin zuwansa, zinari yana da matukar daraja a yankin Hijaz, amma zuwansa ke da wuya ya sauke darajarsa. Larabawa basu taba ganin zinari mai yawa irin wanda Mansa Musa ya kawo Haramin Makka da na Madina ba. Tun daga wancan zamanin zuwa yau zinari bai sake komawa darajarsa ta farko ba.
Bayan ya kamala aikin ibadar Hajji, sai ya daura niyyar komawa kasarsa, sai ya nemi Sharif wanda ke mulkin Makka da ya bashi Malamai wadanda za su taimaka wajen karfafa sha’anin addini a Daularsa.
An sanar da wannan bukata tasa a Masallantan Haramin Makka da na Madina, wannan dalili ya sa Malamai da dama suka yi burin bin sa, a karshe dai ya tafi da mutane dari daga Makka da Madina, wadanda suka kasance malamai ne daga bangarori da dama na fannonin ilimi. Haka nan daga cikin wadannan Malamai dari an zabo wasu daga zuri’ar Sharifai, wasu kuma zuriyar manyan Sahabban Manzon Allah (SAW).
Ya tashi tare da wannan tawaga da zummar komawa Afirka, mutanen Makka da na Madina sun yi bakin cikin rabuwa da shi, sun yi burin ina ma ya kasance a cikinsu. Sarki Mansa Musa ya ratsa ta gabar ruwan Maliya da nufin komawa gida.
An ce lokacin da ya shiga jirgin ruwa sai ya mike tsaye ya kalli yankin Hijaz ya daga hannu ya yi addu’a sannan ya yi bankwana da kasa mai tsarki.
Kamar yadda muka karanta a baya, Sarki Mansa Musa ya yi haramar komawa gida tare da tawagarsa da kuma Malaman da ya taho dasu wadanda yake fatan za su taimaka wajen karfafar sha’anin addini Musulunci a yanki Afirika ta yamma.
Lokacin da ya shiga jirgin ruwa sai ya mike ya dagawa dubun dubatar Larabawan da suka yi masa rakiya har gabar teku hannu, ya yi musu sallamar bankwana, sannan sai ya koma ya zauna akan karagarsa dake cikin jirgin, ya nausa cikin Maliya.
Wannan aikin Hajjin da ya yi ya jawo hankalin duniya daga kowacce Kusurwa. Labarin karfin arzikinsa ya girgiza Sarakunan duniya, ba ma kawai a yankin Larabawa ba, hatta ga sarakunan kasashen Turai da na yankin gabashin duniya.
Malaman tarihi sun tabbatar da cewa wannan ziyarar ce ta ga jawo hankalin duniya zuwa ga nahiyar Afirika, kuma an yi amannar cewa kasashen Turai irinsu Jamus da Faransa da Andulusiya da kuma kasar Ingila, sun samu haske game da dukiyar da take dankare a wannan nahiya, hakan ne yasa ‘yan leken asiri daga kasashen na Turai suka yi ta kwararowa ta teku wasu kuma tsakiyar sahara domin shigowa yankin, an ce hakan shi ne ya bude kofar da ta kai ga tunanin yi wa nahiyar Afirika mulkin mallaka.
A hanyar dawowarsa gida, Sarki Mansa Musa ya sake biyowa ta kasar Misira inda ya sake samun tarba ta ban mamaki. A lokacin ne ya samu zarafin ganawa da wasu daga cikin sarakunan Larabawa da suke yankin Magarib, da kuma wasu mashahuran malamai. Inda har ya samu kyautar littattafai daga Malaman na Misira.
Akan hanyar tasa ne ya sake biyowa ta dausayin nan da yasa aka yiwa matarsa a lokacin da ta bukaci ta huta daga tsananin zafin ranar da ta fuskanta a lokacin tafiyarsu.
A nan suka sake yada zango, inda suka tarar da dausayin yana nan cike da bishiyoyin ni’ima kamar yadda suka tafi suka bar shi, An sake kafawa amaryar tasa tanti inda sake hutawa tsawon lokaci.
Labarin soyayyar da yake yi wa wannan amaryar tasa ya yadu bama kawai a kasarsa ba, da sauran garuruwa, an ce lokacin da ta gama hutawa ta bukaci tawagar ta ci gaba da tafiya, shi ne da kansa ta ya hade tafin hannunsa biyu ta taka ta shiga cikn darbukar dake kan rakumi.
Wannan dausayi ya wanzu tsawon lokaci, domin Fatake dake kai kawo a tsakanin yankin yammacin Afirka da yankin kasashen Larabawa, sun mayar da wannan dausayi wani zango da suke hutawa a cikin sahara, an jima ana cin moriyarsa kafin daga bisani sahara ta binne shi.
A cikin watan Jimada Akhir, a tsarin kalandar Musulunci, Sarki Mansa Musa ya koma gida, inda ya samu jama’arsa wadanda suka yi farin ciki da dawowarsa. A lokacin ne ya tara jama’arsa ya bayyana musu irin alheran da ya taho musu da su daga yankin Hijaz.
Kamar yadda muka fada a baya, ya samu damar tahowa da malamai masana a bangarori ilimi da dama, daga cikin Malaman da Mansa Musa ya taho da su sun hada har da mashahurin mutumin nan masanin tsarin gine gine wato Ishak Al Tajudeen wanda bayan isarsa daular, ya zana tare da ginawa Mansa Musa kasaitacciyar Fadar nan ta Madagou.