Mansa Musa: Mutumin Da Ya Fi Kowa Arziki A Tarihin Duniya (3)

JAKAR MAGORI:

Tare da Nasir Chiromawa 07030863933 (Tes kawai)

Hankalin rundunar Musulmi ya yi matuƙar tashi domin sun fahimci cewa ba ya ta haihu, labarin da ya riske su cewa rundunar Jihadin Kirista (Crus) na daf da karɓe iko da Misira babbar Cibiyar Mulkin Daular Ayuby, birnin da Musulmin suka ɗauka a matsayin zuciyar Musulunci ba ƙaramin tayar musu da hankali ya yi ba.

Manyan Kwamandojin Rundunar Musulmai sun bayar da shawarar janye wa daga fagen dagar, domin komawa da baya da nufin kare Misira daga faɗawa hannun Kiristoci. Wannan shawara ba ta samu karɓuwa a wajen Salahuddin ba, domin ya bayyana musu cewa Mallakar birnin Ƙudus ya fi Misira muhimmanci a wajensa.

Babbar rundunar Kiristoci da ta nufi Misira tana ƙarƙashin babban Kumanda nan Raynaid na Chatillon, shine ya jagoranci rundunar ya durfafi Misra da mayaƙa masu tarin yawa. An tsara cewa bayan karɓe iko da Misira, sai kuma ya haura ta gaɓar ruwan Maliya ya nufi Makka da Madina.

Idan har Raynaid na Chatillon yayi nasarar murƙushe haramin Makka da na Madina, daga nan sai ya juyo da rundunarsa ya biyo biyo ta cikin sahara ya tunkari Salahuddin da rundunarsa, ta yadda za ayi masa ƙofar rago, kafin ya cimma birnin Ƙudus.

A can daya ɓan garen kuma Sarkin Ingila Richard da tasa tawagar sunyi shan bante sun challaka gaɓar ruwa sun nufi haryar da zata kaisu birnin Ƙudus. Dubun dubatar Jarumai cike da shauƙi suna faman haɗuwa da rundunar Musulmai domin su ɗanɗana musu azaba.

Rudunar da take gaba wacce take ɗauke da tutoci da kuma wani ƙaton Gicciye (Cross) zaratan Jarumai ne, ‘yan takife, wasu daga cikinsu an ɗauko hayarsu ne da sassa daban daban na Turai, kuma tuni Paparoma ya yi musu albishir da Aljanna.

Salahudin ya zaɓi mutane 500 biyar aga cikin rundunarsa ya umarce su da koma domin su kare Misira daga farmakin Kiristoci, da farko wasu daga cikin Kwamandojinsa sun nuna shakku akan yadda rundunar mutum ɗari biyar za ta iya tunkarar gagarumar rundunar da Raynaid na Chatillon ke jagoranta.

Amma daga bisani Salahuddin ya ƙarfafi zuƙatansu inda ya bayyana musu cewa Musulmi ɗaya mai taƙawa kan iya tunkarar mutum goma. Don haka ba tare da ɓata lokaci ba wannan runduna ta mutum 500 biyar ta yi harama, suka nufi Misira ta gaɓar ruwa.

Lokaci da suka isa tuni Rundunar Raynald ta kusa cimma Misira, anane aka gwabza mummunan faɗan da Kiristoci suka sha mamaki, ta yadda duk da irin yawan da suke dashi da kuma makaman da suka mallaka, sai da Musulmai suka danna su baya, suka ruguza musu shiri.

Daga yanki kudu da Sahara, an samu ɗauki daga Sarakunan Buzaye, waɗanda suka kawowa rundunar Salahuddin ɗauki, jaruntakar da Buzaye da ‘yan ƙabilar Kurɗawa suka nuna a wannan yaƙi yayi matuƙar bawa Larabawa mamaki.

A kan dole Raynaid na Chattilon ya juyar da akalar rundunar Kiristoci suna koma wa da baya, ba tare da samun nasara ba, suka bi ta gaɓar ruwan Red Sea, suka sauya hanya. A wannan lokacin ne suka tare jiragen ruwan dake ɗauke da Musulmai ‘yan kasuwa da kuma Mahajjata inda suka ɗanɗana musu baƙar azaba, suka yi musu wasoso da kuma yi musu kisan kiyashi.

Labaran abubuwan da suka faru a wannan karon battar ya riski Manyan Sarakunan nan biyu masu wakiltar addinai. Richard ya yi matuƙar baƙin cikin rashin wannan nasara da Kiristoci suka yi na kasa kama Misira, inda ya sake shan alwashin ba zai cire sulkensa ba sai ya cimma burinsa na kare birnin Ƙudus kafin daga bisani ya isa Makka ya ɗanɗanawa Musulmai baƙar azaba.

Ɓarnar da Raynald na Chatillon ya yi wa Musulmi a tekun (Red Sea) ya yi matuƙar baƙantawa Salahuddin rai, domin wasu masana tarihin sun bayyana cewa, hatta ‘yar’uwarsa tana daga cikin waɗanda wannan lamari ya rutsa da su.

Ba tare da ɓata lokaci ba ya bada umarnin karɓe iko da gaɓar ruwan, sannan ya tashi jiragen ruwan guda 30 inda ya umarce su da su kai farmaki birnin Beirut wajen da ya yi tsammanin Raynaid da rundunarsa sun kafa sansani.

Manufar wannan farmaki shi ne karɓe iko da mashigar gaɓar ruwar kuma za ta daƙile kuzarin Kiristoci da sake ratsawa ƙasashen Musulmai domin kai farmaki. An ci nasarar karɓe iko da Beirut bayan kwashe lokaci mai tsawo ana gumurzu.

A yanzu Musulmai sun hara shanshanar birnin Ƙudus mai tsarki, sai dai mafarkin da suke na kama birnin tamkar haɗuwa ne da fatalwa cikin duhun dare.

Exit mobile version