Manufa Mai Dacewa Ta Sa Huldar Sin Da Afirka Samun Ci Gaba
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Manufa Mai Dacewa Ta Sa Huldar Sin Da Afirka Samun Ci Gaba

byCMG Hausa
3 years ago
Sin da Afirka

Yanzu mun yi ban kwana da shekarar 2022. Wasu abokaina dake Najeriya sun buga mun waya, suna cewa an gamu da tashin hankali, da annoba, da ambaliyar ruwa, da hauhawar farashin kaya, a shekarar da ta gabata, lamuran da suka sanya jama’a cikin wahala da bakin ciki, sai dai idan an duba yadda huldar dake tsakanin kasashen Najeriya da Sin ke samun ci gaba a kai a kai, to, za a yi farin ciki sosai.

Haka ne. Ko a cikin watan da ya gabata, ko a kasar Najeriya kadai, za a iya ganin dimbin sakamakon da aka samu, ta hanyar gudanar da hadin kai tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka.

  • Yadda Biranen Sin Suka Farfado Yana Aike Kyakkyawan Sako Ga Duniya

Misali, a ranar 6 ga watan Disamban bara, an gudanar da bikin mika wata sabuwar cibiyar fasahohin noma ta zamani a birnin Abuja, cibiyar da kasar Sin ta gina a matsayin wata kyauta, inda za a yi amfani da ita wajen horar da kwararrun ma’aikata fasahar aikin noma, da raya fasahohin zamani a wannan fanni.

Sa’an nan, a ranar 21 ga watan Disamban bara, wani kamfanin kasar Sin ya kammala aikin gina mataki na farko na layin karamin jirgin kasa a birnin Lagos, wanda shi ne layin karamin jirgin kasa mai amfani da wutar lantarki na farko a yammacin Afirka. Ana sa ran ganin wannan layin dogo ya taimaka wajen saukaka matsalar cunkuson mota a hanyoyin birnin Lagos.

Ban da wannan kuma, duk a watan Disamban da ya gabata, an kaddamar da aikin gina sabon ginin ofishin hedkwatar kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS a birnin Abuja, wanda kasar Sin ta ba da tallafin kudin gina shi da yawansa ya kai dalar Amurka miliyan 31.6. Wannan gini zai ba hukumomi guda 3 na kungiyar ECOWAS damar zama a wuri guda, maimakon yanayin da suke ciki yanzu na kasancewa a wurare 3.

Hakika a wannan zamanin da muke ciki, huldar kasa da kasa na kara zama mai sarkakiya, kana ana ta samun rikici tsakanin kasashe daban daban. Sai dai mene ne dalilin da ya sa huldar dake tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin take samun ci gaba a kai a kai, tare da samar da nagartattun sakamako?

Dalilin shi ne, kasar Sin tana yin hadin gwiwa tare da kasashen Afirka, a karkashin wata madaidaiciyar manufa, wadda ita ce: Nuna gaskiya da sahihanci da adalci.

Wannan manufa ta sa kasar Sin kallon kasashen Afirka a matsayin masu daidaito, maimakon nuna girman kai, da nuna sahihanci wa kasashen Afirka, maimakon neman tilasta musu wani abu. Yayin da take hulda da kasashen Afirka, kasar Sin ba za ta ce, “ya kamata ku koyi dabaruna, domin sun fi na kowa” ba. Maimakon haka, za ta tambaya, “mene ne kake bukata?” da kuma “Wane irin taimako zan iya ba ka?”

A kasar Madagascar, jama’a sun damu da wata hanyar mota da ta hada gabobin gabas da yamma na kasar. Ko da yake hanya ce mai muhimmanci, amma ta dade da lalacewa, lamarin da ya sa a kan shafe a kalla kimanin sa’o’i 12 a lokacin rani, da makwanni 2 a lokaci damina a wannan hanya. Wani lokaci ma, hanyar ta kan katse, ba a iya binta ko kadan. Daga bisani, gwamnatin kasar ta gayyaci wani kamfanin kasar Sin don ya yi wa hanyar kwaskwarima, aikin da aka kammala shi a watan Satumban shekarar bara. Yanzu an rage lokacin da ake dauka domin wuce hanyar zuwa sa’o’i 2 da rabi.

Ban da wannan kuma, a lardin Lusaka na kasar Zambia, jama’a sun dade suna fama da matsalar karancin ruwa. Don daidaita wannan matsala, wani kamfanin kasar Sin ya dauki nauyin gina wata ma’aikatar tace ruwa a kan kogin kaff na kasar, aikin da ya kammala a watan Yulin bara. Yanzu ma’aikatar na samar da ruwa mai tsabta da ya kai cubic mita dubu 50 ga mazauna wurin a ko wace rana.

Manufar kasar Sin ita ma ta sa kasar neman taimakawa kasashen Afirka samun hakikanin ci gaba, da alfanu, yayin da take hadin gwiwa da su.

Misali, a kasar Mali, an kammala aikin gina madatsar ruwa ta Gouina, a watan Disamban bara, wadda wani kamfanin kasar Sin ya dauki nauyin gina ta. Firaministocin kasashen Mali, da Senegal, da Mauritania, da Guinea dukkansu sun halarci bikin mika madatsar ruwan. Wannan babbar madatsar ruwa na da karfin samar da wutar lantarki da ya kai KWH miliyan 621 a duk shekara, wadda za ta taimaka sosai a kokarin daidaita matsalar karancin wutar lantarki da kasashen ke fuskanta.

A kasar Kenya, cibiyar nazarin fasahohin aikin noma ta Sin da Afirka ta yi gwajin noman farar masara irin na kasar Kenya, ta fasahar noma ta kasar Sin, a watan Afrilun bara, inda aka kara yawan masarar da aka girba da kashi 50%, zuwa kilo 2700 a kowa ce eka. Wannan karuwa ta ba manoman kasar Kenya mamaki sosai, duk da fari mai tsanani da kasar ta fuskanta a shekarar da ta wuce. Yanzu cibiyar nazarin na kokarin yayata fasahohin noma masu inganci a kauyukan kasar Kenya.

Ban da gudanar da ayyuka na hadin gwiwa tare da kasashen Afirka, kasar Sin ta ci gaba da kokarin bude kofar kasuwanninta ga kasashen, don ba su damar samun karin riba. A shekarar 2022, an fara shigar da ’ya’yan marmari na Avocado na kasar Kenya cikin kasuwannin kasar Sin, kana gwamnatocin kasashen Zimbabwe da Sin sun daddale yarjejeniyar sayar da lemun kasar Zimbabwe a kasuwannin kasar Sin. Ban da haka, kasar Sin ta yafe ma wasu kasashe 10 marasa karfin tattalin arziki, da suka hada da Benin, da Burkina Faso, da Guinea Bissau, da Malawi, da dai sauransu, harajin kwastam, na kashi 98% na kayayyakin da suke shigo da su zuwa kasar Sin.

Wasu na cewa, dalilin da ya sa kasar Sin ke kokarin kyautata hulda tare da kasashen Afirka, shi ne don neman habaka tasirinta a duniya. Sai dai a ganina, ko wace kasa tana iya yin tasiri a duniya, amma abu mafi muhimmanci shi ne a tantance burin da take neman cimmawa ta hanyar yin wannan tasiri.

Cikin jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, don taya murnar shiga sabuwar shekara ta 2023, ya ce har abada, kasar Sin tana darajanta zaman lafiya, da ci gaba, da abokai da aminanta. Za kuma ta tsaya kan tunani mai dacewa, don samar da gudunmowa ga kokarin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a duniya.

Daga kalaman shugaba Xi za mu fahimci cewa, kasar Sin ba ta da burin yin babakere a duniya, yayin da take hulda da sauran kasashe. Maimakon haka, tana kokarin neman ganin kare zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, da samun ci gaban daukacin bil Adama. Wannan buri ya sa kasar Sin take iya nuna sahihanci ga sauran kasashe masu tasowa, da daukarsu bisa matsayi na daidai wa daida, gami da kokarin hadin gwiwa da su don neman tabbatar da moriyar juna.

Wannan manufar hadin gwiwa mai dacewa, ta sa huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ta karfafa a kai a kai, yayin da ci gaban huldar bangarorin 2, da yadda take amfanawa junansu, sun tabbatar da gaskiyar manufar diplomasiyya ta kasar Sin, da mai da huldar Sin da Afirka abin koyi ga kasashe daban daban.

A shekarar 2023 da muke ciki, za a cika shekaru 10 da kasar Sin ta gabatar da manufarta ta hulda da kasashen Afirka, wato nuna gaskiya da sahihanci da adalci. Tabbas za mu iya gane ma idanunmu karin managartan sakamakon da hadin gwiwar kasashen Afirka da kasar Sin ta samar a cikin wannan shekara. (Bello Wang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?
Daga Birnin Sin

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
Next Post
RCEP Ta Samar Da Abin Koyi Ga Hadin Gwiwar Tattalin Arzikin Shiyya Shiyya

RCEP Ta Samar Da Abin Koyi Ga Hadin Gwiwar Tattalin Arzikin Shiyya Shiyya

LABARAI MASU NASABA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version