Ina yi wa mai karatu barka da Sallah, da fatan Allah ya muna mana ita lafiya, ya kuma maimaita mana ganin na wasu shekarun cikin yalwar arziki da lafiyar jiki da zaman lafiya.
Kusan na jima ina yin rubuce-rubuce akan irin abubuwan da kan faru a lokacin da ake bukukuwan Sallah, ba zan iya tuna takamaimen lokacin da na fara ba, amma ina iya tuna dalilin da ya sa hankali na ya karkata ga bukukuwan Sallah.
A wadancan shekarun, babban dalili shi ne; a duk ranar Sallah karama ko babba matasa kan yi gungu (a wasu garuruwan har su dinka kaya iri daya) su je wuraren da ake yin wasannin sallah. Wurin wasannin kan hada ‘yan unguwanni mabambanta, don haka sabani kalilan ya kan kunna wutar bala’in da sai an dangana ga kisan rai, ko in ce salwantar rayuka. An yi haka ya fi a kirga. Kamar a Kaduna wuraren da suka yi kaurin suna a wancan lokacin kan fadace – fadace har da kisa sun hada da; ‘Gamji Gate’ da ‘Galady’. Yanzu babu ‘Galady’ din sai Gamji ce ta saura a Kaduna.
Haka kuma a washegarin sallah, gungun matasan na sake ziyartar wadancan wurare, inda da zarar an hadu sai kuma a shiga batun daukar fansa, wanda a nan ma wasu rayukan ne ke salwanta. A hankali, wannan al’adar ta zama babba, a kusan garuruwa da daman gaske da ke Arewacin Nijeriya a na aikata hakan.
A irin wadannan wasanni da mota ko babur a lokutan bukukuwan sallah a kan samu rahotannin rasuwar rayuka da dama daga jihohi har ma da kauyukan jihohin. Wanda wannan babban abin lura ne da damuwa.
Iyaye su ne ke da kaso mafi tsoka a wurin dakile ire–iren wadannan al’adu a lokutan bukukuwan sallah, babu yadda za a yi gwamnati ta iya magance wannan abu ba tare da iyaye sun fara nasu aikin ba, ma’ana su sauke nauyin da Allah ya dora musu.
Idan da a ce kowanne Uba zai tsawatarwa dansa cikin nasiha da lalama tare da yi mishi bayanin irin hadarin da ke cikin shiga zugar masu irin wadannan al’adu da za a samu karancin rahotannin barna. Haka kuma idan iyaye za su rika bibiyan mu’amalolin ‘ya ‘yansu a lokutan wannan shagali na Sallah, shi ma zai bayar da daman su iya dakile yiwuwar afkawar matasa ga irin wadannan munanan dabi’u.
Wasu iyayen sun yi kokarin hana ‘ya ‘yansu ga shiga harkokin dabanci da kauranci. Amma yanzu babbar matsalar da ke fuskantar al’umma ta girmi dabanci da kauranci (duk da ita ma harkar dabancin ta fara dawowa a wata sabuwar siffar), wanda kuma idan Iyaye ba su dauki matakin gaggawa ba, karshenta sune za a bari da kukan takaici a kuma haifarwa da al’umma da annoba.
Kamar yadda al’amarin fasadin Luwadi ya zama ruwan dare; a wannan lokutan bukukuwan Sallah masu irin wannan dabi’a ta dabbobi zasu fake su yi ta bata kananan yara. Kwanakin baya na ke fadi ma wani abokina ya kamata mu yi bincike a kan dalilin da ya sa shaidanu ‘yan luwadi suke farmakar kananan yara. Idan Allah ya nufa za mu gabatar da wannan bincike mu fitar da nazari a kai.
Idan a shekarun baya al’amarin luwadi bai shigo kasar hausa sosai ba, toh yanzu kam ya shigo ya mamaye wurare da dama. Kusan kullum sai ka ji labarin an cafke wani dan iskan ya na aikatawa. Abin takaicin shi ne kaso 80 da a ke kamawa, su na aikatawa ne da kananan Yara da kuma Matasa. Wasu yaran ma basu da wayon bambancewa tsakanin fari da baki.
Tunda mun fahimci cewa wadanda suka fi fadawa tarkon ‘yan luwadi su ne ‘yan shekaru 7 zuwa 30. Dole ne iyaye su sa idanu sosai a kan duk wani motsin ‘ya ‘yansu. Ba ko ina ya kamata a kyale yara su rika zuwa ba, musamman ma ya kamata iyaye su rage yawan yawace-yawacen yara da sunan ‘yawon Sallah’.
Na biyu shi ne, akwai wasu kuma wadanda mutane ne, amma dabi’ar tamkar ta dabba. Su kuma wadannan, bata kananan yara mata su ke yi; Kamar ‘yan shekaru 5 zuwa 10. Su kan yi musu dabaru, tare da jan hankalinsu da sunan goron sallah. Saboda haka, a nan ma dole ne Iyaye ya zama sun takaita yawon ‘ya ‘yansu mata, saboda gudun sharrin dabba a rigar mutum.
Na uku shi ne yadda samari da ‘yan mata su ke yin amfani da lokacin sallah a matsayin ranakun da za a aikata zinace-zinace da masha’a. Iyaye na da karfin ikon hana afkuwar wannan masifa, ta hanyar takaita yawace yawacen su ‘yan matan.
Daga karshe zan so iyaye su fahimci cewa; ko dai su tashi tsaye wurin yiwa ‘ya ‘yansu garkuwa daga wadannan mugaye da shaidanun mutane, ko kuma a yiwa rayukan ‘ya ‘yan nasu katoton tabon da warkewarshi sai an yi zufa. Binciken masana halayyar jama’a da zamantakewa ya tabbatar da cewa, idan a ka fara aikata alfashar luwadi da Yaro ya na wahala ya daina. Idan kuma bai daina ba, dole ne zai bata wasu yaran da ya ke rayuwa da su. Idan Iyaye ba su motsa ba yanzu, sai yaushe?