Hukumar nan da ake kira da suna ‘National Lottery Regulatory Commission’, Wato hukumar kula da adashin tallafi ta ƙasa, wacce da zarar ɗan Nijeriya ya ji an faɗe ta, musamman kalmar ‘Lottery’, sai a ɗauka hukumar ayyukan abin da ke gabanta shi ne caca, ko kuma sa-ido wuraren da ake yin caca a sassan Nijeriya. Kan haka wakilinmu BALARABE ABDULLAHI ya sami daman zantawa da babban daraktan da ke kula da ɓangaren wayar da kan al’umma na hukumar, Malam ISA ABDUL’AZIZ SA’IDU, inda ya warware wa wakilinmu zare da abawa, da ya shafi ayyukan wannan hukuma, kuma ya yi tsokaci kan yadda ‘yan Nijeriya ke ɗaukar wannan hukuma. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Ya ku ke duban yadda ‘yan Nijeriya suke kallon wannan hukuma ta ku?
A gaskiya mafiya yawan ‘yan Nijeriya suna ɗaukar wannan hukuma ta mu cewar ta na da alaƙa da caca kai tsaye ko kuma fakaicce, to duk waɗannan tunani guda biyu babu ɗaya da hukuma ta mu ke da alaƙa da shi, wato batun caca da ake kallonmu da shi a wannan hukuma
To yanzu, waɗanne matakai ku ke ɗauka na yadda ‘yan Nijeriya za su fahimci ayyukan da gwamnatin tarayya ta ɗora muku?
Alal haƙiƙa ka akwai ayyuka da yawan gaske da mu ke ayyuka da mu ke aiwatarwa da kai tsaye suna da alaƙa da tallafa wa ‘yan Nijeriya, amma a baya mafiya yawan ‘yan Nijeriya bas u san waɗannan ayyuka ba, amma da mu ka motsa mun fara ganin canji daga al’ummar Nijeriya..
Tun da ka ce wannan hukuma ta na ƙarƙashin gwamnatin tarayya ne, to waɗanne ayyuka aka ɗora muku?
Ayyukan da aka ɗora mana sun haɗa da yadda a ke yin adashin tallafi a kowane ɓangare na ƙasar nan, wato yadda mutum ko ƙungiya za su bugi ƙirji su tara mutane su riƙa karɓar kuɗaɗensu ba tare da wani ko kuma wasu tsare-tsare ba, wanda a ƙarshe sai ka ga da wanda ke tara adashin gatar da wanda ya bayar da adashin duk sun tsunduma a cikin matsala.
Tun kafi ma ire-iren waɗannan matsaloli su taso,gwamnatin tarayya ta ɗora ma na alhakin ganin duk wanda yak e son wannan adashin gata, to wajibi ne ya zo hukumarmu, mu bashi ƙa’idodin yin adashin gata, in ya cika ƙa’idodin mu bas hi damar yin adashin gatan, in bai cika ƙa’idodin ba, mu dakatar da shi daga tara kuɗaɗen jama’a, kamar yadda ya ƙuduri aniyar yi.wannan kenan.
Shi kuma wanda ya zuba adashin gata, in ya sami matsala a tsakaninsa da mai zuba adashin, mutum ɗaya ne ko kuma kamfani, to sai ya zo hukumarmu, ya yi ma na bayanin matsalolin da suka faru a tsakaninsa da wanda yay i hulɗa da shi, ko kamfanin da yay i hulɗa da shi, sai mu tashi tsaye mu ga lallai mun karɓo masa haƙƙinsa da wanda yay a yi hulɗa da shi.To ka ga duk bayanan da na yii ma ka babu batun caca a ayyukanmu kenan.
Wato an kafa mu ne da maƙasudin duk wanda aka cutar da shi a adshin gata, mu bi masa haƙƙinsa ga wanda ya cuce shi ko kuma ga kamfanin da ya cutar da wanda ya zuba adashin gatan.Kuma in an sa wani gasa, bayan kammala gasar sai wanda ya ci gasar ya fuskanci rashin ba shi haƙƙoƙnsa daga waɗanda SUka shIrya gasa, ba tare da ɓata lokaci ba za mu shiga matsalar, mu taimaki wanda aka hana shi kyautar da aka ce za a ba wanda ya sami nasara.
Wannan hukuma ta na bayar da tallafi ne ga ‘yan Nijeriya?
Kuma kamar yadda na shaida ma ka a baya, in ka sayitikitn shiga adashin, sai aka canza ƙa’idodi, ba gaya ma k aba, in ka shaida ma na za mu bi ma ka haƙƙin ka.Wato in aka ce duk wanda ya yi kaza za mu bas hi ka za, to kafin a fara sai mun ga tsarin zahiran na abin da ya ce, zai bayar.
Har bankuna kuna shiga domin biyan mutum haƙƙinsa?
Ai babu inda ba mu shiga, in dai an yi mana kuka.Misali, in banki suka ce, in ka je ka za za mu ba da rancen ka za, to mu kan tabbatar duk wanda ya cika sharuɗɗan an ba shi abin da ya nema ba tare da wani ɓata lokaci ba.Wato kamar masu ajiya a banki, ka aje Naira miliyan ɗaya, bankin suka ce, in ka bar wannan kuɗi ba tare da ka taɓa ba, bayan shekara ɓaya, za mu ba ka naira ka za,to in ka sami matsala da bankin da zarar ka shaida ma na za mu bi wa wanda yay i ma na kuka .Za mu tabbatar sun tura wa wanda ya aje kuɗin alƙawarin da aka yi masa na tura masa alƙawarin a cikin asusunsa da wannan banki.
Wasu matakai ku ke ɗauka ga masu shirya adashin gata da suke karkara,na yadda bas u yin wasu tsare-tsare masu inganci,a ƙarshe ma sai ka ga an gudu da kuɗaɗen jama’a?
Muna da tsarin sa ido ga ire-iren waɗannan mutane da ka ambata,in an kawo ma na kuka,mu kan buƙaci mu zauna teburi guda da su,domin ganin tsarin yadda za su kula da dukiyan al’umma da suke karɓa.Kuma sai hukumarmu ta ga kuɗin da asusunsa na banki da kuma cikakken adireshinsa,duk muna yin haka ne,ka da ya tattara kuɗaɗen jama’a ya gudu.In ya cika ka’idodin da hukumarmu ta tsara,za mu bas hi lasisin amincewa da yin adashin gata a tsakanin al’umma,kuma lasisin shugaban ƙasa ne da kansa ke sa hannu.Da zarar an bas hi wannan lasisin an amince da shi kenan yay i adashin gata a tsakanin al’umma.
Akwai wani haraji da ake biyan gwamnati daga mai adashin gatan a ƙarshen shekara?
Babu ko shakka, a kwai haraji da ake biyan gwamnatin tarayya,kuma duk yadda ake biyn harajin ya na cikin tsare-tsaren da mu ke sa ido a kai.Duk kuɗaɗen harajin da aka biya,mu kan sa shi a lalitar gwamatin tarayya,wanda da ire-iren waɗannan kuɗaɗe ne gwamnatin tarayya ke amfani da su wajen yi wa ‘yan Nijeriya ayyukan ci gaba a sassan ƙasar nan.
Daga Ƙarshe, wannan ofishi naku dake Kaduna, ya ƙumshi jihohi nawa ne?
Wannan ofishi da nan Kaduna,ya ƙunshi jihohin arewa maso yamma,wato jihohin Kaduna da jihar Neja da jiharKatsina da jiharkano da kuma wasu jihohi da wannan jihar ke kula da su,amma duk ofisoshin wannan hukuma da suke Nijeriya, babbar ofishinmu ya na Abuja.