Manufofi Da Mu’amalolin Nijeriyar Jiya Da Kasashen Ketare

Daga Muktar Anwar,

Duba da irin yadda Nijeriyar Jiya ta mu’amalanci Kasashen Duniya gabanin wannan mawuyacin lokaci ko yanayi da muke ciki, babu makawa wajen yin jinjina ga wadanda suka dauki-gabaren tafiyar da irin wadancan mu’amaloli a jiyan.

Binciken masana na nuna cewa, wasu gwamnatoci da suka shude cikin wannan Kasa, sun tashi tukuru, wajen tabbatar da cewa wannan Kasa ta Nijeriya ce ahakku kuma mafi cancanta wajen jagorantar daukacin wannan nahiya ta Afurka da muke ciki. Sannan, ba da karadi ko kwarewa wajen yada farfagandar iska ne wadancan gwamnatoci da suka shude ne, suka samu sukunin kai wa ga yi wa Afurkan jagoranci ba, face da aiki ne tukuru na zahiri.

Babu shakka masharhanta kan ciri tuta ne ga wasu gwamnatocin da suka gabata a jiya cikin wannan Kasa, cikinsu akwai gwamnatin Janar Yakubu Gowon mai ritaya, inda gwamnatin ta tashi a aikace, wajen ganin ta kawo dorarren hadin-kai cikin wannan nahiya ta Afurka, yunkurin da a yau din nan da ake ciki, za ka rasa takamaiman wani shugaba daga shugabannin Afurka, da ke taka irin makamanciyar rawar da Gowon ke takawa a lokacinsa.

Ta tabbata cewa, Gowon ne babban wanda ya taka muhimmiyar rawa, wajen samar da kungiyar da ke da muradin bunkasar tattalin arzikin kasashen Afurka ta yamma, wato kungiyar ECOWAS “Economic Community of West African States”. Har kawo yanzu, wannan Kungiya na nan, sai dai irin aiyukan da ta gabatar a jiya, wadanda karara ke yin nuni da sanya muradan Afurka ne a gaba farko ba na Turawa ba, an rasa irin wannan cikakkiyar akida tattare da shugabannin Afurkar yau, tamkar ta jiya. Kasashe su dunkule wuriguda, suna masu kishin juna gami da bai wa juna kariya, ta irin wannan gamayya ne kudurorinsu da manufofinsu kan sami cimmuwa, tare da tsintar kai bisa tudun-mun-tsira. Shi yasa, duk da karfi na tattalin arziki da karfin soja da za a ga daidaikun Kasashen Turai ke da, bai isa ba, sai da suka samar da kakkarfa kuma gawurtacciyar kungiyar EU “European Union”.

Kungiyar da ba ka isa ka ce akwai wata nahiya a Duniyar yau, da ke juya akalar wannan mashahuriyar Kungiya ba. Amma kungiyar ECOWAS fa?.

Ya wuce ma ana juya ta, hantsila ta ne ma ake yi a yau. Takaicin da ba a faye kwalli da shi ba a jiya, lokutan su Gowon da marigayi Murtala.

Masana sun hakkake cewa, a Nijeriyar Jiya, lokacin gwamnatin Murtala da Obasanjo (1975-1979), Nijeriya ce kangaba, cikin dukkanin lamuran da suka shafi nahiyar Afurka. Bugu da kari, a lokacin, za a samu cewa manufofin alaka da Kasashen Duniya da Nijeriya ke gabatarwa, za a samu cewa tana yin la’akari ne da maslahar Kasashen Afurka farko, ba maslahar masu jajayen kunne Turawa ba.

An sami tashin-gwauron-zabin kar6uwar kyawawan manufofin Nijeriyar Jiya, lokacin da Kasar tayi-uwa, tayi-makar6iyar cewa, tilas dole ne sai an bai wa Kasar Afurka ta Kudu (South Africa) cikakken “yancinta na cin-gashin-kai daga azzaluman Turawa “yan kama-waje-zauna. Irin wannan kumaji abin nema na manufofin Nijeriyar ta Jiya, sai hakan ya tilasa Majalisar Dinkin Duniya ba ta jagorancin Kwamitin da ke yaki da nuna wariyar launin-fata na Majalisar ta Dinkin Duniya “UN Anti-Apartheid Committee” (Jega and Farris, 2010 : 4–5).

Kima, karfi da kwarjinin Nijeriyar Jiya, ta-kai ta-kawo cewa;

“…If Nigeria wasn’t at a table where African issues were discussed (the discussion) is incomplete”.
(Eze 2009) (Jega and Farris, 2010 : 5).
Abinda wancan Turanci na sama ke cewa shi ne, a lokacin da Nijeriyar Jiyan ke kan sharafinta game da manufofinta na Kasashen Ketare, ya tabbata cewa, a duk sa’adda aka hadu bisa wani teburi da zimmar tattauna batutuwan Kasashen Afurka, muddin dai Nijeriya ba ta wannan waje, to fa an yi ba a yi ne ba. Ma’ana, da sauran magana, saboda magana ba ta kammalu ba ke nan. Abin nufi karara shi ne, Kasar ta Nijeriya, na da kwarjini da karfin warware duk wani hukunci da za a nemi zartarwa a halin ba ta nan, indai za a yi wani batu ne game da wata Kasa a Afurka. Shin, Nijeriyar Yau na da irin wancan karsashi da kumaji irin na Jiya?. Hujja?
Ka da garin tuya a mance da albasa, gwamnatin shugaba Tafawa Balewa ma a bar a jinjinawa ce, idan a na magana game da kyawawan manufofin mu’amaloli irin na kasa da kasa da su ka afku a Nijeriyar Jiya. A lokacin Balewan, Kasar Faransa (France), ta tasamma yin gwajin makaminta na kare-dangi a dajikan Sahara da ke a nahiyarmu ta Afurka, amma nan da nan ne gwamnatin Balewan ta soki wannan shiri na Faransa da kakkausan harshe. Sai da aka wayigari dangantaka ta yi tsami a tsakanin Kasashen biyu.

Bugu da kari, gwamnatin ta Balewa, ta tashi haikan wajen yunkurin samar da zaman lafiya a Kasashe irinsu Congo da Lebanon. Sannan, kasar ta Nijeriyar Jiyan ce ta dakile wani yunkurin juyin mulkin da aka tasamma yi a kasar Tanzania.

Nijeriyar Jiyan ce dai ta karkashin kasa, ta rika antayawa kungiyar bakaken fata ta ANC, ta su marigayi Mandela da ke a kasar South Africa, wajen yakar ta’addanci miyagun Turawan mulkin mallaka, har zuwa lokacin da suka kwaci “yancin nasu. Ba kungiyar ECOWAS kawai ba, hatta ma yayin samar da kungiyar hadin-kan Kasashen Afurka ta AU “African Union”, babu wata Kasa a duk fadin Afurka, da ta taka rawa sama da Nijeriya (Nijeriyar Jiya). Malam, ba abin mamaki ne ba “yan Nijeriyar Yau, musamman wadanda ba su yi wayo ba, koko ba a haife su ba, lokacin da Nijeriyar Jiya ke taka irin waccan kasaitacciyar rawa abar bege, su ga tamkar ma suna cikin magagin barci ne, koko ma tamkar zuki-ta-malle ne kawai ake kwarara musu.

Exit mobile version