Manufofin Da Suka Sa Aka Haramta Zina

Hukuncin

Assalamu alaikum malam ina son karin bayani game da manufofin shari’a a kan haramta zina.

 

Wa alaikum assalam Addinin musulunci ya zo don ya kare tsatson Dan’adam da mutuncinsa, don haka ya shar’anta aure kuma ya haramta zina, ga wasu daga cikin hikimomin da haramta zina ya kunsa :

 1. Katange mutane daga keta alfarmar shari’a.
 2. Samar da Dan’adam ta hanya mai kyau, ta yadda za’a samu wanda zai kula da shi, saboda duk wanda aka same shi ta hanyar zina, to ba za’a samu wanda zai kula da shi ba yadda ya kamata.
 3. Saboda kada nasabar mutane ta cakudu da juna.
 4. Katange mace daga cutarwa, ita da danginta, saboda zina tana keta alfarmar mace, ta zamar da ita ba ta da daraja.
 5. Kare mutane daga cututtuka, kamar yadda hakan yake a bayyane.
 6. Toshe hanyar faruwar manyan laifuka, miji zai iya kashe matarsa, idan ya ga tana zina, kamar yadda mace za ta iya kashe kwartuwar mijinta, daga nan sai a samu daukar fansa, sai fitintinu, su yawaita.
 7. Zina tana kawo gaba da kiyayya a tsakanin mutane.
 8. Kare mutuncin yaron da za’a Haifa, domin duk yaron da aka Haifa ta wannan hanyar zai rayu cikin kunci. Allah ne mafi sani.

 

Hukuncin Sakin Mai Haila

Malam mun samu rikici da matata ko ya halatta na sake ta tana haila?

 

Ya haramta a saki mace lokacin da take haila, saboda fadin Allah “Ya kai Annabi idan za ku saki mata, to ku sake su a farkon iddarsu) Suratu Addalak aya ta farko, wato a farkon  tsarkin da ba ku take su a cikinsa ba. Ana nufin a halin da za su fuskanci idda sananniya, wannan kuwa ba ya faruwa sai idan ya sake ta tana da ciki ko tana cikin tsarkin da bai take ta ba, domin idan ya sake ta a cikin haila to ba ta fuskanci idda ba, saboda hailar da ya sake ta a ciki ba za’a kirga da ita ba, haka kuma idan ya sake ta tana da tsarki bayan ya sadu da ita, domin bai sani ba shin ta dauki ciki ta yadda iddarta za ta zama irin ta mai ciki ko kuma ba ta dauka ba ta yadda za ta yi idda da haila, saboda rashin tabbacin haka sai sakin ya haramta. Ya tabbata a cikin Bukhari da Muslim cewa: Ibn umar ya saki matarsa tana haila, sai Umar ya bawa Annabi (SAW) labari, sai Annabi ya yi fushi, sai ya ce “ka umarce shi ya mayar da ita sannan ya rike ta har ta yi tsarki sannan ta yi haila, sannan ta yi tsarki, sannan in ya so ya rike ta ko kuma ya sake ta kafin ya sadu da ita, wannan ita ce iddar da Allah ya umarta a saki mata a ita” ana togace gurare guda hudu wadanda sakin mace mai haila yake hallata:

 1. Idan sakin ya kasance kafin ya kadaita da ita ko kafin ya sadu da ita, to anan ya halatta ya sake ta tana haila, saboda anan bata da idda, sakinta ba zai zama ya sabawa fadin Allah madaukaki (Ku sake su a farkon iddarsu) ba.
 2. Idan ta yi hailar ne tana da ciki
 3. Idan ya sake ta ne bayan ta fanshi kanta, (KUL’I) to a nan babu laifi ya sake ta tana haila
 4. Idan ya yiwa matarsa I’laa’i kuma aka yi watanni hudu bai dawo ba.

Allah ne mafi sani.

………………..

Hukuncin Wanda Ya Auri Mace Saboda Kyanta

 

Malam: Akwai wani hadisi da yake Magana kan cewa kowa  ya auri mace kawai dan kyanta Allah zai hana masa jindadin kyan, ko dan kudinta Allah zai hana masa jin dadin kudin,. Shin hadisin akwai shi kuma ya inganta?

 

Ga yadda hadisin ya ke: “Duk wanda ya auri mace saboda kudinta, allah zai kara masa talauci, duk wanda ya auri mace saboda kyawunta allah zai kara masa muni”. Sai dai a cikin hadisin akwai Abdussalam bn Abdulkuddus wanda yake rawaito hadisan karya, don haka hadisin bai inganta ba, kuma ba za a kafa hujja da shi ba.

Allah ne mafi sani.

………………………………

Ya Yaga Takardar Sakin Kafin Matarsa Ta Gani, Ya Hukuncin Yake?

Assalamu alaikum, malam shin idan mutum ya rubuta takardar saki ya aje, sai wani ya gani shin matar ta shi tasaku?

 

Wa alaikum assalam To malam matukar ya rubuta da niyya kuma yana cikin hayyacinsa ba takura masa aka yi ba, to ta saku, saboda fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi : “Allah ya yafewa al’umata abin da ta riya a zuciyarta, mutukar bata fada ba, ko ta aikata” ka ga kuma rubutu aiki ne.Kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana zartar da abubuwa da yawa ta hanyar rubutu, ka ga ya zama hujja kenan. Wannan shi ne mazahar Abu-hanifa da Malik kuma shi ne zancen Shafi’i mafi inganci. Duba Al-mugni : 7\486 Allah ne mafi sani

 

 

Exit mobile version