CRI Hausa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home DAGA BIRNIN SIN

“Manufofin Kasar Sin” Sun Nuna Goyon Baya Ga Ra’ayin Cudanyar Bangarori Da Dama

by CRI Hausa
July 31, 2020
in DAGA BIRNIN SIN
2 min read
“Manufofin Kasar Sin” Sun Nuna Goyon Baya Ga Ra’ayin Cudanyar Bangarori Da Dama
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

“Kamata ya yi bankin AIIB ya kasance wani sabon dandamali na kasashe mambobinsa, wanda zai inganta samun bunkasuwa tare, da raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dan Adam.” Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana haka ne a jiya Talata, a yayin taron shekara-shekara ta kafar bidiyo na bankin zuba jarin samar da ababan more rayuwa na Asiya ko AIIB a takaice karo na 5, inda kuma ya gabatar da manufofi guda hudu a fannin, tare kuma da jaddada cewa, za a yi kokarin raya bankin, ta yadda zai kasance wani sabon bankin raya kasa na bangarori da dama, kuma sabon dandamalin gudanarwa dake dacewa da halin da ake ciki, kuma wata sabuwar hukumar hadin kan kasa da kasa bisa babban ma’auni, da kuma sabon misalin koyo na hadin kai tsakanin bangarori da dama na kasa da kasa.
Bisa yanayin da ake ciki na yaki da annobar numfashi ta COVID-19 da tsanantar halin tattalin arzikin duniya, irin manufar da Sin ta dauka, ta nuna tsayayyen goyon baya ga ra’ayin cudanyar bangarori da dama, wadda ta kuma nuna siffar kasar Sin a matsayin wata babbar kasa dake sauke nauyin kanta.
A cikin shekaru hudu da wani abu da suka wuce, yawan kasashe mambobin bankin AIIB ya karu daga 57 a farkon lokacin kafuwarsa zuwa mambobi 102. Ya zuwa yanzu dai bakin ya riga ya zuba jarin kusan dala biliyan 20 a fannin ababen more rayuwa.
Game da manufofi guda hudu da shugaba Xi Jinping ya gabatar, tsohon karamin jakadan kasar Poland dake birnin Shanghai na kasar Sin Sylwester Szafarz ya nuna amincewa sosai gare su. A ganinsa, manufofin za su taimaka wajen warware wasu matsalolin kasa da kasa da ake fuskanta a yanzu, za kuma su samu tsayayyen goyon baya daga wajen dukkan kasashe mambobin bankin, ciki har da kasarsa Poland. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

SendShareTweetShare
Previous Post

Yau Musulmin Duniya Ke Fara Ruguntsumin Babbar Sallar

Next Post

Al’ummar Kabilar Tibet Sun Fita Daga Talauci Bisa Manufofin Gwamnatin Kasar Sin

RelatedPosts

Gyara Kayanka Baya Zama Sauke Mu Raba

Gyara Kayanka Baya Zama Sauke Mu Raba

by CRI Hausa
21 hours ago
0

Majalisar Dinkin Duniya da Kwamitinta na sulhu, sun yi kakkausar...

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Ziyarci Cibiyar Wasan Dusar Kankara Ta Kasa

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Ziyarci Cibiyar Wasan Dusar Kankara Ta Kasa

by CRI Hausa
21 hours ago
0

Yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci birnin...

Pakistan Ta Amince Da Amfani Da Rigakafin COVID-19 Na Sinopharm A Matakin Gaggawa

Pakistan Ta Amince Da Amfani Da Rigakafin COVID-19 Na Sinopharm A Matakin Gaggawa

by CRI Hausa
22 hours ago
0

Hukumar kula da ingancin magunguna ta Pakistan (DRAP) ta amince...

Next Post
Al’ummar Kabilar Tibet Sun Fita Daga Talauci Bisa Manufofin Gwamnatin Kasar Sin

Al’ummar Kabilar Tibet Sun Fita Daga Talauci Bisa Manufofin Gwamnatin Kasar Sin

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version