Connect with us

Madubin Rayuwa

Manyan Ayyukan Ci Gaban Da Masari Ya Kawo: Katsina Za Ta koma Kan Matsayinta

Published

on

Z

abin taken, ‘Mayar Da Jihar Katsina Kan Matsayinta” a matsayin taken kamfen din Mai Girma Honorabul Aminu Bello Masari, wanda yake dan takarar neman kujerar gwamna ne na Jam’iyyar APC  a wancan lokacin, da nufi ne aka yi shi. Zabi ne da aka yi bisa lura da kuncin yanayin da tattalin arzikin Jihar yake a wancan lokacin. Wacce aka ce ita ce ta biyu a bayan karshe na Jihohin da tattalin arzikin su ya lalace, kuma Jiha ta uku a ci baya wajen ilimi, wanda duk hakan ya faru ne sabo da irin mummunan mulkin da Jihar ta ga mu da shi, wacce a can baya ta kasance jagaba a fannin ilimin da Noma. Jihar Katsina gida ce ga makarantar gaba da Firamare a duk Arewacin kasarnan, wacce kuma a wancan lokacin take jagorantar noman Auduga, Gyada da kuma hatsin da ake nomawa a kasarnan.

Kasantuwan yana daga cikin ma’aikatan da suka bauta wa Jihar kafin ya fada siyasa a shekarar 1992, inda aka nada shi Kwamishina a ma’aikatar Ayyuka, Gidaje da Zirga-Zirga, Gwamna Masari, bai kwana da sanin irin kalubalen da ke fuskantarsa ba na kokarin da ya sanya a gaba na farfado da Jihar da dawo wa da ita kan matsayin ta na baya can a tsakankanin sa’o’inta. Amma kasantuwar zaga Jihar da ya yi akalla sau biyar kafin babban zaben na 2015, sai irin dimbin aikin da ke fuskantan na shi ya kara bayyana a gare shi, wanda lamari ne mai tsoratarwa. Amma duk da hakan ya kasance mai cike da azaman dawo da Jihar zuwa matsayinta na kasancewa a gaba ga sauran sa’o’inta na kasarnan, inda yake amfani da maganan nan na shi ta cewa, “Matsala tana tabbata ne kadai, in ba a sa ka kudurin kawar da ita ba,”

A wajensa, hatta rashin isassun kudi, ba za su zama uzuri ba na rashin iya tabuka komai, domin a na shi fahimtar, lamarin ba na yawan kudin da kake da su ne ba, a’a, hanyar da ka bi ne wajen kashe abin da ke hannun naka kawai. Da wannan gaskiyan fahimtar na shi ne ya sami azamar jan ragamar Jihar ta Katsina tun daga ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2015 cikin nasara, inda yake amfani da dan abin da ke hannun shi wajen kyautata rayuwar al’umman Jihar bakidayansu ba tare da wata gajiyawa ba. Kamar yadda ya sha fadi ne cewa, “Bai yiwuwa ka saka siyasa kan lamarin Ilimi, Lafiya da Tsaro ko Noma.”

 

ILIMI:

A fili yake cewa, ba wata al’umma da za ta daukaka sama da matakin ilimin mutananta. Wannan shi ya sanya gwamnatin ta Masari har gobe take sanya ilimi a mataki na daya, na biyu da na uku a cikin gwamnatin na shi, wanda hakan ne ya sanya a cikin shekarun nan uku, sashen na ilimi ya lamushe akalla kashi 22 na duk kudaden kasafin kudinta na shekara. Irin kokarin da gwamnatin ta Masari ta kawo a sashen na ilimi, musamman a makarantun Firamare da Sakandare, wanda ya kai ga habakan na su ba ya misaltuwa.

Wadannan sanya bakin da gwamnatin ta Masari ta yi a sashen na ilimi bai takaitu a samar da gine-gine ba kadai, ya hada har da horas da su kansu malaman ingantaccen ilimi da kuma kara daukan wasu kwararrun malaman, kyautata masu, yi masu karin girma da kuma biyan su albashin su da sauran hakkokinsu a kan lokaci.

A baya, muna da azuzuwan karatu ne da aka gina su domin daukan dalibai 50, amma sai ya kasance ana cusa masu dalibai har sama da 150, a makarantun Firamare da kuma na Sakandare, nan da nan gwamnatin Masari ta dukufa wajen gyarawa da kuma gina sabbin ajujuwan ta yanda har aka kai ga samar da sabbin ajujuwa 752, aka kuma gyara sama da guda 1,598, a duk fadin Jihar. Aka kuma samar da ababen zama da na karatu sama da guda 10,000, da suka hada da kujeru da tebura masu dauke da mazaune biyu duk an samar da su kuma tuni an rarraba su.

Hakan ya sanya masu mallakan makarantu masu zaman kansu na kuka da cewa ana kwashe masu dalibai, domin kuwa a yanzun iyaye sun gwammace su kai ‘ya’yansu makarantun Firamare da Sakandare na gwamnati da suke a garuruwan Katsina da Daura. Hakanan yadda aka samar da dakunan gwaje-gwaje na kimiyya da fasaha daidai da zamani da dakunan karatu na zamani, gami da yadda aka adamta ajujuwan da Kwamfutoci, wadanda ba za ka taba samun kwatankwacin su a dukkanin makarantu masu zaman kansu ba a Jihar.

A jimlace, gwamnatin ta Masari, ya zuwa yanzun ta gyara gami da gina sabbin makarantun Firamare 160 da kuma na Sakandare 25, da suka hada da gina ajujuwa da dakunan kwana a makarantun Sakandare na kwana a kowane daga cikin mazabun dan Majalisar Dattawa uku na Jihar.

Gwamnatin ta yi karin girma tare da biyan kudaden ariya na sama da Malaman Firamare da Sakandare 1100 a Jihar, wasu daga cikinsu sun shafe sama da shekaru 10 ba tare da samun karin girman ba.

Dukkanin Makarantun mata a yanzun sun zama na kwana.

Tare da malamai sama da 2000 da ake da su a makarantun na Firamare da Sakandare, a yanzun haka muna shirin kara daukan wasu 5000 ne sabbi a karkashin shirin S Power.

 

LAFIYA:

Gwamnatin ta dukufa wajen aikin gyarawa, farfadowa da sake fasali da kashi 70 na Manyan asibitocin Katsina, Daura,  Funtua, Malumfashi, Musawa da Kankiya. Wadanda duk aka adamta su da kayan aiki na zamani da za su iya gogayya da na ko’ina a cikin kasarnan.

Kamar hakan dai yana gudana na gyara, fadadawa a asibitocin Dutsinma da Mani. Hakanan kuma abin da ke gudana kenan a dukkanin kananan asibitocin sauran Kananan Hukumomin Jihar tamu.

Ya zuwa yanzun, mun dauki ma’aikatan lafiya 690, da suka hada da Likitoci 110 (cikin su akwai kwararru 15), ma’aikatan jinya 250 da kuma Anguwar zoma 330 da sauran wasu ma’aikatan lafiyan, tare da wasu 500 da a yanzun haka ake kokarin daukan na su.

Gwamnatin Masari, ta samar wa Makarantan koyon aikin Nas ta Katsina tabbaci, hakan a karo na farko tun daga shekarar 1956, ta kuma nunka yawan daliban da take dauka daga 50 zuwa 120.

Babban al’amari ma shi ne hobbasan da gwamnatin ta yi a fannin na lafiya na kafa cibiyar koyarwa ta Jihar a Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’aduwa, da ke Katsina. Aikin ya yi nisa za kuma a kammala shi ne nan da shekaru uku.

 

TSARO:

Gwamna Masari ya dauki mataki sosai kan barazanar tsaro, da ke aukuwa da sunan satan Shanu, Kashe-kashe, satan mutane da kuma Fyade, wadanda suka shafi sha’anin noma da sauran sha’anonin kasuwanci sosai musamman a kananan hukumomi takwas na Jihar.

Lamarin lalacewar tsaron ya kai, a wata rana cikin watan Maris 2014, duk da cewa Shugaban kasa a wancan lokacin Goodluck Jonathan tare da manyan jami’an Jam’iyyar da ke mulki ta PDP su na garin, ‘yan ta’adda suka kashe mutane 142 a wani gari da ke tsakanin Faskari da Karamar Hukumar Sabuwa cikin wani harin da suka kwashe sama da awanni biyar su na aikata barna ba tare da an taka ma su birki ba.

Da hawansa mulki, Gwamna Masari, ya kaddamar da jami’an tsaro na hadin gwiwa na Jihohi bakwai da ke Arewa maso gabas, da suka hada da, Katsina, Kano, Kaduna, Jigawa, Zamfara, Sakkwato da Jihar Kebbi, har ma da Jihar Neja.

Ya kuma samar da shirin yin afuwa ga barayin shanun da suka tuba, wadanda suka sallama bindigoginsu ga gwamnati a wani buki na musamman da aka shirya kan hakan, wanda manyan jami’an Soji da na ‘Yan sanda suka halarta, a sakamakon karban tuban na su, za a sake karban su cikin al’umma, za kuma a samar masu da kayan more rayuwa kamar makarantu da asibitoci a wuraren da suke zaune. Ya zuwa yanzun an gina masu asibitoci guda tara da kuma makarantu tara wadanda duk ana gab da kammala su a wuraren da gwamnan ya alkawarta.

Tare kuma da hadin gwiwa da kamfanin sadarwa na MTN, ya samar da na’urar gane shanaye, da kuma wasu matsalolin na shanaye, (an shiya na’urar ne ta yadda za a iya gano shanayen da aka sace), a Runka ta Karamar Hukumar Safana, a ranar Asabar 2 ga watan Disamba 2017.

 

NOMA:

Bisa irin yadda Gwamna Masari ya mahimmantar da aikin noma, Mataimakinsa, Alhaji Mannir Yakubu ne ya danka ma alhakin lura da sashen na noma a matsayin Kwamishinan ma’aikatar ta noma, wanda Dakta Abba Abdullahi ke taimaka masa, wanda kwararre ne wanda duniya ke ji da shi a bangaren na noma. Jihar Katsina tana cikin shirin nan na babban Bankin kasarnan na samar da Auduga da Shinkafa, Jihar tamu ta Katsina ce ta zo ta daya a noman Auduga ta kuma zo na biyu a noman Shinkafa, inda Jihar Kebbi ne kawai ta sha gabanta a matsayin ta farko a noman na Shinkafa.

Noma a Jihar ta Katsina ya sami babban tallafi, ta yanda ake raba wa manoman Jiha ingantaccen takin zamani a kan lokaci ga manoman rani da na damina ba tare da sai an tsaya yin wani bikin na musamman ba wajen raba takin zamanin.

An samar da Taraktocin Noma, wadanda a yanzun ake hada su a Jihar tamu, an samar da su har an rarraba su ga manoman Jihar ta hanyar wani bashi mai saukin gaske da gwamnati ta ba su.

Gwamnatin ta Masari, ta kammala dukkanin shirye-shirye a tsakaninta da kamfanin Taraktoci na Indiya mai suna, ‘Mahindra Machines,’ domin ya zo Jihar ya rika hada Taraktocin da kuma sauran kayan aikin gonan na shi a kamfanin karafa na Kankiya da aka farfado da shi a kwannan nan.

An kuma kafa tsangayar aikin noma a Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’aduwa, domin kara cincida fannin na noma a Jihar tamu.

 

RUWAN SHA:

A wani mataki da ba a taba daukansa ba a baya, an farfado tare da kara daukaka darajar Dam din Ajiwa, domin amfanin garin Katsina da makwabtansa, shi ma Dam din Malumfashi an farfado da shi domin amfanin garin na Malumfashi da makwabtansa, da kuma Dam din Mairuwa domin amfanin garin Funtuwa da makwabtansa, kamar yadda aka farfado da na Daura, wanda duk gwamnatin ta Masari ce take gudanar da ayyukan na su, inda matsayin aikin wasun su ma ya kai kashi 80.

Hakanan tare da hadin gwiwar gwamnatin tarayya, gwamnatin ta Masari ta dukufa wajen kammala aikin ruwa na Dam din Zobe na garin Dutsinma, wanda a baya aka yi watsi da shi, da Dam din Sabke na Daura da Dam din Jibiya na garin Jibiya.

An kuma farfado da madatsun ruwa masu yawa, ana kuma kan aikin wasu masu yawa a dukkanin mazabun ‘yan majalisar dattawa uku, domin noman rani da kuma na shan dabbobi.

 

MASANA’ANTU:

An shirya taron masana tattalin arziki da zuba jari wanda ya sami halartar manyan masana daga Nijeriya da kasashen waje, da manyan ‘yan kasuwa da kamfanoni har ma da rukunin kamfanonin Dangote da na BUA, da kuma wasu da suka zo daga kasashen China, Indiya, Amerika, Dubai da Ingila.

Gwamnatin Masari, ta kyautata yanayi ga dukkanin masu son zuba jari da kuma yin kasuwanci a Jihar Katsina.

Gwamna Masari, ya farfado da wasu masana’antu da ba sa aikin komai tun a shekarar 1979 da gwamnatin Balarabe Musa ta kafa su. Sun hada da, Kamfanin karafa na Kankiya, Da na Kaolin na Kankara, da na konannen bulo na Funtuwa da na fata na Daura da sauran su.

‘Yan kasuwan China tuni sun kafa shagunan su a Jihar Katsina, Kamfanin Dangwate ma ya sayi makeken fili da zai noma tumatir da sauran kayan gona, gami da kamfanin da zai sarrafa su.

Su ma kamfanin BUA sun bukaci gwamnatin Jiha da ta sama masu filin da za su kafa kamfanin yin tufafi da sauran su.

 

HANYOYI DA LANTARKI:

Gwamnatin ta Masari ta kammala dukkanin ayyukan hanyoyin da ba a gama ba, wadanda ta gada daga tsohuwar gwamnatin da ta gabata, yawancin su wadanda aka bayar da ayyukan su ne cikin gaggawa gab da faduwan gwamnatin na su a watan Mayu na 2015.

Ya zuwa yanzun, gwamnatin ta Masari ta gina hanyoyi masu tsawon sama da Kilomita 250, a dukkanin mazabun Sanatoci uku, ba ya ga wasu kilomita 500 na hanyoyin karkara wanda gwamnatin ta bayar a kananan hukumomi 34 na Jihar.

Sama da Naira bilyan 2.5 aka kashe wajen gina hanyoyin ruwa a garuruwa da yawa na Jihar, kamar su, Katsina, Daura, Funtua, Malumfashi, Dutsinma, Kankiya, Danja, Dandume da Jibiya.

Ana kan aikin gyaran tashar mota da kasuwar Funtuwa, tare da daukaka matsayin su.

An sayo daruruwan injunan raba wutar lantarki domin amfanin karkarun Jihar a dukkanin kananan hukumomin Jihar 34.

Yanzun haka, ana kan aikin ginin wasu rukunnin gidaje uku ne da suka kunshi gidaje 450, aikin na su ya yi nisa wasu ma na gab da kammalawa.

 

SAMAR DA AYYUKAN YI:

Sama da matasan Jihar nan 10000 ne suke cin gajiyar wasu shirye-shirye bakwai na koyar da sana’o’i, daban-daban, inda mata suka sami kashi 60 maza kuma ke da kashi 40.

Cibiyoyin da ke gudanar da wadannan ayyukan sun hada da, Katsina State Economic Empowerment Directorate (KASEED), Youth Craft Billage, Women Affairs Ministry, Department of Girl Child Education da Youth And Women Empowerment.

A karshe, Gwamna Masari ba irin jabun ‘yan siyasan nan ne ba, wadanda zantukan su ba a bakin komai suke ba. Mai Girma Gwamna Aminu Bello Masari, dan siyasa ne wanda ke gwama fada da cikawa, ba tare da nu na bambancin siyasa ba.

Bai yarda da yin aiki domin riya ba, ko kuma wai domin fuskantar zabe na gaba, babban damuwarsa shi ne yin abin da ya kasance daidai ga jikokinmu, wannan shi ne ya ba shi daman daukan abin da wasu ba su mahimmantar da shi ba, matukar dai ya tabbatar da yin hakan shi ne ra’ayin al’umma.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: