Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa, burin Gwamnatin Tarayya na fitar da ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga kangin talauci za a cimma su ne ta hanyar dabaru da hankali.
A cewar wata sanarwa dauke da sa hannun mai magana da yawunsa Laolu Akande, Mataimakin Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin da yake jagorantar taron farko na kwamitin gudanarwa na rage talauci tare da dabarun habaka.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2019 yayi alkawarin fitar da ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga talauci cikin shekaru 10.
A ranar 12 ga watan Yuni, shugaban ya ce, gwamnatinsa ta fitar da ‘yan Nijeriya miliyan 10.5 daga kangin talauci a cikin shekaru biyu, duk da kara tabarbarewar alkaluman rashin aikin yi da hauhawar farashin kayan abinci.
Yadda gwamnatin Buhari ke shirin fitar da ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga kangin talauci a cikin shekaru goma ba zai ta’allaka da kasuwanci kamar yadda aka saba ba, amma wata dabara ce mai sauki, wacce za ta iya samar da sakamako kamar yadda Shugaban ya yi alkawari, a cewar Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo.
Da yake bayyana kyakkyawar fatan cewa ta wannan hanyar, Kwamitin zai iya samun ci gaba cikin sauri, Farfesa Osinbajo ya ce, “domin kar a yi wannan kawai, wani daga cikin wadannan kwamitocin masu kishin-kishin din da ba su cimma komai ba, dole ne mu kasance da niyya sosai na manufofinmu da yadda za mu cimma su.”
Farfesa Osinbajo ya bayyana hakan ne a Abuja cikin makon da ya gabata a taron Rage Talauci na Kasa tare da Kwamitin dabarun bunkasa tattalin arziki wanda aka gudanar a fadar shugaban kasa.
Da yake jawabi ga mambobin kwamitin, Farfesa Osinbajo ya ce, gwamnati za ta yi amfani da wata hanya daban kuma mafi inganci wajen aiwatar da manufar kawar da talauci a kasar domin samar da sakamako.
A cewarsa, “Ina matukar son mu tunkari wannan kamar yadda ya kamata, bisa la’akari, ta yadda za mu iya magance dukkan matsalolin tare da mai da hankali kan hakikanin ci gaban.”
“Ina so mu duba fiye da duk abin da za mu yi, za a samu aiki mai yawa na takarda, amma yawancin hankali shi ne ke bunkasa tattalin arziki. Abin da sauran kasashe suka yi, ba da gaske ba ne don sake inganta kafafun. Don haka, ina so mu mayar da hankali kan wadancan abubuwan na hadin gwiwa, don mu sami ci gaba a zahiri.”
Da yake ba da misali da Bangladesh inda aka aiwatar da dabarun rage talauci, Mataimakin shugaban kasar ya lura da yadda bangaren masana’antun kasar ke da muhimmanci.
“A zahiri Bangladesh na fitar da tufafi fiye da yadda muke fitar da mai,” in ji shi.
A cewarsa, “Kasashen da suka yi nasarar fita daga kangin talauci sun samar da ayyuka da dama ta hanyar masana’antu, kuma sun kirkiro dabaru da niyya.
“Dole ne mu kalli abin da wasu suka yi, wayayyun abubuwan da wasu mutane suka yi, da kuma daukarsu.”
Ya kuma yi magana game da harkar noma, inda ya ce, “lallai ne mu yi tunani mai kyau game da yadda muke tallafawa harkar noma.”
“Ina ganin da gaske muna bukatar yin zurfin tunani saboda gwamnatoci sun yi iya kokarinsu a kan magance talauci amma gaba daya magana suke, ba su bayar da irin sakamakon da ya kamata su bayar ba, kuma ina ganin saboda ana mai da hankali sosai kan takardu da aikin takarda da hanyoyin tattaunawa ne kadai,” in ji Mataimakin shugaban kasa.
Farfesa Osinbajo ya bayyana cewa, rage talauci na kasa tare da dabarun ci gaba yana nufin ya kasance dabarun kasa ne, ba kawai kokarin tarayya ba kuma yana da nufin fitar da mutane miliyan 100, na kasa baki daya daga kangin talauci a cikin wa’adin shekaru 10.
A kalaman nasa ya ce, “ina so in nanata cewa wata dabara ce ta kasa sabanin tsarin tarayya wanda hakan ne ya sa kwamitin gudanarwa ya hada da na tarayya da kuma na jihohi.”
Yayin da yake kuma jaddada rawar da kamfanoni masu zaman kansu ke takawa, Mataimakin shugaban kasar ya ce, “a zahiri, wannan kokarin dole ne a kuma yi shi kan yadda za a saukaka samar da ayyukan yi ga kamfanoni masu zaman kansu. Gaskiyar ita ce, babu yadda za a yi Gwamnatin Tarayya ko Gwamnatin Jiha su iya kirkirar yawan ayyukan da muke bukata.”
“Ya kamata mu dan yi takaitaccen bayani kan abubuwan da ke kunshe a halin da muke ciki a yanzu ta fuskar rasa ayyukan yi da,” in ji shi.
Yayin da yake ci gaba, Farfesa Osinbajo ya ce, za a yi kokarin mayar da hankali kan samar da dama ga ‘yan Nijeriya don su samu abin dogaro da kai tare da wadata su da sana’o’in da ake bukata.
A taron na yau, mambobin da suka halarci taron sun hada da Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti, wanda kuma shi ne Shugaban kungiyar gwamnonin Nijeriya, Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno da Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha; Ministoci kamar na aikin gona, Muhammad Nanono; Masana’antu, Kasuwanci da zuba jari, Niyi Adebayo, da kwadago da samar da aikin yi, Dakta Chris Ngige suma duk sun halarci taron, yayin da karamin Ministan kasafin Kudi da tsare-tsaren kasa, Prince Clem Agba ya halarci taron shi ma.
Daga baya a karshen taron, kuma yayin gabatar da tambayoyi daga ‘yan jarida, Gwamna Sule na Jihar Nasarawa ya ce, “duk abin da ke cikin kwamitin shi ne gwamnati ta samu damar fitar da ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga kangin talauci a cikin shekaru 10 masu zuwa.”
Ya ce, bayan da aka sake nazarin Sharuddan magana (TOR), Kwamitin Gudanarwa na yanzu yana kafa kungiyar masu fasaha da kungiyar kare lafiyar jama’a ta kasa sannan kuma ta ci gaba da taronta bayan hutun Sallah.