Connect with us

RAHOTANNI

Manyan Jami’an Gwamnatin Kasar Sin Sun Maida Martani Kan Takaddamar Cinikayyar Kasarsu Da Amurka

Published

on

Tun farkon bana, kasar Amurka ta kaddamar da takaddamar cinikayya a tsakaninta da kasar Sin, al’amarin da ya jawo hankalin duk fadin duniya. A ranar 24 ga watan Satumba, gwamnatin kasar Sin ta bullo da wata takardar bayani game da shaidu da matsayinta kan takaddamar cinikayya dake tsakaninta da kasar Amurka, inda ta yi bayani filla-filla kan hadin-gwiwar Sin da Amurka ta fannin tattalin arziki da cinikayya dake kawowa juna moriya, da nufin daidaita wannan takaddama ta hanyar da ta dace.

Wasu masu sharhi na kasar Amurka sun bayyana cewa, wai ana samun gibin kudaden cinikayyar kayayyaki tsakanin Amurka da Sin, a sakamakon takara mai cike da rashin adalci da kasar Sin ke haifarwa, kuma kasar Amurka ta samu hasarori a sakamakon hakan.

Game da wannan batu, a wajen taron manema labaran da ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya a ranar 25 ga watan Satumba, wakilin maaikatar kasuwancin Sin mai kula da shawarwari kan ciniki a tsakanin kasa da kasa, kuma mataimakin ministan kasuwancin kasar Fu Ziying ya bayyana cewa, wadannan zarge zarge ba su da tushe balle makama.

Fu Ziying ya kara da cewa, bambancin yawan cinikin dake tsakanin Sin da Amurka ya shafi yawan cinikin da suka gudanar, kuma ba ya nufin samun riba ko hasara. Sin da Amurka, suna da bambancin matsayi a fannin samar da kayayyaki a duniya, yayin da Amurka take a matsayi na gaba, Sin ta zama a matsayin baya. Sai dai kamfanonin Sin sun samu kudi daga kere-kere, amma Amurka na samun kudi masu yawa a fannonin tsara salon kayyayaki, da samar da sassan inji, da kuma aikin sayarwa.

Har ila yau samun rashin daidaito kan cinikin dake tsakanin Sin da Amurka, yana da nasaba da kayyade fitar da kayyayaki da Amurka ta yiwa Sin. Hukumomin da abin ya shafa na kasar Amurka sun kiyasta cewa, idan aka sassauta kayyade fitar da kayyayakin zamani masu amfani ga jama’a, yawan gibin kudin da Amurka ke samu daga Sin zai ragu da kashi 35 bisa dari.

Fu Ziying ya kuma nuna cewa, Sin tana son yin kokari wajen kara sa kaimi ga yin ciniki tsakanin bangarorin biyu cikin daidaito, kana tana fatan Amurka za ta amsa kiran Sin a wannan fanni.

Shi ma a nasa bangaren, mataimakin ministan kasuwancin kasar Sin, kuma mataimakin wakilin maaikatar kasuwancin Sin mai kula da shawarwari kan ciniki a tsakanin kasa da kasa Wang Shouwen, ya bayyana cewa, lokacin sake yin shawarwari kan tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Amurka, yana da nasaba da matsayin da Amurka take dauka.

Wang Shouwen ya ce, yanzu Amurka ta dauki matakan kayyade ciniki tsakaninta da Sin, hakan ya haddasa rashin daidaito a shawarwarin. Kana an riga an yi shawarwari a tsakanin manyan jamian Sin da Amurka har zagaye hudu, inda aka cimma raayi bai daya a fannoni da dama, har ma bangarorin biyu sun fitar da hadaddiyar sanarwa, amma Amurka ta sabawa alkawuranta, inda ta dauki matakan kayyade ciniki dake tsakaninsu, don haka ba za a iya ci gaba da shawarwarin ba.

Har wa yau, a nasa bangaren, mataimakin direktan kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na Sin Lian Weiliang ya bayyana yau, cewar Amurka ta kara yawan haraji kan kayayyakin Sin da darajarsu ta kai dala biliyan 200, hakan zai kawo illa ga ci gaban tattalin arzikin Sin. Ko da ba a iya magance hakan ba, amma shi ba babbar matsala ba ce ga Sin. Sin na da karfin tinkarar matsalar ta hanyar fadada bukatun cikin gida da kyautata ingancin bunkasuwarta. (Masu Fassarawa: Zainab Zhang, Murtala Zhang, ma’aikatan sashin Hausa na CRI)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: