Connect with us

KASUWANCI

Manyan Jami’an Kwastom 304 Za Su Yi Ritaya

Published

on

Hukumar yaki da fasa kwauri ta kasa (Kwastom) ta kammala shirye-shiryen yi wa wasu manyan jami’anta guda 304 ritaya sakamakon sun kai shekara 60 da haihuwa.

Rahotanni sun bayyana wasu daga cikin jami’an kuma wasu sun cika shekaru 35 su na aiki ne, wanda hakan shi ma ya na cikin tanadi na yin ritaya a cikin dokokin aikin gwamnati tarayya.

Hukumar ta sanar da wadannan jami’ai shirin ajiye aiki zuwa farkon shekarar 2020.

Daga cikin wadanda ritayar za ta shafa akwai kwanturola guda 102 da su ka hada da mataimakan manyan kwanturola (DCG) guda biyu, mataimakan manyan kwanturola na biyu (ACG) guda uku, kwanturola 13, mataimakan kwanturola 39 da mataimakan kwanturola na biyu guda 45.

Mataimakan manyan kwanturola (DCG) guda biyu su ne, A.A. Dangaladima da ke kula da sashen kudi da mulki da kuma Sanusi Umar da ke kula da sashen dauka da kula da ma’aikata.

Mataimakan manyan kwanturola na biyu (ACG) guda uku su ne, jami’I mai kula da shiyya ta C, Frances Enwereuzor; mataimakin mai kula da sashen kudi da mulki, Bukar Amajam, da jami’i mai kula da shiyyar B, Chris Odibu.

Sauran jami’ai masu mukaman kwanturola da za su yi ritayar su ne, Bictor Dimka; Florence Didon; Yusuf Bashar; Francis Adetoye; Gwani M. J; Ogwude L. N; Edede I. E; Abdulahi I. A; Zulkifu A. A; Garba K. U; Loko Y; Angbalaga J. J da Adediran.

A matakin mataimakan kwanturola kuwa akwai Agbo A. H; Abdulrahman T; Salihu M. S; Abubakar M. D; Bello A. N; Chima D. N; Muhammed M; Aliyu D. G; Idris K. I; Namanu A; Zakari N; Ibume R. K; Oyafemi C. I; Waziri S. A; Abioye; T. O; Idris A. I; Muhammed A. B; Ebieme A. U; Adamu S. A; Yusuf S; Adie B. U; Dauda A. Okoloagu D. I; Eneh O. O da Mamu B. Sauran sun hada da Odwong B. R; Lot-Eburajolo J. E.; Thlama P. W; Umar A; Mustapha I. A; Umoh P. M; Bewaji I. O; Muhammed S. D; Maude A. M; Idris Danladi A. L; Omonoyan O. O; Malah D. A; Tanko S. M da Orekie M.C.

Da ya ke tsokaci game da sunayen, kaakakin hukumar kwastam, Joseph Attah ya bayyana cewa wannan ba wani sabon abu ba ne, domin da ma hukumar ta saba shirya jami’anta da za su yi ritaya tare da sanar da su kafin lokaci ya yi, kuma su kan tafi hutun wata uku kafin cikar wa’adinsu.
Advertisement

labarai