Manyan Jami’an Tsaron Faransa Na Fuskantar Zargin Rashawa

Masu bincike a ma’aikatar shari’a ta Faransa na zargin wasu jami’an ma’aikatar tsaron ƙasar da laifin rashawa wajen bayar da hanyar jiragen saman dakon jiragen yaƙinta zuwa waje.

Tuni masu bincike suka kai samame a sashen da ke kula da ajiyar kayayyaƙi na ma’aikatar tsaron da ke Ɓillacoublay kusa da birnin Paris, inda suka gudanar da bincike.

Jaridar Le Monde da ake bugawa a ƙasar ta ruwaito cewa ma’aikatar tsaron na bayar da hayar jiragen a kan kuɗaɗen da suka kama daga Euro milyan 50 zuwa milyan 60 kowace shekara a daidai lokacin da sojojin ƙasar ke fama da rashin jiragen da za su yi jigilarsu.

Exit mobile version