Manyan Kungiyoyin Firimiya Suna Zawarcin Harry Kane

Daga Abba Ibrahim Wada

Kungiyoyin Manchester City, da Manchester United da kuma Chelsea sun tuntubi wakilan tauraron dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, Harry Kane kan neman kulla yarjejeniya da shi, bayan da dan wasan ya shaidawa kungiyar tasa aniyarsa ta sauyin sheka a karshen kakar wasa ta bana.

Yayin ganawar da yayi da manema labarai a baya bayan nan, dan wasa Harry Kane kuma kaftin din tawagar ‘yan wasan kasar Ingila mai shekaru 27 a duniya ya ce babban burinsa a yanzu shi ne neman lashe kofuna.

Bayanai sun ce tun a shekarar bara Kane ya so rabuwa da Tottenham, amma shugabannin kungiyar suka rarrashe shi ya kara lokaci, bayan da suka maye gurbin tsohon kocinsu Mauricio Pochettinho da Jose Mourinho, wanda shi ma suka sallama a watan jiya.

Tuni dai kungiyoyi a Ingila suka fara nuna sha’awarsu ta daukar dan wasan wanda ake saran kudinsa zai kai sama da fam miliyan 100 a kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa ta bana da za’a bude nan gaba kadan.

Exit mobile version