Connect with us

MANYAN LABARAI

Manyan Mukamai 86 A Arewa: Rijiya Ta Bada Ruwa Guga Ta Hana?

Published

on

Daga dukkan alamu yanzu haka Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya shiga tsaka mai wuya, saboda ganin yadda al’ummar Kudancin Nijeriya ke gunaguni tare da zargin Shugaban kasa ya fi fifita Arewacin kasar, a lokaci guda kuma ‘yan Arewa na ganin bai tsinana mu su komai ba, inda su ke yi ma sa gori tare yi ma sa bita-da-kulli da cewar, su ne kan gaba wajen ba shi kuri’a, kuma su na zargin sa da gaza yin komai kan tabarbarewar tsaro a yankin. Sai dai kuma dukkanin mukamai na tsaro ya na hannun ‘yan Arewa.

Yawancin ’yan Arewacin Nijeriya su na dora laifin kacokan a kan Shugaba Buhari, duk da cewa, idan a ka duba, hatta kudaden tafiyar da harkokin tsaron, ’yan Arewa ke tsarawa kuma a mika mu su a hannunsu.
To idan kuwa haka ne, kaka-tsara-kaka! Ya kamata ‘yan Arewa su jinjina wa Buhari ganin yawan manyan mukamai da ya bai wa ‘yan Arewa, duk da cewa, amma kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.
Manyan mukamai sama da 86 masu muhimmanci Shugaba Buhari ya bai wa ‘yan arewa. Ya kamata ‘yan Arewa su yi alkalanci tare da yi wa shugaban adalci duba mukaman da ya bai wa ‘yan Arewa ba tare da sun iya taimaka ma sa ba wajen kawo karshen matsalolin yankin.
Ga dai jaddawalin mukamai 86, wadanda Shugaba Buhari ya gwangwaje ‘yan Arewacin Najeriya da su:
1. Mai Bawa Shugaban kasa Shawara kan Tsaron kasa- Babagana Manguno – Jihar Borno
2. Mai Bawa Shugaban Shawara Kan Kafafan Yada Labarai- Garba Shehu – Jihar Kano
3. Chief Protocol- Lawal Kazaure – Jihar Jigawa
4. Shugaban Sojojin kasan Najeriya- Yusif Tukur Buratai – Jihar Borno
5. Shugaban ‘Yan Sandan Najeriya- Muhammadu Adamu – Jihar Nasarawa
6. Shugaban Kwastom- Hameed Ali – Jihar Bauchi
7. Shugaban Sojin Sama- Air Marshal Sadikue Abubakar – Jihar Bauchi
8. Shugaban Immigration- Muhammadu Babandede – Jihar Jigawa
9. Shugaban Fire Serbice- Liman A. Ibrahim – Jihar Niger
10. Shugaban Cibil Defence- Abdullahi Gana Muhammad – Jihar Niger
11. Shugaban DSS- Yusif Magaji Bichi – Jihar Kano
12. Prison Serbice- Ja’afaru Ahmed – Jihar Kebbi
13. Military Defence Intelligence- Air bice Marshal Mohammed Sani Usman – Jihar Kano
14. Nigeria Intelligence Agency (NIA)- Ahmed Rufai Abubakar – Jihar Katsina
15. Shugaban Kamfanin Mai Na Nijeriya (NNPC)- Malam Mele Kolo Kyari – Jihar Borno
16. Shugabar Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa (NPA)- Hadiza Bala Usman – Jihar Katsina
17. Ministan Abuja- Mohammed Musa Bello – Jihar Adamawa
18. Ministan Ilimi- Adamu Adamu – Jihar Bauchi
19. karamar Ministar Ma’aikata- Ambassador Maryam Katagum – Jihar Bauchi
20. Ministan Ayyukan Musamman- George Akume – Jihar Benuwe
21. karamin Ministan Gona- Mustapha Baba Shehuri – Jihar Borno
22. Minstan Sadarwa- Ali Isa Pantami – Jihar Gombe
23. Ministan Ruwa- Suleiman Adamu – Jihar Jigawa
24. Ministar Kudi- Zainab Ahmed – Jihar Kaduna
25. Ministan Muhalli- Muhammad Mahmood – Jihar Kaduna
26. Ministan Gona- Sabo Nanono – Jihar Kano
27. Ministan Tsaro- Bashir Salihi Magashi – Jihar Kano State
28. Ministan Sufurin Jiragen Sama- Hadi Sirika – Jihar Katsina
29. Ministan Shari’a- Abubakar Malami – Jihar Kebbi
30. karamar Ministar Abuja- Ramatu Tijjani – Jihar Kogi
31. Ministan Yada Labarai- Lai Mohammed – Jihar Kwara
32. karamar Ministar Sufuri- Gbemisola Saraki – Jihar Kwara
33. Ministan Kimiyya da Fasaha- Mohammed H. Abdullahi – Jihar Nasarawa
34. Ministan Cikin Gida- Zubair Dada – Jihar Neja
35. Ministar Mata- Paulen Tallen – Jihar Plateau
36. Ministan ’Yan Sanda – Maigari Dingyadi – Jihar Sokoto
37. Ministan Lantarki- Sale Mamman – Jihar Taraba
38. karamin Ministan Aiyyuka da Gidaje- Abubakar D. Aliyu – Jihar Yobe
39. Ministar Jinkai Da Walwala- Sadiya Umar Faruk – Jihar Zamfara
40. Shugaban PTDF- Dr Bello Aliyu Gusau – Jihar Zamfara
41. Shugabar Petroleum Ekualisation Fund (PEF) Hajiya Asabe Asamau Ahmed – Jihar Neja
42. Babban Sakataren TEDFUND- Suleiman Bogoro – Jihar Bauchi
43. Darakta Janar Na SMEDAN- Dr. 44.Dikko Umar Radda – Jihar Katsina
44. Darakta Janar Na FRCN- Mansur Liman – Jihar Katsina
45. Darakta Janar Na NHIS- Farfesa Usman Yusuf – Jihar Katsina
46. Manajan Darakta Na FERMA- Injiniya Nuradeen Rafindadi – Jihar Katsina
47. Manajan Darakta Na Federal Mortgage Bank of Nigeria- Arch Ahmad Dangiwa – Jihar Katsina
49. Manajan Darakta Na NIMET- Farfesa Sani Abubakar Mashi – Jihar Katsina
50. Babban Sakatare Na PPPRA- Abdulkadir Saidu Umar – Jihar Katsina
51. Shugaban Nigerian Railway Corporation (NRC) – Usman Abubakar Sandamu – JIhar Katsina
52. Likitan Shugaban kasa- Dr. Shu’aib Sanusi Rafindadi – Jihar Katsina
53. Hadimin Shugaban kasa- Sabi’u Yusuf (Tunde) – Jihar Katsina
54. Babban Jami’in Tsaron Fadar Shugaban kasa- Bashir Abubakar Bindawa – Jihar Katsina
55. Babban Jami’in ’Yan Sandan Fadar Shugaban kasa- Abdulkarim Dauda – Jihar Katsina
56. Jakadan Nijeriya a Iran- Ambasada Hamza Ibrahim Tsiga – Jihar Katsina
57. Jakadan Nijeriya a Saudiyya- Ambasada Justice Isa Dodo – Jihar Katsina
58. Jakadan Nijeriya a Chana- Ambasada Usman Aliyu Bakori – Jihar Katsina
59. Jakadan Nijeriya a Dubai- Ambasada Muhammadu Rimi Barade – Jihar Katsina
60. Mamban Kwamitin Manufofin Kudi Na CBN- Dr. Aliyu Sanusi Rafindadi – Jihar Katsina
61. Mamban Hukumar NIMASA- Alhaji Gambo Ahmad Mahuta – Jihar Katsina
62. Kotun Kula Da da’ar Ma’aikata- Barista Murtala Kankia – Jihar Katsina
63. Daraktan Gyare-gyare na Hukumar FAAN- Salisu Nura – Jihar Katsina
64. Kwamishinan Hukumar Kula Da Ma’aikatan Shari’a- Sanata Abba Ali – Jihar Katsina
65. Manajan Daraktan Hukumar Buga Kudin Nijeriya- Abbas Umar Masanawa – Jihar Katsina
66. Shugaban Hukumar Daidaiton daukar Ma’aikata- Dr. Bello Tukur Ingawa – Jihar Katsina
67. Shugaban Hukumar Tara Kudin Kula da ’Yan Sanda- Suleiman Abba – Jihar Jigawa
68. Babban Akanta Na kasa- Ahmed Idris – Jihar Kano
69. Shugaban NITDA- Kashifu Inuwa Abdullahi – Jihar Jigawa
70. Shugaban Hukumar Tara Kudin Shiga (FIRS)- Muhammad Mamman Nami – Jihar Neja
71. Shugaban Shippers Council- Hassan Bello – Jihar Kebbi
72. Shugaban Hukumar Bada Katin kasa (NIMC)- Malam Bello Ibrahim Gwandu – Jihar Sokoto
73. Shugaban Hukumar INEC- Farfesa Mahmood Yakubu – Jihar Bauchi
74. Darakta Janar na NEMA- AbM Muhammadu Alhaji Muhammad (rtd) – Jihar Borno
75. Darakta Janar na NOA- Garba Abari – Jihar Yobe
76. Babban Daraktab NYSC- Sule Kazaure – Jihar Jigawa
77. Shugaban NDLEA- Muhammed Mustapha Abdullah – Jihar Adamawa
78. Shugaban Hukumar NCC- Farfesa Umar Dambatta – Jihar Kano
79. Sakataren Gwamnatin Tarayya- Boss Mustapha – Jihar Adamawa
80. Shugaban Hukumar EFCC- Ibrahim Magu – Jihar Borno
81. Shugaban Hukumar Bada Ilimi Kyauta (UBEC)- Dikko Suleman – Jihar Katsina
82. Shugaban Hukumar Kula Da Jami’o’i (NUC)- Farfesa Shehu Galadanchi – Jihar Kano
83. Shugaban Hukumar NTI- Farfesa Garba Dahuwa – Jihar Bauchi
84. Mai Taimaka Wa Shugaban kasa Kan Kafafen Sadarwar Zamani- Bashir Ahmad – Jihar Kano
85. Shugaban Budaddiyar Jami’ar Nijeriya (NOUN)- Farfesa Abdalla Uba Adamu – Jihar Kano
86. Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban kasa- Farfesa Ibrahim Gambari – Jihar Kwara.
Duk da irin wannan tagomashi da Shugaban kasa Buhari ya yi a arewacin Najeriya, babu wani dalili da zai janwo a gaza wajen sanya ma sa albarka ko yi ma sa sambarka.
A zahirance, Shugaban kasa Buhari ya kyautata wa yankin Arewa, amma kullum su na kalubalantar sa, saboda rashin kyakkyawan wakilci a gwamnatinsa. Ya kamata kungiyar Dattawan Arewa ta tattara hankalinta wajen kiran ‘yan Arewa masu rike da manya mukamai, domin lalubo bakin zaren yankin maimakon mayar da hankali wajen kalubalantar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda shi ma ya fito daga Arewacin Najeriya din ne.
Kullum ‘yan Arewa su na kukan cewa, yankin Kudancin kasar su ne ke rike da madafun ikon kasar, amma zancen akwai gyara ko mu ce kuskure. Da a ce ‘yan Arewa da su ke rike da irin wadannan manyan mukamai a Gwamnatin Tarayya za su mayar da hankali wajen daidaita al’amurran da su ka shige duhu a arewacin Najeriya, da zancen ba haka ya ke ba a yanzu. Idan a na maganar rashin aiki a Arewa, laifin su waye? Wakilan Arewa a kunshin gwamnatin Buhari ya kamata su tsaya sosai da sosai wajen ganin sun gyara, amma ‘yan arewa na kokawa, saboda rashin daidaito a daukar ma’aikata.
Rashin tsaro ya yi kyamari, bayan duk wani fanni na tsaron Nijeriya su na karkashin kulawar ‘yan Arewa, amma sun ja bakinsu sun yi shiru a na kashe bayin Allah, alhali duk masu kula da hakkin tsaron Najeriya ‘yan Arewa ne. Ya kamata su yi duk mai yiwuwa wajen ganin an shawo kan lamari.
Shin don Allah tsakanin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da masu rike da madafun iko har mutane 86 da su ka fito daga shiyyar Arewacin Najeriya wa ke da laifi?

Tamat!
Advertisement

labarai