Daga Mahdi M. Muhammad,
Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya zargi wasu kusoshi manyan mutane da kasancewa masu ingiza kiraye-kirayen raba Nijeriya.
A cewar dan majalisar, ‘yan kasa nagari ba su da ra’ayi iri daya da wadannan manyan mutanen, kamar yadda suka yi amannar cewa kasar ta ci gaba da kasancewa a matsayin daya babu rabewa.
Lawan ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Asabar, 3 ga Afrilu, a garin sa na jihar Yobe.
Ya ce, “Manyan mutane su ne matsalar. Kuma koda sun ce a’a, dole ne mu yi tunani. Na yi imanin cewa ya kamata mu yi adalci ga dumbin ‘yan Nijeriya, wadanda da yawan su sun kasance talakawa ne.”
Shugaban majalisar dattijan ya ci gaba da cewa, mutane suna son a jagoranci su yadda ya kamata, kuma dole ne a yi hakan. Ya zama dole ga talakawa a ba su shugabanci na adalci.
Lawan wanda ya yi amannar cewa hadin kan Nijeriya ba abu ne da za a iya tattaunawa da shi ba, ya kara da cewa, kada mutane su yi sakaci lokacin da suka koka.
Jawabin shugaban majalisar dattijan ya sake bayyana ra’ayin fadar shugaban kasa kan rabawar. A wani rahoto a baya, fadar shugaban kasa ta mayar da martani ga masu neman raba kasar, tana mai cewa, babu wanda zai iya durkusar da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana masu neman rabawar a matsayin mayaudara wadanda suka dauki nauyin yi wa shugaban kasar zagon kasa da tunanin zai firgita. Kiran rabawar ya ta’azzara a makonnin da suka gabata. Wani sanannen mai rajin kare hakkin Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, a kwanan nan ya ayyana kasar Yarbawa mai cin gashin kanta, yana mai cewa yana da goyon bayan sarakuna a yankin.
Amma kuma, majalisar dattawan Yarbawa (YCE) ta hanzarta warware ikirarin, suna cewa, Sunday Igboho ba ya wakiltar Yarabawa.
Haka zalika, wani tsohon dan gwagwarmaya a yankin Neja Dalta, Mujahid Asari-Dokubo, kwanan nan ya bayyana kansa a matsayin shugaban sabuwar gwamnatin Biafra a zahiri a kudu maso gabas.