Connect with us

RAHOTANNI

Manyan ’Yan Siyasar Da Suka Fuskanci Shari’a A Gwamnatin Buhari

Published

on

A kokarin wannan gwamnatin na alwashin da ta sha kan yakar cin hanci da rasahawa da sauran laifukan da kan karya tattalin arzikin kasa, ta garkame gaggan ‘yan siyasa da dama a gidajen Yarin kasarnan daban-daban.

Gaggan ‘yan siyasan da suka hada da tsaffin gwamnoni, tsaffin Ministoci da Shugabannin Jam’iyyun Siyasa, duk an tilasta masu barin hamshakan fadojin su da ke mahimman wuraren kasannan domin su dandani zaman gidajen yarin dalilin aikata laifukan karya tattalin arzikin kasa a lokutan da suke kan mulki.

Daure manyan ‘yan siyasan a gidajen yari, ya kawo ma daurarrun wani haske ne a mafiya yawan lokuta, kamar yadda misalin hakan ya faru a gidan yarin Jos, inda kasantuwar tsohon gwamnan Jihar, Sanata Jonah Jang, ya sanya a dawo da lantarkin gidan yarin da ta jima a cikin duhu.

Yayin da wasunsu ke moran kasantuwa a dakunansu su kadai, wasun su ma kan kashe dare ne da iyalan su a dakunan na su na gidan Yarin. Misalin hakan, shi ne na tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, wanda ke zaune a gidan yarin Kurmawa tare da ‘ya’yansa biyu.

Baya ga ‘yan Majalisu, da yawan ‘yan siyasan da aka ajiye su a gidajen yarin duk ana tuhumar su ne da aikata laifukan karya tattalin arziki a lokuta daban-daban na gwamnatocin baya.

An zartar da hukunci kan shari’u biyu a karkashin wannan gwamnatin, duk da cewa tun da jimawa ne aka fara shari’un mutanan da lamarin ya shafa.

Baya ga wadanda ke garkame a gidajen yarin, akwai kuma wadansu da suka yi gudun hijira domin su kauce wa komar ta hukumomin jami’an binciken. Irin su sun hada da tsohon Shugaban Jam’iyyar ta PDP, Adamu Mu’azu, tsohuwar Ministan albarkatun man fetur, Diezani Alison-Madueke, da Jamila Tangaza, wata tsohuwar darakta.

 

 • Ramalan Yero, Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna

Mukhtar Ramalan Yero, tsohon gwamnan Jihar Kaduna, kwanan nan ne aka jefa shi gidan yarin Kaduna. Cikin shekaru biyar ne Yero ba tare da ya taba tsayawa wata takara ba, ya zama Kwamishina, Mataimakin Gwamna, daga bisani ma ya zama Gwamnan.

Yero, wanda ya faro daga mukamin daraktan kudi a wani kamfanin Namadi Sambo, (Nalado Nigeria Limited), har ya zama Kwamishinan kudi a shekarar 2007, Mataimakin gwamna a shekarar 2010, ya kuma zama Gwamna a shekarar 2012, sanadiyyar mutuwar Patrick Yakowa, a wani hatsarin Jirgin sama na Helikwafta, sai da ya kwashe mako guda a gidan yarin na Kaduna.

An tsare shi ne a gidan yarin a ranar 31 ga watan Mayu har zuwa ranar 6 ga watan Yuni 2018, tare da tsohon shugaban Jam’iyyar PDP a Jihar ta Kaduna, Abubakar Gaya-Haruna, da wani tsohon Sakataren gwamnatin Jihar, Hamza Ishak da tsohon Ministan lantarki, Nuhu Somo Way. Duk ana tuhumarsu ne da yin almundana wanda hukumar EFCC ke masu.

 

 • Jonah Jang, Tsohon Gwamnan Jihar Filato

Tsohon Gwamnan Jihar Filatau, Kwamandan Sojin Jiragen sama , Jonah Dabid Jang, ya kasance babban bako a gidan yarin Jos na tsawon kwanaki takwas.

Kasantuwar Sanata Jang, wanda ke wakiltar mazabar dan Majalisar Dattawa a Filatau ta Arewa,  a gidan yarin na Jos, hakan ya yi sanadiyyar dawo da hasken lantarkin gidan yarin.

Jang wanda ya taba zama gwamnan mulkin Soja Jihar Binuwe da tsohuwar Jihar Gongola da Filatau, a tsakankanin shekarar 2007 da 2015, yana fuskantar tuhumomi 12 ne na karkatar da Nara bilyan 6.3, tare da tsohon mai biyan kudi na ofishin sakataren gwamnatin Jihar, Yusuf Pam. Amma ya musanta zargin da ake yi masan.

 

 • Bala Ngilari, Tsohon Gwamnan Jihar Adamawa

Kasantuwar shari’ar ta tsohon gwamnan na Jihar Adamawa, Bala James Ngilari, ita ce ta farko da aka fara daurewa a wannan gwamnatin.

A watan Maris 2017, ne aka daure Ngilari, kan gazawar da ya yi na tsayuwa da dokokin Jihar. A hukuncin da ya yanke na tsawon mintuna 75, Mai Shari’a Nathan Musa, ya sami tsohon gwamnan da laifi a kan tuhumomi guda hudu, sa’ilin da ya wanke shi a kan tuhuma guda, da ta kunshi zargin hada baki da aikata laifi. Alkalin ya daure tsohon gwamnan na tsawon shekaru biyar a gidan yari.

 

 • Jolly Nyame, Tsohon Gwamnan Taraba

Bayan gwabza shari’a na tsawon sama da shekaru 10, an daure Rabaran Jolly Nyame, tsohon gwamnan Jihar Taraba har na tsawon shekaru 14, kan laifin almunbazantar da dukiyar gwamnati a lokacin mulkin na shi.

Mai shari’a Adebukola Banjoko, na babbar kotun birnin tarayya da ke Gudu, Abuja, ne ya aike da Nyame gidan yarin bisa samun sa da laifin cin amana ta hanyar barnatar da Naira bilyan 1.64, wanda hukumar EFCC ta tuhume shi da aikatawa.

An haife shi ne a shekarar 1955, ya zama gwamnan Jihar ta Taraba daga watan Janairu 1992 zuwa watan Nuwamba 1993. Ya sake zama gwamnan Jihar daga watan Mayu 1999 zuwa 20917. Hukumta shin da aka yi yana daya daga cikin nasarorin da hukumar ta EFCC ke tinkaho da shi.

 

 • Sanata Peter Nwaoboshi

Sama da awanni 48 ne Peter Nwaoboshi (PDP-Delta ta Arewa), ya kasance babban bako a gidan yarin Kirikiri, kan zargin yin sama da fadi da Naira milyan 805, wanda hukumar ta EFCC ta yi ma shi.

Nwaoboshi, wanda ke shugabantar kwamitin Majalisar kan hukumar ci gaban Neja Delta, (NNDC), an gurfanar da shi ne gami da wasu kamfanoni guda biyu, – Golden Touch Construction Project Ltd da Summing Electrical Ltd, bisa tuhumar su da aikata laifuka biyu na cuwa-cuwa da kuma juya kudade, a gaban mai shari’a Mohammed Idris. An baiwa Sanatan belin kanshi da kanshi ne bisa sanayya.

 

 • Lamido Da ’Ya’yansa Biyu

Jim kadan da zuwan wannan gwamnatin ne a watan Yuli 2015, aka garkame tsohon gwamnan Jihar Jigawa tare da ‘ya’yayensa biyu, Aminu da Mustapha, a gidan kurkukun Kurmawa, bisa tuhumarsu da laifin yin cuwa-cuwan sama da Naira bilyan 1.351.

An ce an yi cuwa-cuwan kudin ne ta hanyar wasu kamfanoni guda hudu duk mallakan Lamidon ne da ‘ya’yansa. Kamfanonin sune, Bamaina Holdings Limited, Bamaina Company Nigeria Limited, Bamaina Aluminum Limited da Speeds International Limited. An ce an baiwa Sule Lamidon daki guda ne tare da’ya’yan na shi. Lamido, yana daya daga cikin ‘yan siyasar na Jam’iyyar ta PDP da yake neman kujerar ta Buhari.

 

 • Olisah Metuh

Tsohon Kakakin Jam’iyyar ta PDP, Mista Oliseh Metuh, yana a gidan yarin na Kuje da ke Abuja, bisa tuhumar yin almundahanan kudade.

Hukumar ta EFCC tana tuhumarsa ne da karban Naira milyan 400 daga tsohon mai baiwa Shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Sambo Dasuki, wanda ake jin suna daga cikin dala bilyan 2.1, wanda aka tanada domin sayo makamai a lokacin tsohuwar gwamnatin da ta gabata. Har yanzun dai ana ci gaba da yin shari’ar duk da kasantuwar zuwan Metuh kotun a kan gadon asibitin.

 

 • Sanata Bala Mohammed Da Dansa

Tsohon Ministan na babban birnin tarayyan Sanata Bala Mohammed tare da dan na shi, Shamsuddeen, an garkame su ne a kurkukun na Kuje a lokuta daban-daban bisa tuhumar yin wala-walar kudade.

A lokacin da hukumar ta EFCC ta gurfanar da shi kan tuhumar da take ma shi na aikata laifuka shida, da suka kai Naira milyan 864 na cin hanci da yin bayyanin karya kan kadarorin da aka mallaka. Shi kuwa dan na shi ana tuhumar sa ne kan aikata laifuka 15 duk na cuwa-cuwar kudin.

 

 • Sanata Dino Melaye, Ana TuhumarSa Da Saye Da Sayar Da Bindigogi

Tilas ne Dino Melaye, ya yi wa, sa’a da kuma rashin lafiyar da suka ceci shi daga shiga kurkuku, domin kuwa a hannun ‘yan sanda ne kadai ya zauna.

Ba wai tuhuma ce ta yin cuwa-cuwa ake tuhumarsa da aikata wa ba, sai dai tuhuma ce ta hada baki da aikata laifi gami da mallakan bindigogi ba bisa ka’ida ba, da sauran su. Matsalar na shi ne ta kai ga gayyata ukun da aka yi wa Shugaban ‘yan sanda na kasa, Ibrahim Idris, zuwa Majalisar, wanda duk kuma ya bijire wa zuwa Majalisar, wanda hakan har ta kai ga ayyanawar da Majalisar ta yi masa da makiyin tafarkin Dimokuradiyya wanda kuma sam bai cancanci rike mukamin na shi ba, da ma kowane irin mukami ne a ciki ko ma wajen kasarnan.

 

 • Sambo Dasuki, Tsohon Mai Ba Shugaban kasa shawara Kan Harkar Tsaro

Tsohon Mai Baiwa Shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Kanar Sambo Dasuki, ya kwashe watanni 31 a yanzun haka garkame, bisa zargin yin watanda da dala bilyan 2.1, na sayan makaman yaki. Yawancin tuhume-tuhumen da ake yi wa manyan ‘yan siyasan duk sun samo asali ne daga gare shi. Daga cikin wanda ake zargin da an yi masu watandan kudaden na makamai sun hada da, tsohon gwamnan Jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa, da takwaransa na Jihar Kano, Ibrahim Shekarau, Raymond Dokpesi, Bello Haliru da dansa, Musiliu Obanikoro da dansa.

 

 • Babangida Aliyu, Tsohon Gwamnan Neja

Tsohon gwamnan Jihar Neja, Babangida Aliyu, hukumar ta EFCC ta rike shi bisa zargin yin amfani da mukaminsa na gwamna wajen karkatar da kudade.

Babangida Mu’azu, ana tuhumarsa ne da laifin karkatar da Naira bilyan 2 na zaizayar kasa ta fuskacin siyasar sa.

 

 • Fani-Kayode, Da Nenadi Usman

A rana guda ne ta watan Yuni 2016, tsohon Ministan Jiragen sama, Femi Fani-Kayode, da Ministar kudi, Nenadi Usman, aka garkame su a gidajen yari daban-daban, bayan an gabatar da su a gaban kotu a Legas, kan tuhumarsu da laifin yin cuwa-cuwan Naira bilyan 4.9. Hukumar EFCC ce ta gurfanar da su a gaban mai shari’a Sule Hassan, kan tuhumarsu da aikata laifuka 17. Yayin da aka culla Fani Kayode, kurkukun Ikoyi, ita kuwa Nenadi, a garkame ta ne a kurkukun kirikiri, wanda ba shi ma da waje na musamman da aka tanada domin mata.

 

 • Dariye, Tsohon Gwamnan Filato

Na baya-bayan nan shi ne, Sanata Joshua Dariye, (APC Filatau ta tsakiya), a ranar Talata ne aka yanke ma shi hukunci na zaman shekaru 14 a gidan yari, kan aikata laifin cin amana da kuma wasu shekarun biyu bisa aikata laifin barnatar da dukiyar al’umma, amma duk biyun za su tafi ne a jere. Dariye, wanda ya canza sheka zuwa Jam’iyyar ta APC a watan Satumba 2016, mai shari’a Adebukola Banjoko, na babbar kotun tarayya ta Abuja ne ya zartar masa da hukuncin.

Shi ne dan Jam’iyyar ta APC na farko da aka daure. Daga cikin tuhume-tuhume 23 da ake ma shi, an same shi ne da laifi kan tuhumomi 15, da suka hada da cin amana da barnatar da dukiyar al’umma. An kuma sallame shi kan tuhumomi takwas. An fara gurfanar da dan Majalisar ne a watan Yuli na shekarar 2007. Ana tuhumarsa ne kan kudaden da suka kai Naira bilyan 1.16 da ya yi cuwa-cuwar su a shekaru sama da 10.

 
Advertisement

labarai