Manyan ‘Yan Wasan Da Ba Za Su Buga Gasar Turai Ba

Gasar Turai

Ranar Juma’a za a fara gasar cin kofin nahiyar Turai da kasashe 24 za su barje gumi a tsakaninsu a bana duk da cewa tun a bara ya kamata a gudanar da gasar da Portugal ke rike da kofin, amma cutar korona ta kai tsaikon da aka dage karawar zuwa bana.

Sai dai kuma kawo yanzu akwai fitattun’yan wasa biyar da suka taka rawar gani a kwallon nahiyar Turai, amma ba za su buga gasar da za a fara ranar Juma’a ba kuma cikinsu har da dan kwallon tawagar Norway da Borussia Dortmund, Erling Haaland wanda kasarsa ba ta samu tikitin shiga wasannin ba.

Sauran sun hada da dan wasan tawagar Sweden, Zlatan Ibrahimovic na AC Milan da dan wasan baya Sergio Ramos na Sifaniya da na tawagar Netherlands, Virgil van Dijk wanda yaji ciwo a Liberpool.

Erling Haaland, dan kwallon tawagar Norway mai shekara 20:

Kamar yadda ake fada dan kwallon ya kai darajar Yuro miliyan 100 a kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo, kuma Haaland shi ne fitaccen dan wasa da ke kan ganiya da ba zai buga gasar nahiyar Turai ba.

Haaland ya yi wa tawagar ‘yan wasan kasar Norway wasanni biyu na neman shiga gasar Turan da na cike gurbi guda daya, kuma bai ci kwallo ba da kasar ta kasa kai banten ta a karon farko tun shekara ta 2000.

Zlatan Ibrahimovic, dan wasan tawagar Sweden mai shekara 39.

Kowa ya yi mamaki da aka ji sanarwar cewar dan kwallon AC Milan zai koma buga wa Sweden wasa, bayan shekara biyar da yin ritaya daga buga wasa a kasar tasa duk da cewa matakin nasa ya janyo cece kuce a duniya.

Wata kwallo da ya ci Italiya a gasar 2004 daya ce daga mafi kayatarwa da aka zura a raga a tarihin gasar nahiyar Turai kuma Ibrahimobic ya bayar da kwallo biyu aka zura a raga a wasa biyu da ya yi wa tawagar a karawar neman gurbin shiga gasar bana, sai dai kuma raunin da ya yi a gwiwar kafa ya hana shi zuwa buga wasannin bana.

Sergio Ramos, dan wasan tawagar Sifaniya, mai shekara 35:

Da dan kwallon Real Madrid da Sifaniya ya buga gasar cin kofin nahiyar Turai ta bana da ya zama kan gaba a yawan buga wasanni mai 180 sai dai matakin kin gayyatar tasa ya janyo cece-kuce a fadin duniya.

Sai dai kuma kocin na Sifaniya bai zabi gayyatar kyaftin Ramos ba, wanda ya lashe gasar Turai a shekarar 2008 da kuma shekarar 2012, sakamakon raunin da yake ta jinya wanda yasa bai buga wasanni ba da dama a kakar wasan data gabata.

Ansu Fati, dan kwallon tawagar Sifaniya, mai shekara 18:

Ana kwatanta dan wasan Barcelona da cewar yana da kwarewar buga wasa da zura kwallaye a raga kamar yadda ya yi a gasar rukuni-rukuni da kuma a gasar cin kofin zakarun turai na  Champions League.

Ya kafa tarihin matashin da ya ci wa tawagar kasar Sifaniya kwallo, sai dai kuma ba zai samu damar buga wa kasar babbar gasar ba, sakamakon raunin da ya yi a watan Nuwamba, kuma har yanzu bai warke ba.

Virgil van Dijk, dan wasan Netherlands, mai shekara 29:

Dan wasan Netherlands shi ne ake alakantawa da mai tsaron baya mafi fice kawo yanzu, mai buga wasa  a kungiyar kwallon kafa ta Liverpool wadda ta lashe gasar cin kofin firimiya a shekarar data gabata.

Sai dai kuma dan wasan ya ci karo da koma baya, sakamakon raunin da ya yi da hakan ya kai tsaiko ga wasannin Liberpool, kuma dan kwallon bai warke ba da hakan ya kasa yi wa kasar wasan farko

Exit mobile version