Manyan Yunkuri Biyar Da Aka Taba Yi Na Dauke Kabarin Annabi (SAW) Daga Madina

Kabarin Annabi

Daga Rabi’u Ali Indabawa,

Annabi Muhammad (SAW), shi ne Annabin karshen zamani wanda aka haife shi a Makkah ya yi Hijra ya koma Madina. Musulmi sun yi imanin cewa babu sauran wani Annabi da zai zo bayansa har ya zuwa ranar tashin alkiyama, saboda Allah ya cika Addininsa da ya zama shiriya ga Musulmi ta hanyarsa. Ga wani takaitaccen nazari a kan yunkurin da aka taba yi kusan sau biyar na dauke jikinsa daga Madinarsa (SAW). Shabbaki (Kabarin) Annabi Sallahu alaihi wasallama yana nan a Madina. An sha yunkurin tono jikinsa mai tsarki  Sallallahu alaihi wasallama daga Raudarsa da aka rufe shi.

Yunkurin Farko

Yunkurin farko na satar gawar Annabi Muhammad (SAW) tare da sauya shi daga Madina zuwa Masar, an yi shi ne a farkon shekara ta biyar da fara kirga shekarun hijrah. Sarkin Masar Ba Amrullah ne ya bayar da umarnin. Ya kasance mugun mutum, da ya shirya wannan ɓarnar don jawo hankalin duniya zuwa Masar. Basaraken ya kashe kudi da yawa don aiwatar da wannan aiki.

Ya aika Abu Al-lfateh zuwa Madina don ya gudanar da shirin. Lokacin da Abu Al-Fateh ya isa Madina, mazauna Madina sun san labarin makircin da ya zo da shi, sai suka kama shi suka kusa kashe sojojin da ya zo da su.

Wannan ya sa Abu Al-Fateh firgita. Ya ce, “Ba zan taɓa aiwatar da wannan kazamin shirin ba ko da kuwa mai Sarkin da ya sa ni zai kashe ni,” ya yi tunanin haka a zuci kenan ba jimawa sai babban hadari ya ratsa wannan yankin da maraice. Gidaje da dabbobi da mutane da yawa sun mutu sakamakon ruwan saman da aka yi mai isaka. Shikenan sai Abu Al-Fateh ya sami kyakkyawan uzuri don ya gudu daga Madina. Allah Ta’alah ya tseratar da Annabi Sallahu alaihi wasallam da Sahabbansa.

 

Yunkuri Na Biyu

Sarki Ba Amrullah ya shirya makirci na biyu amma bai yi nasara ba. Ya turo wasu mutane su sake sato jikin Annabi Muhammad. Sun fara zama a wani gida kusa da masallacin Annabi Sallallahu alaihi wasallam kuma sun fara tona rami mai ɓullewa don shiga cikin kabarin Annabi sallallahu alaihi wasallam. Ana cikin haka, sai walkiya ta fantsama yankin kuma aka ji wata murya na cewa ana shirin tono kabarin Annabinku! Nan take Mutanen Madina suka ruga da gudu daga gidajensu suka fara bincike, a karshe sun yi nasarar gano masu laifin suka kashe su duka.

 

Yunkuri Na Uku

Yunkuri na uku kan sace jikin Ma’akin Allah Sallallahu alaihi wasallama, an shirya shi ne a shekara ta 557 bayan Hijira.

An yi zargin cewa Kiristoci ne suka yi wannan shirin. Akwai wani shugaban addini a Misira da ake kira da Sultan Nuruddin Zanki, ya ga Annabi Sallallahu alaihi Wasallam a cikin mafarkinsa. Annabi sallallahu alaihi wasallam ya yi masa nuni zuwa ga wasu kunshi biyu masu launi ja, ya ce wa Sarkin “ku cece ni daga wadannan mutanen biyu”.

Bayan Sultan ya farka, sai ya bayyana mafarkin ga wani malami mai ba shi shawara mai suna Jamaluddeen. Malamin ya bashi shawarar cewa ya hanzarta ya ziyarci Madina. Lokacin da ya isa Madina, sai kuwa ya ga alamar waɗancan mutane da ke shirin aikata wannan danyen aiki. Sun yi ikirari kuma suka fada masa labarin ramin da suke hakawa. Sarkin ya ba da umarnin a kashe su.

Yunkuri Na Hudu

Yunkuri na hudu, an shirya shi ne ranar 29 ga Zul Kida, shekara ta 578 bayan Hijirah, wanda Kiritocin Siriya suka yi. Sun kama hanya sun yi nisa, bai fi kusan tafiyar kwana daya su isa Madina ba, sai wani shahararren jarumi Hajib Luhluh ya zo tare da rundunarsa wadanda suka kware a yakin teku suka cafke su.Yunkuri Na BiyarAkwai wani malami Shamsuddin Sawab Lamti, wanda yake shugaban ma’akatan Masallacin Ma’aikin Allah Sallallahu alaihi wasallama na Madina. Sawab, yana da wani aboki da ya zama mafi kusanci da Sarkin Madina a wancan lokacin. Wata rana abokin nasa ya fada masa cewa, akwai wasu mutane da suka zo daga yankin Halb, sun bai wa sarkin Madina cin hanci kuma sun nemi ya bari su tone kabarin Manzon Allah Sallahu alaihi wasallama da Sahabbansa biyu. Da jin haka sai hankalin Sawab ya tashi. Ba da jimawa ba kuma, sai wani dan aiken Sarkin Madina ya zo ya kira Sawab zuwa gaban Sarki. Bayan da suka je, Sarkin ya ba Sawab umarnin cewa “Wasu mutane za su zo su kwankwasa kofar Masallacin Annabi Muhammad Sallallahu alaihi wasallama’ da daddare, idan sun zo ka bude musu kofar, kuma ka bar su su yi duk abin da suke so a wurin, kar ka tsoma baki a kan duk abin da za ka gani ko ta wace hanya.”Sawab ya amsa wa Sarkin da irin amsar da  yake so. Bayan Sallar Isha, an rufe kofar masallacin Annabi Sallallahu alaihi wasallama kamar yadda aka saba. Sai kuwa aka kwankwasa kofa, Sawab ya bude kofar, Sai ga mutane 40 suna shiga cikin masallacin, yana lissafa su daya bayan daya. Suna dauke da kayan aikin rushe gini kuma suna dauke da fitila ta haskawa. Suna kan hanyar zuwa daki mai alfarma har sun kai matakin da za su fara aikin, kawai aka yi wata girgizar kasa, suka afka ciki su da kayan aikin nasu gabadaya, sai ya zamto babu wata alama da ta rage da za a ce an taba yin su a duniya ma. Sarki ya yi jiran ganin dawowarsu na wani lokaci ya ji shiru, daga karshe ya aika aka kirawo Sawab ya tambaye shi, ‘Sawab wasu mutane sun zo wurin ka? Ya ce ‘Eh, amma gaba dayansu an hallaka, sun nutse a cikin kasa.” Sawab ya nemi Sarkin ya zo ya gane wa idanunsa abin da ya faru, da sarki ya zo ya gani, sai ya ce wa Sawab to ya kame bakinsa wannan ya zama sirri ka da ya bari kowa ya ji.

Sun yi nufin makirci, amma Allah ya fi su iyawa

 

Mun ciro muku wannan bayani daga The Saudi Expert

 

Exit mobile version