Manzon Allah (SAW) Ba Ya Neman Ladan Isar Da Manzanci Sai Dai Soyayya Ga Danginsa

Manzon Allah

Tare da Shehu Isma’ila Umar Almaddah (Mai Diwani)

Assalamu alaikum wa rahmatullahi ta’ala wa barkatuh. Masu karatu za mu dora karatunmu daga wanda muka kawo muku a makon jiya.

Abdullahi bin Abbas (RA) ya tafi a kan cewa ayar nan da ta ce “Ka ce ni ba na neman wani Lada a cikin isar da sakon nan, sai dai nuna soyayya ga makusantana”, tana nufin kira ne ga duk danginsa da su Larabawa su so Manzon Allah (SAW) saboda kusancinsa da su.

Dalilin saukar ayar shi ne, wasu ne daga cikin Sahabbai (RA) suka hada kudi mai yawa suka ba Manzon Allah (SAW) a matsayin tukwicin sakon Musuluncin da ya kawo, sai Allah ya ce a mayar musu, Manzon Allah don Allah ne ya kawo sakon ba don su biya ba.

Manzanni ba su rokon a biya su ladan sakon Allah da suke isarwa kuma su shiryayyu ne.

A kan wancan maz’habar ta Abdullahi bin Abbas (RA), Imamu Bukhari da Muslim sun ruwaito Hadisi a kai daga Muhammadu bin Basshari, daga Muhammadu bin Ja’afari, daga Shu’ubatu, daga Abdulmaliki bin Maisarata ya ce, “Na ji Dawusu (Almajirin Abdullahi bin Abbas) yana fada cewa an tambayi Abdullahi bin Abbas (RA) shin mecece fassarar ayar da ta ce “ba na neman Lada daga gare ku, sai dai soyayya a cikin dangina?”, sai Sa’idu (wani malamin Kuraishawa) bin Jubairu bin Mud’amu bin Adiyyi ya yi sauri (kafin Abdullahi bin Abbas ya ba da amsa) ya ce “abin da ake nufi da dangi makusanta su ne iyalan gidan Annabi (SAW), sai Abdullahi bin Abbas ya ce ma sa “ka yi gaggawa, babu wani dangi na Kuraishawa face Manzon Allah (SAW) yana da kusanci da su, abin da ayar take nufi shi ne “sai dai ku sada abin da yake tsakanina da ku na zumunta.”

Ibin Hajaral Askalani ya ce wannan fassara ta Sa’idu bin Jubairu ita ce wadda Aliyu bin Hussain (Zainul Abidiyn RA) yake kai, haka nan galibin malamai, ma’ana ana nufin a so iyalan gidan Manzon Allah (SAW). Manzon Allah (SAW) yana da dangi da yawa, amma babu wadanda suka fi alfahari da shi kamar ‘ya’ya musamman wadanda suka fita daga jikinsa (SAW).

Baya ga Aliyu Zainul Abidyn da ke kan wancan fassarar, Malamai irin su Saddi da Amru bin Shu’aibin duk sun tafi a kai kamar yadda Imamud Dabari ya fitar daga gare su. Idan an dauki fassarar da Sayyidina Aliyu Zainul Abidiyn (RA) ya tafi a kai ne, to ayar tana kira ne ga dukkan duniyar musulmi su so dangin Annabi (SAW) makusanta. Idan kuma fassarar Sayyidina Abdullahi bin Abbas (RA) aka dauka, to magana ce ake yi da Kuraishawa wadanda Annabi (SAW) ya fito daga cikinsu, ma’anar “min anfusikum” na cikin “Lakad ja’akum”.

Idan kuma an dauki cewa ayar da Muminai take magana a matsayin makusanta, to ko wane Mumini ya shiga cikin makusantan Annabi (SAW), saboda Manzon Allah (SAW) ya ce wa Salmanul Farisi yana daga cikin iyalan gidansa. Don haka kowane Mumini shi ma yake alfahari da cewa daga cikinsu ne Manzon Allah ya fito.

Da yake duk dangi suna alfahari da samun Manzon Allah (SAW) a cikinsu, mu ma a nan Afirka, Shehu Ibrahim Inyass (RA) ya ce muna alfahari da zamowar mu surukan Annabi (SAW) saboda ya yi sa-daka da Sayyida Mariyatul Kibdiya (‘Yar Misra daga kabilar Kibdayawa bakaken fata). Annabi (SAW) ya ce wa Sahabbai “idan kun bude Misra ku zauna mun da sirikaina lafiya”. Bayan Nana Khadija (RA) ta haifa wa Annabi (SAW) ‘ya’ya shida, babu wacce ta kuma haihuwa a cikin matansa masu girma da daraja sai Mariyatul Kibdiya wacce ta haifa masa Ibrahimul Mu’azzamu. Shehu Ibrahim (RA) ya ce wannan shi ne babban rabonmu, kenan muma muna da wani abu na kusanci da za mu yi alfahari da shi (SAW).

Haka nan Annabi (SAW) ya yi aure a cikin Yahudawa, don haka su ma za su yi alfahari da shi inda za su musulunta. Ya auri Sayyida Safiyyatu bintu Huyayyi bin Akhbar.

Wani abu na mata ya taba hada ta da Sayyida Aisha (RA) ta ce mata “Bayahudiya kawai”! Sai ta je da kuka ta fada wa Manzon Allah (SAW), sai Annabi (SAW) ya ce mata “A’a, ai ke kin wuce nan, ke ‘yar Annabi Musa ce ‘yar’uwan Annabi Haruna (AS).

Kowa zai yi alfahari da Annabi (SAW) kuma abin ya zamo ceto a gare mu ranar Alkiyama Albarkarsa (SAW). Yabon Da Allah (SWT) Ya Yi Wa Annabi SAW (3) Har yanzu dai a kan ayar Lakad ja’akum muke bayani dangane da fassara ko ma’anar kalmar “min anfusikum” da ake karantawa da rufu’a ko “min anfasikum” da ake karantawa da fataha, kamar yadda aka samu daga wurin malamai. Karatuttukan da muka yi a baya a karkashin wannan (makwanni biyu da suka gabata) duk gabaki daya suna bayani ne a kan karanta kalmar da “rufu’a”.

Idan kuma muka koma bangaren wadanda suka tafi a kan “fataha”, “min anfasikum” ma’anar kalmar ita ce: Annabi (SAW) ya zo muku ne a matsayin mafi daukakar daraja a cikinku kuma mafificinku. Karantawa da “rufu’a” ko “fatahar” duk yabo ne ga Annabi (SAW).

Alkur’ani ya nuna Manzon Allah (SAW) mafificin kowa da kowa ne baki daya. Bayan wannan kololuwar yabo da Allah ya yiwa Annabi, Allah ya kuma siffanta shi da kyawawan siffofi abin yabo da godewa da kirari masu yawa. Allah (SWT) ya ce “Annabi (SAW) mai kwadayi ne a bisa shiriyar al’ummarsa (na shiga Musulunci da kara Imani a ciki), da nuna damuwa a kan duk abin da zai wahalar ya cutar da al’ummarsa a duniya da lahira, da nuna rahama da jinkansu (Muminai). Wani sashe na Malamai sun ce Allah ya ba Annabi (SAW) wadansu sunaye guda biyu daga cikin nasa (SWT).

Allah shi ne Ra’ufu (mai tausayi) kuma Rahimu (mai jinkai) amma sai ya ba Manzon Allah. Amma duk da haka, kyautar sunayen ba ta sa Manzon Allah ya zama Allah ba. Sunayen na Allah ne, shi kuma Annabi an bashi ne saboda girmansa a wurin Allah, ba nasa ba ne. Kamar misali, wani Alhaji mai kudin gaske zai iya baiwa wani talaka rigarsa mai tsada ya sa, komai wuce wurin talakan nan ai don an bashi rigar Alhaji ya sa, ba zai shiga gidan Alhajin ya ce ya zama nasa ba saboda ya sa wannan rigar.

Amma kuma samun rigar daraja ce sosai a wurin talakan. Ba wadannan sunayen biyu ba kawai, akwai Malaman da suka kirga sunayen Allah guda 70 da Allah ya ba Annabi (SAW). Wasu Malaman kuma sun ce dukkan sunayen Allah guda 99 Allah ya ambaci Manzon Allah da su in ban da guda daya shi ne “Allahu”.

Haka nan, yana daga kirarin da Allah (SWT) ya yiwa Annabi (SAW) a cikin ayar nan ta Suratu Ali’imran, “Allah ya yi baiwa ga Muminai da ya aiko Annabi daga cikinsu…”. Da kuma wata aya ta Suratul Jumu’ah, “Allah shi ne ya aiko da Manzo a cikin Ummiyyai (Mutanen Makka ko Larabawa)…”. Da fadin Allah (SWT) a wata ayar, “Kamar yadda muka aiko da Babban Manzo a cikinku…”.

An karbo daga Sayyidina Aliyu bin Abi Dalib (Karramallahu waj’hahu) cewa, ma’anar fadin Allah (SWT) “Manzo ya zo daga cikinku” kamar yadda ya ji daga Annabi (SAW), ita ce “Annabi ya fi kowa dangi (babu dangi irin nasa), babu surukai irin nasa, babu iyaye irin nasa ko wanda yake da kwarewa irin tasa”, nasabarsa tun daga kan Annabi Adam (AS) har zuwa iyayensa (SAW) dukkansu aure ne suka yi babu zina”. Malam ibn Khaldun ya ce ya kirga uwaye 500 a nasabar Annabi (SAW) har zuwa kan Annabi Adam (AS), amma ba a samu wadda zina ce ta yi ba aure ba kuma bai samu tarihin wani daga cikin iyayensa (SAW) sun aikata abin da jahilan lokutansu suka rika aikatawa ba.

An karbo daga Sayyidina Abdullahi bin Abbas (RA), ya ce ma’anar ayar “da jujjuyawar ka a cikin masu sujada” ita ce Allah ya fitar da tsatson Annabi (SAW) daga Annabi zuwa Annabi har shi ma ya fitar da shi Annabi. Ma’ana nasabar Annabi ba ta taba bi ta wurin wanda ba Annabi ba. Shi a wurin Abdullahi bin Abbas (Farfesan Al’umma), duk iyaye da kakannin Annabi (SAW) Annabawa ne.

Annabi shi ne wanda ake ma sa wahayi na shiriya amma ba a umurce shi ya isar ga kowa ba don ya shiryar da shi. Manzo kuma shi ne wanda aka saukar masa da shiriya sannan aka umurce shi ya isar ga wadanda aka aiko shi wurinsu. Hakika da a yanzu ana bin irin wannan karatu da fahimta ta magabata na kwarai, masu fadar munanan kalamai a kan iyayen Annabi (SAW) ba za su yi ba. Domin Sahabin Annabi ne ya ce iyayensa (SAW) Annabawa ne.

Exit mobile version