Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RA'AYINMU

Maraba Da Lokacin Hunturu…

by Tayo Adelaja
October 27, 2017
in RA'AYINMU
3 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

A shekara ana da yanayi da ke jujjuyawa a tsakanin rani da damina da suka haɗa da bazara, damina, kaka da hunturu.

Rani yana kamawa daga ƙarshen watan Oktoba har zuwa watan Maris. Amma daga watan Disamba zuwa ƙarshen Fabarairu shi ne ake ce wa tsakiyar rani. A tsakanin lokacin ciyayi na bushewa da wasu itatuwa, sannan mafi akasarin bishiyoyi sukan yi kakkaɓar ganye saboda ƙafewar danshin ƙasa da suka baza jijiyoyinsu a ciki.

samndaads

Kowane lokaci yakan zo da irin ɗabi’unsa, bazara an san ta da zafi, damina an santa da ruwa, kaka an santa da fara ɗaukewar ruwa sai kuma hunturu da aka sani da sanyi da ƙura da buji da iska.

Hunturu yakan kankama sosai idan aka zo ƙarshen watan 11 zuwa tsakiyar Disamba. Sanyi yana tsananta, hazo da buji su bazu a ko ina sannan yankunan da suke kusa da Sahara (Borno, Katsina, Sakkwato Kebbi da sauran su) su fuskanci ƙura da iskar rairayi wani lokaci ma har da guguwa.

Akwai cututtuka da wannan yanayi yakan haifar ko ƙarfafa su waɗanda ya kamata kowa ya yi rigakafin kamuwa da su.

 

Likitoci sun shawarci mutane su riƙa amfani da abubuwan ci waɗada suke ɗauke da sinadarin Ɓitamin C kamar su lemon zaƙi, kankana da sauran su. Sannan ana buƙatar ƙara shan ruwa sosai da kuma kiyaye tsaftar duk wani abu da za a iya ci. Amfani da abubuwan nan zai ƙarfafa garkuwar jiki da kuma rigakafin kamuwa da cututtukan da ake iya ɗaukawa a yanayin Hunturu.

A wasu lokutan na Hunturu, manyan hadari kan taru amma babu komai a ciki sai zunzurutun ƙura da buji wadda abin yakan iya haifar da guguwa, ƙasa ta rufe idanu sannan jiragen sama sai su kwashi kwanaki ba su tashi ba saboda rashin kyawon yanayi.

Sauran matsalolin da jama’a kan iya fuskanta a fatar jiki sun haɗa da bushewar fata, cikewar ido da ƙasa da kuma masu ciwon asama (mai tsohe numfashi).

Har ila yau, yanayin yana motsa ciwon shawara, da tari, sannan ta sanadiyyar wasu ƙwayoyin cututtuka da ke yaɗo ana iya saurin kamuwa da ciwon ido (apolo).

Don haka ya zama wajibi kowa ya yi rigakafin waɗannan cututtukan da ma wasu da ba mu ambata ba ta hanyar sanya kayan tsare sanyi da tabbatar da tsafta ba tasaka-tsami ba da kuma kiyaye yara da tsofaffi ta hanyar yi musu abubuwan da suka dace a kan kariyar sanyin.

Masu amfani da wuta wurin jinɗimi su yi hattara, wutar na iya haifar musu da gobara a gida ba ya ga illar da za ta yiwa kiwon lafiya musamman idan aka cika yin kusa da ita.

Iyaye su kuma kula da yaran da kan yi sha’awar wasa da wuta a lokacin, domin kasancewar galibin abubuwa suna bushewa a yanayin na hunturu, nan da nan gobara za ta iya tashi.

Masu ababen hawa da ke kara-kaina a kan tituna, ya zama wajibi su rage gudu domin hazo da buji na iya rufe nisan gani, idan mutum bai yi wasa ba zai iya jin sa a rami ko kuma ya gwabza wa wani mai abin hawa. Bugu da ƙari, idan so samu ne a rage tafiye-tafiyen dare a lokacin na hunturu domin baya ga duhun dare, hazo yana ƙara rikita yanayin.

 

Da fatan za mu ga wucewar lokacin na hunturu da ke tinkaro mu lami lafiya.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

SHAFIN FARKO

Next Post

Badaƙalar Maina: Tsakanin Dambazau Da Oyo-Ita, Wane Ne Mai Gaskiya?

RelatedPosts

Kannywood

Alhakin Shiga Tsakanin ’Yan Kannywood Da Afaka Ya Rataya A Wuyan Ganduje

by Muhammad
5 days ago
0

Masana sha’anin shari'a suna cewa, da a yi kuskuren hukunta...

Dambarwar Najeriya Cikin Shekaru 60: Murna Ya Kamata Mu Yi Ko Kuka?

Yayin Da Nijeriya Ta Cika Shekaru 60 Da ‘Yancin Kai…

by Muhammad
5 months ago
0

A jiya ne Nijeriya ta yi bikin cika shekaru 60...

Gwamnatin Tarayya Za Ta Kafa Cibiyar Jinkan Tsofaffi – Minista Sadiya

Kafa Hukumar Kula Da Nakassasun Nijeriya Da Dawo Da Martabarsu

by Muhammad
5 months ago
0

A ranar Litinin, 24 ga Agusta na 2020 ne, Shugaban...

Next Post

Badaƙalar Maina: Tsakanin Dambazau Da Oyo-Ita, Wane Ne Mai Gaskiya?

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version