A makon da ya gabata, warhaka akwai sassan da aka yi musu ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a yankin Arewacin Nijeriya ciki har da Babban Birnin Tarayya Abuja, amma sai gashi a wannan makon za a iya ƙirga kwana shida da shigowar ƙaramin buji da sanyi da iska da ƙura wanda ke alamta cewa hunturu ya sawo kai.
A shekara ana da yanayi da ke jujjuyawa a tsakanin rani da damina da suka haɗa da bazara, damina, kaka da hunturu.
Rani yana kamawa daga ƙarshen watan Oktoba har zuwa watan Maris. Amma daga watan Disamba zuwa ƙarshen Fabarairu shi ne ake ce wa tsakiyar rani. A tsakanin lokacin ciyayi na bushewa da wasu itatuwa, sannan mafi akasarin bishiyoyi sukan yi kakkaɓar ganye saboda ƙafewar danshin ƙasa da suka baza jijiyoyinsu a ciki.
Kowane lokaci yakan zo da irin ɗabi’unsa, bazara an san ta da zafi, damina an santa da ruwa, kaka an santa da fara ɗaukewar ruwa sai kuma hunturu da aka sani da sanyi da ƙura da buji da iska.
Da yake hunturu yana zuwa da sauyin yanayi mai ƙarfi da salo iri-iri, mutane su ma sukan juya domin zamantakewarsu ya dace da yanayin. ‘Yan kasuwa masu sana’ar kayan rufe sanyi (rigunan sanyi, hulunan sanyi da safa) da zarar hunturu ya shiga kakarsu ta yanke saƙa. Cinikin kayan yakan kankama babu kama hannun yaro saboda kowa musamman waɗanda fita ta zama masu dole su yi shigar da za ta rage sanyin ratsawa jikinsu walau ta kai ko ta ƙafa ko kuma ta gangar jikin baki ɗaya.
Akwai cututtuka da wannan yanayi yakan haifar ko ƙarfafa su waɗanda ya kamata kowa ya yi rigakafin kamuwa da su.
Likitoci sun shawarci mutane su riƙa amfani da abubuwan ci waɗada suke ɗauke da sinadarin Ɓitamin C kamar su lemon zaƙi, kankana da sauran su. Sannan ana buƙatar ƙara shan ruwa sosai da kuma kiyaye tsaftar duk wani abu da za a iya ci. Amfani da abubuwan nan zai ƙarfafa garkuwar jiki da kuma rigakafin kamuwa da cututtukan da ake iya ɗaukawa a yanayin Hunturu.
A wasu lokutan na Hunturu, manyan hadari kan taru amma babu komai a ciki sai zunzurutun ƙura da buji wadda abin yakan iya haifar da guguwa, ƙasa ta rufe idanu sannan jiragen sama sai su kwashi kwanaki ba su tashi ba saboda rashin kyawon yanayi.
Sauran matsalolin da jama’a kan iya fuskanta a fatar jiki sun haɗa da bushewar fata, cikewar ido da ƙasa da kuma masu ciwon asama (mai tsohe numfashi).
Har ila yau, yanayin yana motsa ciwon shawara, da tari, sannan ta sanadiyyar wasu ƙwayoyin cututtuka da ke yaɗo ana iya saurin kamuwa da ciwon ido (apolo).
Don haka ya zama wajibi kowa ya yi rigakafin waɗannan cututtukan da ma wasu da ba mu ambata ba ta hanyar sanya kayan tsare sanyi da tabbatar da tsafta ba tasaka-tsami ba da kuma kiyaye yara da tsofaffi ta hanyar yi musu abubuwan da suka dace a kan kariyar sanyin.
Masu amfani da wuta wurin jinɗimi su yi hattara, wutar na iya haifar musu da gobara a gida ba ya ga illar da za ta yiwa kiwon lafiya musamman idan aka cika yin kusa da ita.
Iyaye su kuma kula da yaran da kan yi sha’awar wasa da wuta a lokacin, domin kasancewar galibin abubuwa suna bushewa a yanayin na hunturu, nan da nan gobara za ta iya tashi.
Masu ababen hawa da ke kara-kaina a kan tituna, ya zama wajibi su rage gudu domin hazo da buji na iya rufe nisan gani, idan mutum bai yi wasa ba zai iya jin sa a rami ko kuma ya gwabza wa wani mai abin hawa. Bugu da ƙari, idan so samu ne a rage tafiye-tafiyen dare a lokacin na hunturu domin baya ga duhun dare, hazo yana ƙara rikita yanayin.
Da fatan za mu ga wucewar lokacin na hunturu da ke tinkaro mu lami lafiya.