Maraba Da Maganin Rigakafin Cutar Maleriya

Maleriya

Al’ummar duniya sun yi matukar farin cikin musamman a Nijeriya a yayin da Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO) ta sanar da amincewa da fara aiki da safurin maganin rigakafin cutar maleriya mai suna RTS, S/AS01 (RTS, S) ga kananan yara a yankin Afrika da sauran yankuna a duniya, gwajin maganin za a yi ne a kan safurin cutar maleriya nan ne da ke kira da P. falciparum. Wannan amincewar ta samo asali ne sakamakon nasarar da aka samu a kan gwajin da ake yi na maganin rigakafin a kasar Ghana, Malawi da Kenya inda aka yi wa yara fiye da 800,000 allurar tunda aka fara aikin a shekarar 2019.

Maganin rigakafin na RTS, S ya samu ne sakamakon aiki tukuru na tsawon shekara 30 da kamfanin hada magunguna na GladoSmithKline plc (GSK) da hadin gwiwar PATH, tare da kuma tallafin wasu cibiyoyin bincike na kasashen Afrika.

“Wanan wata babbar tarihi ce, samar da maganin rigakafi wani nasara ce da aka samu a fannin kimiyya da fasaha, lafiyar yara kanana da kuma kokarin kawo karshen cutar maleriya a fadin duniya,” inji shugaban hukumar WHO Dakta, Tedros Adhanom Ghebreyesus. “Amfani da wannan maganin rigakafin tare da sauran hanyoyin da ake amdani dasu a halin yanzu zai kai ga ceto rayukan yara da dama duk shekara.” Inji shi.

Cutar Malariya dai na sanadiyyar rashin lafiya da mutuwar yara da dama a yankin Afrika. Cuta ce mai barazana ga rayuwa ana kuma yada cutar ne ta hanyar cizon macen sauro da ake kira da ‘Anopheles moskuitoes’. Ana iya kare daukar cutar da kuma warkar da ita. An kiyasta mutum fiye da Miliyan 229 suka kamu da cutar a fadin duniya a shekarar 2019, an kuma kiyasta mutum 409,000 sun mutu sanadiyyar cutar a shekarar 2019.

Cutar ta fi barna ga yara ‘yan kasa da shekara biyar; a shekarar 2019, kashi 67 (274 000) na yara da suka mutu a duniya sakamakon kamuwa da cutar. Kungiyar WHO reshen Afrika ke dauke da mafi yawan masu fama da cutar a duniya, kididdigar da aka yi a shekara 2019 ta nuna cewa kashi 94 na wadanda ke kamuwa da cutar suna Afrika.

Abin takaicin, a ra’ayin wannan jaridar shi ne, yayin wasu kasashe suka fatattaki cutar maleriya, amma ta cigaba da zama annoba da barazana a yankin Afrika musamman Nijeriya, dalilin haka kuma a bayyana yake. Hukumar WHO ta ayyana fattakar cutar maleriya a kasashe 40 an kuma basu takardar shaidar fita daga kangin cutar, kasashen sun hada da El Salbador (2021), Algeria (2019), Argentina (2019), Paraguay (2018), da Uzbekistan (2018).

Haka kuma kasa Chana ce kasa ta farko da aka ba shaidar fatattakar cutar maleriya a yanki Asiya a wannan shekara a cikin shekara 30. Sauran kasashe da suka samu wannan matsayin a yankin sun kuma hada da (1981), Singapore (1982), da Brunei Darussalam (1987). An kakkabe cutar ne daga nahiyar Turai ta hanyar gamayyar feshi da amfani da magani da kuma tsaftace muhalli.

Rahoton ‘World Malaria Report’ na shekarar 2020 ya bayyana cewa, Nijeriya ce ke dauke da mafi yawan na masu dauke da cutar Maleriya a duniya inda take da kashi 27 na masu cutar a duniya, a shekarar 2019 masu cutar suka zama kashi 23 na adadin wadanda cutar ta kashe a duniya.

Masu cutar sun karu da kashi 3.5 a tsakanin shekarar 2016 da 2019, daga kashi 293 zuwa 303 a cikin mutum 1000 suna kuma fuskantar hadarin kamuwa da cutar a cikin wannan lokacin da ake bayani.

Ra’ayin wannan jaridar ita ce, muna maraba da wannan cigaban na samar da maganin rigakafin cutar maleriya. A kan haka muke kira ga gwamnatin tarayya da ta yi issashen shirin sayen maganin rigakafin da zaran an fara sayarwa. Barnar cutar maleriya ga al’ummar Nijeriya a kullum ya fi ta annobar cutar korona. Kada gwamnati ta jira sai an samu tallafin kasashe masu bayar da agaji kafin al’umma su samu wannan maganin rigakafin.

Muna kira ga gwamnati da ta fara gangamin fadakar da jama’a a kan bukatar karbar allurar da zaran an fara rabawa. An samu kiraye-kiraye daga malaman addini da wasu shugabanin siyasa a kan kada a karbi allurar cutar korona, bai kamata lamarin ya zama haka ba a kan maleriya.

Ya kuma kamata gwamnatin tarayya da fara nata kokarin na samar da allurar a cikin gida. Kamar yadda Shugaban Bankin Raya Afrika, Dakta Akinwunmi Adesina ya fada kwanakin baya, cewa, yakamata kasashen Afrika su fara samar da allura rigakafi maimakon yawo rokon alurar a kasashn duniya. Ya kara da cewa, Bankin Raya Afrikan zai zuba jarin Dala Biliyan 3 a bangaren hada magunguna don tallafa wa kamfanonin hada magunguna na Afrika ciki har da Nijeriya.

Hakoron kakkabe cutar maleriya gaba daya a Niejiya ya kamata a fuskanta, dole a mayar da dukkan karfi don cimma wannan manufar.

 

Exit mobile version