Tsohon ɗan majalisar dattawa mai wakiltar Zamfara ta Tsakiya, Sanata Kabiru Marafa, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC, inda ya zargi Shugaba Bola Tinubu da watsi da jihar Zamfara duk da irin gudunmawar da ya bayar a zaɓen 2023.
Marafa, wanda shi ne ya jagoranci yaƙin neman zaɓen Tinubu/Shettima a Zamfara, ya ce matakin da ya ɗauka ya biyo bayan taro na kwanaki biyu da ya yi da magoya bayansa a faɗin jihar. Bayan tattaunawa, ƙungiyar magoya bayan nasa ta bayyana cewa duk da nasarar Tinubu a Zamfara ƙarƙashin jagorancin Marafa, jihar ta ƙara fuskantar matsalar tsaro da kuma wariyar siyasa.
- Masu Sha’awar Shiga Harkar Fim Su Shiga Da Zuciya Daya -Auwal Marafa
- Marafa Ya Fice Daga APC, Ya Zargi Tinubu Da Watsi Da Zamfara
Ƙididdiga ta nuna cewa a shekarar 2024, Zamfara ce ta fi kowace jiha yawan sace-sacen mutane a Nijeriya, inda aka samu fiye da mutum 1,200 da aka yi garkuwa da su. Duk da haka, jihar ba ta samu komai daga gwamnatin Tarayya ba sai matsayin Ministan Jiha, alhali sauran jihohin Arewa maso Yamma sun samu ministoci biyu-biyu.
Ƙungiyar Marafa ta kuma zargi gwamnatin Tinubu da watsi da tsarinsa na siyasa da kuma rashin tallafawa al’ummar da ke fama da matsalolin tsaro. Daga ƙarshe, ta bayyana cewa Marafa da dukkan magoya bayansa a ƙananan hukumomi da mazaɓu 147 na Zamfara sun fice daga APC, kuma nan gaba za su bayyana sabon matsayar siyasar da za su bi.