Zubairu M Lawal" />

Marayu Da Zawarawa Sun Samu Tallafi Daga Uwargidan Gwamnan Nasarawa

Uwargidan Gwamnan Nasarawa

Uwargidan Gwamnan jihar Nasarawa Hajiya Silifata Abdullah Sule ta taimakawa Marayu marasa galihu da zaurawa masamman wadanda mazajensu suka rigayemu gidan gaskiya da kayan masarufi.

Taron da ya gudana a ranar Littinin wanda Gidauniyar Uwargidan Gwamnan mai suna Silifata Abdullah Sule (SAS) ta gudanar a harabar gidan Gwamnati a garin Lafia, ya samu halartan mabukata da aka gayyato domin samun tallafin.
Da take jawabi Uwargidan Gwamnan Kuma Giwan Matan jihar Nasarawa Hajiya Silifat Abdullah Sule ta ce mun duba munga akwai dubban mutani da basu iya dogaro da kafafunsu sakamon rashin samun galihu a rayuwa.
Wasu suna zaune ne babu abincin cin yau bare na gobe wasu mazajensu sun mutu sun barsu da kananan yara.
Hakan ya sanya muka zakulo wasu daga cikin su da muka ga ya dace mu fara kashi kashi. Cikin kananan Hukumomi 13 da muke da shi a wannan jihar akwai dubban marayu da suke rayuwa cikin rashin galihu.
Mun zakulo guda 300 muka kashe masu kimanin naira miliyon biyar.
Muna dauki marayu 150 zaurawa wadanda mazajensu suka mutu ko aurensu ya kare kuma suna cikin halin kunci da yara suma 150.
Hajiya Silifat tace wannan Gidauniyar zai cigaba da kewayawa wajen taimakawa marasa galihu a fadin jihar Nasarawa, sannun a hankali zamu rage yawan marayuwa dake rayuwa cikin kunci.
Ta kara da cewa “zamu sharewa marasa galihu da marayu da tsofafin mata da ke rayuwa cikin talauci yan Rabbana ka wadatamu hawaye.
Ta ce , wannan Gidauniyar ta (SAS) an tanadar da shine saboda duba rayuwar Marayu da kananan yara da tsofafi da suke rayuwa cikin kunci, domin taimakawa gare su.
Hajiya Silifata tayi kira ga sauran marasa galihu da Nakasassu dasu kara hakuri anabi daki daki ne saboda idan dambu yayi yawa bayajin mai.
Hajiya Silifata ta yi kira ga iyaye dasu daura yaransu akan tafarkin niman ilumi kada su barsu suna yawon tallace-tallace saboda babu abinda talla ke haifarwa face bakin ciki da bacin rai.
Ilumi shine cigaban kowata al’umma da darajarsu Kuma ilumin yara mata daga darajar Duniya ce.
Haka zalika ta bukaci matan jihar Nasarawa dasu kara hakuri saboda wannan Gwamnati ta Injiniya Abdullah Sule tana da kyakyawar kuduri na daga Darajar mata zuwa matakin nasara.
Itama da take jawabi Kwamishiniyar harkokin mata da walwala ta jihar Nasarawa Hajiya Halima Ahmad Jabiru ta godiya da irin wannan abin alheri da Uwargidan Gwamnan take yi na taimakawa marasa galihu.
Hajiya Halima tace ciwon ya mace ta ya mace ce, saboda sanin darajar yaran mata ya sanya Uwargidan Gwamnan Hajiya Silifat kullun tunaninta yadda zasu taimakawa mata manya da kanana.
Ta bukaci matan jihar Nasarawa da su kyale yaransu mata suna zuwa makaranta domin samun ilumi mai inganci. Tace Gwamnatin Injiniya Abdullah Sule na kowa da kowa ne, kowa da rawar da zai taka domin cin gajiyar romon Demokurdiyya.
Hajiya Zainab Aminu Muazu Maifata Uwargidan Shugaban karamar Hukumar Lafia. Tayi kira ga wadanda suka amfana da wannan tallafin dasu kara godiya ga Uwargidan Gwamnan kuma Giwan Mata mai taimakawa marasa galihu.
Ta bukaci da su kara baiwa Giwan Matan jihar Nasarawa da Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullah Sule hadin kai saboda sun damu da rayuwar da suke ciki.
Shi ya sanya a koda yaushe ake ta kokarin koyar da mata sana’o’in hannu domin dogaro da kai.
Hajiya Zainab Ahmad ta jinjinama wannan Gidauniyar dake samar da ayyukan yi ga Mata da matasa harma da tsofafi. Tayi kira ga al’umman jihar Nasarawa dasu baiwa Gwamna Abdullah Sule da Uwargidan sa goyon baya domin kai jihar Nasarawa zuwa ga tudun mun tsira.
Itama Dakta Hauwa Mainoma ta bukaci Mata dasu kara godiya ga Gwamnatin Injiniya Abdullah Sule saboda yadda akullun suke samun cigaba ta fannin abubuwan dogaro da kai.
Ta ce mata sunafi kowa amfana da wannan Gwamnati ta Injiniya saboda da hawan wannan Gwamnati matan da aka koyar da su Sana’a da basu jali na dogaro da kai suna dayawa.
Ta yabawa Hajiya Silifata saboda yadda take kokari wajen taimakawa mata da matasa da marayu.

Exit mobile version