Marigayi Gambu Me Wakar Barayi A Mahangar Kimiyyar Zamantakewa ‘SOCIOLOGY’

Gambu

Daga Idris Sulaiman Bala,

Kamar a kowacce al’umma, a kasar Hausa, barna da kangarewar yara, da kuma dabi’u marasa kyau ababen kyama ne. wannan kyama kuma ta biyo bayan tsammanin da al’umma ke da shi a kan mutanenta na kiyaye duk wasu ayyukan da suka sabawa ka’idar al’ada.  Bilhalisali ma, shi aikata barna wani al’amari ne tabbatacce a rayuwa, babu wata al’umma da ba a aikata barna a cikinta; don haka kasar hausa ba za ta zama ta tsallakewa irin wannan aiki ba. Kawai dai abu daya ake iya yi, shi ne a samar da hanyoyin dakile barnar.

Tun asali akwai barayi da ’yan fashi a kasar hausa, wadanda ke addabar mutane da muguwar dabi’ar sata. Sai dai sata ba ta samu karbuwa ba, saboda da jimawa iyaye da makusanta kan yi wa mutum hudubar cewa ya yi kowacce irin sana’a amma ban da sata.

Iyaye ba su cika damuwa da saba ka’idar ‘ya ‘yansu ba, matukar ba sata suke yi ba. domin kafa misali da yadda aka tsani sata a kasar hausa, muna iya waiwayan kalaman Abubakar Imam a littafinshi na ‘Magana Jari Ce’ wanda aka wallafa a shekarar 1976. Maganar ya yi ta ne dangane da Nomau:

“Ka iya sata? Ba fa sana’ar raggo ba ce, ba ko ta ’ya ’yan kirki ba ce, ba ta kuma masu tausayi da jin kai ba ce, ba ko ta masu gudun azaba ba ce. Sana’a ce ta tababbu wadanda Shaidan ya mallaki zuciyarsu. In kana iyawa, to, ko me ya faru gare ka duniya da lahira ka da ka yi kuka da dayan mu, (Imam, 1976:37).”

A wurin masana kimiyyar zamantakewa, a na iya yin nazarin wakokin Gambu ne ta hanyar bin diddigin kalamanshi da ke kumshe a cikin waka.  Kalaman na Gambu sukan fada cikin dayan wadannan: ingiza aikata barna, sabawa koyarwar addini, sabawa ka’idar al’umma, ingiza gaba, ingiza ta’asa.

Yana da kyau mu fahimci cewa ba Alhaji Gambu ba ne mawaki na farko da ya fara ko ya ke sabawa koyarwar addini, ingiza barna ko rura wutar gaba. Misali Dan – Anache a wakarsa ta ‘Shagon Mada’  ya na cewa:

“Dan Audu banda Sallar safe gama sallar safe na rage maka karfi.”

Haka kuma ya kara da cewa: “Kashe mutum a gafarta ma.”

Bari mu leka mu ga wuraren da za a iya tsintar kalaman da ke ingiza aikata barna, sabawa koyarwar addini, sabawa ka’ida a cikin wakokin Gambu.

Gambu bai taba boyewa wani laifinshi na ingiza aikata barna ba, bai kuma taba musanta alaka da mabarnata ba, kamar yadda ya ke fadi da bakinshi a wasu wakokinshi, inda ya ke cewa:

“Ni allimamin masu laihi. Duk inda nigga anata laihi ban wucewa.”

Ya kara da cewa:

“Ko wahitto kama masu laihi, in ya wuce Gambu yayi banna, kuma baya bidar masu laihi.”

Duk da cewa hatta shi Gambu ya san cewa wannan abin da ya ke aikatawa barna ne, amma bai sa ya saduda ba. da bakinshi ya fadi cewa:

“Na yi wanga kidi an kwashe kanti, ba a rage ko sisin kwabo ba; na yi kidi an gargade garke ba a raga ba; na yi wanga kidi an yanke dattijo, an kashe dan yaro matashi, na yi wanga kidi an yanke Mace; an kashe mai karfi ina kusa.”

Wannan kenan. Haka kuma akwai wasu karin wuraren da Gambu ke fitar da barna a bayyane. Kamar inda ya yiwa kanshi shaida da cewa:

“Ni ka gami bayi ka zamba, arna ka ta’adi ni ka laihi. Ni ka iske barayi lahiya lau, ba su nihin sata da rannan. Sai in jinjina ganga in zuga su, su tai su bido kayan mutane.”

Akwai lokacin da Gambu ya tarad da wani barawo wanda bai da niyyar yin sata, sai ya ce da shi:

Wa kaka shakka gani ga ka? Dauri kaka shakka ko ko kashewa?

Sannan muna iya ganin yadda wannan mutum ya rika hana barayi su tuba su bar aikata wannan barna. Kamar yadda ya fadi bayan ya dawo daga aikin hajji. Ya ke cewa:

“Mi arranar barin su (Barayi)? Yaushe an ka yin sata can kasar Makka inda adda Annabi balle nan banza da wohi.”

Wani karin ta’asar da Gambu ya yi shi ne yadda ya ke ba barayi lagon yadda za su aikata barnarsu cikin nasara tare da karin karfin gwiwa ga wadanda ba su yi nisa a harkar sata ba. A wata wakar da ya yi wa ‘Sani Koko’ wanda ya shahara da yin sata da bindiga. Gambu ya ce:

“In ka ishe mai kudi kwance sharkat. Kar kai mai sata ya na kwana. Jijjigarshi. Tassai. In shege ya tada kai nai. Tare bakin shege da bindiga. Ce in ba kurdi ba ran ka. Nan shi ka nuna ma inda duk su ke, ba shi musawa.”

Idan barayi suka aikata satarsu hujjoji sun tabbatar da cewa akwai kaso na musamman da suke ba Gambu. Amma don bayar da tabbaci, ga abin da Gambun yake umurtan wani kasurgumin barawon tufafi mai suna ‘Dan Inna Bagudo’:

“Bani riga, Dan-Inna Riga. Ko ta uban wa dauki bani. Akwai ni da tsoho mai rine mani ba ganewa za a yi ba.”

Wadannan ‘yan baituka da na kawo sun nuna yadda Gambu me wakar barayi ya yi amfani da waka wurin ingiza barayi su yi sata, sannan kuma yadda ya yi ta nuna alakarsa da wadannan mabarnata, akwai ma wuraren da yake fadin shi da barayi tafiyar duk daya ce. Yanzu kuma zan yi kokarin fito da irin ta’asar da Gambu ya yi wurin ingiza saba ka’ida.

Tun asali a kasar hausa ba a kaunar wadanda ke saba ka’ida, akwai ma karin maganar hausawa da ke cewa; “A na Sha’awar dan banza, amma ba a so nai.” Ma’ana mutane na sha’awar su ga a na saba ka’ida amma babu wanda ke son ya haifi me saba ka’ida. Amma shi Gambu baro – baro ya ke cewa:

In ka taba ganguman nan yanzu sai nai maganar banza da wohi. Ni da rana kamar Malam, da daddare kau nahi mai tsari sakarci.”

“In na shiga jirgi daga garin Dole in zani Lolo, sai kaga mata nata tabi, ga Gambu mijin Kulu…Dogo mijin kulu Gambu da iska mai kashewa.”

“…Arna ka giya arna ka shanta. Hausawa karanbani ka jan su. Bakambare ni ke. Mu adda giya mu muka gaje ta. Mu am arna masu burkutu; mu ar arna masu duma; mu ka sarbi. Mu a arnan Roko tun dadewa. Mu akka giyar kwakwa ta bammin. A debi giyar kwalba a koshi. Ga sarbi nan ba’a taba ba. Sarbi zandarmar giya ta. Bulala taka wa mashayi.”

Tafiya ta yi tafiya, yanzu kuma zan so na lalubo irin sabawa addini da ke cike da wakokin Gambu. Ba wai kawai sabawa addini saboda ya na yi wa barayi waka ba, a’a, har ma da irin kalaman da ya ke amfani da su, sun ci karo da addini. Bari mu ji abin da Gambu ya fadi da bakinsa:

“Mutai gidan Dikko in ci haramum in raga musu.”

Bayan da ya je gidan Dikko din domin ya kai kukan cewa ba shi da ragon da zai yanka domin yin layya. Sai ya fara waka ya na cewa:

“….Dikko ya gama sallah ya yi zaune, ya kama mugunyar tasbahar nan da ba neman lada a ke ba a na ta bidar kayan mutane.”

Haka kuma Gambu saboda tsabar wauta da sabawa addini akwai wurin da ya ke cewa:

“Ba azumi nika wa gudu ba, yawan sallan nan yau da gobe. Ba salla nika wa gudu ba, yawan dukin nan yau da gobe, bashi barin mai rai da wando.”

Sabon Allah da kauracewa koyarwar addini ta bayyana kuru – kuru ne a wakar da Gambu ya yiwa ‘Alu’ wani shahararren dan caca. A cikin wakar ya na ba Alu din shawara ne kamar haka:

“Alu..in aza ka ga hanyar da baka tsira gobe. Ali ga wani mugun wuri da zan gwake ka. Ka dai aje salla Ali ka bar dukawa. Ni mai kidin ka ban alwalla. Kai baka yin attahiyatu fatuha ta bace ma.”

A wata wakar kuma Gambu ya na yiwa Allah izgilanci ne da raini. Amma kuma sai ya ke neman ya waske. Ya na kokarin yin tuhuma ne. ga abin da ya ce:

“Ba Allah nika wa tambaya ba. Wai laihin mutuwa daukar barayi, ta bar mai kurdi lahiya lau. shin Allah missa hakan ga.”

Ko a iyaka nan na dasa aya a wannan nazari, za a ga yadda na tsakuro wasu munanan abubuwa a cikin wakokin Gambu, wadanda kuma ba iyakarsu ba kenan.

Babu wani abin burgewa da Gambu balle wakokinshi. Babu wani abin burgewa ga ire – irenshi da dangoginsu, saboda saurarensu na haifar da kangararru da mabarnata ne a cikin al’umma. Sauraran irin su Gambu akai-akai na iya yin tasiri ga dabi’ar mutum, idan bai bi a hankali ba, sai ya fara sha’awar kwatanta baitukan mabarnacin a aikace.

Exit mobile version