Connect with us

LABARAI

Marigayi McCain Tsayayyen Mutum Ne, inji Saraki

Published

on

Shugagan majalisar dattijai, Dakta Abubakar Bukola Saraki, ya mika ta’ziyyarsa a kan rasuwar marigayyi Sanata John Sidney McCain, Sanata a majalisar dattijai na kasar Amurka, ya na mai cewa, McCain abin koyi ne ga dukkan masu harkar yin doka a fadin duniya.
A wata sanarwa da mai ba shui shawara a kan harkokin watsa labarai, Yusuph Olaniyonu, ya sanya wa hannu, Saraki ya jinjina wa McCain, kasancewarsa soja dan kishin kasa kuma dan majalisa mai dinbin masaniya a harkokin aikinsa.
“A matsayinsa na dan majalisar kasar Amurka, John McCain, ya kuma kasance soja, kuma kawararren dan siyasa wanda za a dade ba a maye gurbinsa ba a harkokin siyasar Amurka dama duniya baki daya.
“Tsayuwarsa a kan harkokin siyasa da iya tafiyar da jama’a ba tare da nuna bambancin siyasa ba yana nuna cewa shi mai cikakken kishin kasa ne, za ci gaba da tunawa das hi a matsayin dan takarar shugabancin kasar Amurka da kuma gudumnawar daya bayar a lokacin yakin Betiman da aka yi shekarin baya.
Shugaban majakisar datijai ya mika ta’aziyyarsa ga al’uma da gamnati kasa Amurka gaba daya a bisa wannan baban rashin.

Advertisement

labarai