Connect with us

LABARAI

Marigayi Sa’in Bichi: Hakimin Da Ba Ya Kwana Da Kudi

Published

on

Marigayi Sai’n Bichi, Alhaji Wada Waziri shi ne tsohon Sa’in Kano Hakimin Makoda. Kazalika, Sain sabuwar Masarautar Bichi na farko bayan da Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya canza wannan tahiri ta hanyar bunkasa Masarautu biyar, wato Masarautun Kano, Rano, Karaye, Gaya da kuma Bichi, wacce Marigayi Wada Waziri ya zama Sainta na farko, kuma Hakimin Danbatta a wanan Masarauta ta Bichi mai dumbin tahiri.

Hakimin na Danbatta, wanda ake yi wa lakabi da Kwamared Wada Waziri ya taba kasancewa a matsayin Shugaban Kungiyar Kwadago na farko a tarihin Jihar Kano, sannan gogaggen Ma’aikacin Lafiya kuma masani a harkar Muhalli. Shugaban da ya jajirce wajen tabbatar da doka da oda kan sha’anin tsaftar gari, wanda kuma ya yi fice tun yana Ma’aikacin gwamnati, kafin ya kai ga zama Basarake. Duk dai da cewa, ya gaji Sarautar daga zuriyar Danbazawa.

Baya ga gwagwarmayar aiki da siyasa, Marigayin yana daya daga cikin Dattawa masu fada  a ji a Jam’iyyar PDP. Kazalika, da gudunmawarsa a kafa Jam’iyyar PDP a Gwamnati Jihar Kano da kasa baki-daya a shekarar 1999. Sannan, ya yi aiki da Gwamnatin Janar Muhammadu Buhari, wacce ya karbi mulki daga hannun Alhaji Shehu Shagari a shekarar 1983 zuwa 1985.

Marigayi Hakimin Danbatta, Sa’in Bichi shi ne wanda talakawan da yake jagoranta suka yi masa kyakkyawar shaidar cewa, baya taba yarda ya kwana da kudi matukar talakansa ya zo gabansa ya gabatar masa da tasa bukatar. Ma’ana, indai har talakawansa na cikin halin matsi ko takura, Sa’in na Bichi yana kokarin warware musu wannan matsala iya gwargwadon iyawarsa.

 

Dakta Ali Musa Hamza Burum-burum, kwararren Likita ne a Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, kuma tsohon Sakatare a Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano, Kazalika tsohon Shugaban Karamar Hukumar Tudun Wada ya bayyana cewa, rashin Sa’in Bichi ba karamin rashi al’umma suka yi ba. Domin kuwa a cewar tasa, sun yi aiki da shi sun kuma karu da iliminsa kwarai da gaske. Don haka, rashinsa rashi ne na kowa da kowa a Jihar Kano da ma kasa baki-daya.

Har ila yau, shi ma Alhaji Haruna Isyaku Makoda, Garkuwan Sa’in na Bichi ya bayyana cewa, bai gaji Sarauta ba amma daga gidan Malanta ya fito, kuma shi ba mai kudi ba ne, amma zaman lafiya yasa aka kira shi aka yi masa wannan Sarauta ta Garkuwar Sa’in Bichi. Sannan kuma a cewar tasa, sun kai shekaru sama da 45 suna zaune da Sa’in Bichi lami lafiya, tun ma yana Ma’aikacin gwamnati kafin ya shiga harkokin siyasa.

Haka nan a cewar Garkuwar, ya koyi abubuwa da dama daga wurinsa wadanda suka hada da yawaita yin alhairi ga kowa da kowa, sannan baya taba wulakanta kowa babba da yaro. Yana kuma rike ‘ya’yan ‘yan’uwa da marayu kamar yadda yake rike ‘ya’yan cikinsa, babu wani banbanci. Kazalika, Sa’in Bichi yana karbar nasiha da gaskiya daga ko’ina ta fito.

Shi kuwa wani makusanci, da kuma Wazirin Sa’in Bichi Alhaji Abba Wada Waziri cewa ya yi, Sa’in Bichi ya koya musu abubuwa da daman gaske day a hada da hakuri, zumunci, haba-haba da jama’a tare da kyautata musu da sauran makamantansu.

Hakan tasa ya zama wajibi mu rike zumunci da hakuri da juna, hada kan ‘yan’uwa, taimakawa al’umma, Abokan arziki wadanda muka sani da wadanda ma ba mu sani ba. Saboda haka, ya zama wajibi mu jajirce da rokon Allah wajen nema masa rahama da kyakyawar makoma, Allah Ya ji kan sa Ya sa ya huta.

Sain na Bichi dai ya rasu yana da shekaru 87 a duniya, ya kuma bar mata biyu da ‘ya’ya 7 da kuma jikoki masu tarin yawa. Sannan, an samu mahalarta jana’izarsa da kuma taaziya daga sassa daban-daban na kasar nan da ma sassan duniya. Kazalika dan nasa Abba, ya yi godiya tare da yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da Mataimakinsa da kuma sauran daukacin ‘Yan Majalisar Kano da na kasa, da Shugabaninsu baki-daya.

Haka nan, da Masarautun Kano, Rano, Gaya, Karaye da Bichi da kuma sauran daukacin kungiyoyi da al’ummar Nijeriya da wajenta baki-daya, wadanda suka hada da Kasar Ingila, Jamani, Masar, Saudiyya da dai sauran makamantansu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: