Muazu Hardawa" />

Martabar Dajin Yankari Ta Farfado A Idon Duniya –Habu Mamman

Gandun dajin yawon shakatawa na Yankari da ke cikin Jihar Bauchi na daya daga cikin gandun daji da ya  shahara a Nijeriya da duniya baki daya yadda mutane da dama suke zuwa domin hutawa da kuma yin tarurruka na yau da kullum ko mitin da bukukuwa da sauran hidimomin yawon shakatawa.

Wakilinmu a Bauchi ya jima yana ziyartar wannan waje don duba yadda lamurra ke kasancewa a gkndun  dajin Wanda a halin yanzu gwamnatin jihar Bauchi ta sanya ragamar gudanar da wannan daji a hannun Injiniya Habu Mamman Babban mai tallafawa gwamnan jihar Bauchi Barista Mohammed Abdullahi Abubakar kan lamuram inganta dajin na Yankari, Wurin da a halin yanzu ke samun maziyarta daga sassa daban daban na Nijeriya har da kasashen ketare.

Injiniya Habu Mamman ya bayyana cewa tun daga lokacin da ya karbi ragamar gudanar da gandun dajin na Yankari ya himmatu wajen neman abokan hulda yadda suke bani gishiri na baka manda tare da bayar da rancen abubuwan da ake bukata don gudanar da lamurran gandun dajin. Da sannu har aka wayi gari masu tallafawa sun amfana an biya kowane abokin hulda abin da ya zuba don tallafawa gudanar da dajin. Yanzu an kai wani matsayi da gandun dajin ke rike da kansa ta hanyar kasuwancin da ake gudanarwa har an wayi gari wajen na samar da kudin shiga wa gwamnatin jihar Bauchi.

Injiniya Habu Mamman ya kara da cewa a baya idan mutum ya ziyarci gandun dajin sai ya jira Kafin a wanke mayafan gado a gyara daki don ba maziyarta da suka zo gandun dajin na Yankari  daki don zama na tsawon lokacin da mutum ke so. Amma yanzu kpmai ya inganta yadda hukumomi da dama ke zuwa dajin don yin mitin da tarurruka. Haka suma mutane masu bukukuwa  da son hutawa suna zuwa dajin don samun yanayi mai kyau Wanda ya yi kama da na kasashen turai da duk wani gandun daji da ya yi suna a duniya.

A halin da ake ciki dajin Yankari na shirin gina filin jirgin sama wanda za a rika amfani da wasu kamfanonin jiragen sama don yin zirga zirgar dauko baki daga filin jirgin saman Bauchi zuwa Yankari da komawa da su madadin tafiya a mota daga cikin garin Bauchi zuwa dajin kimanin kilomita 120 sai a samu sauki ga masu bukatar hakan. Wadanda kuma suke da bukatar dauko jirgi daga ko wani wuri suna iya zuwa kai tsaye da kowane irin jirgi madaidaici su sauka kai tsaye a harabar gandun dajin.

Har wa yau Injiniya Habu Mamman ya bayyana cewa gandun dajin Yankari na kunshe da wurare na tarihi wanda ya kunshi gidajen mayaka na mutanen da wadanda suka fafe duwatsu suka yi kogo suka zauna a ciki shekaru aru aru, da rijiyoyi irin na mutanen da tare kuma da kayan tarihi wanda ya shafi dajin da dabbobin da suke dajin da yadda ake gudanar da dajin da tarihin dajin da na wadanda suka assasa shi.

Bayan haka akwai wurare na wanka da ake kira Wikki spring water ruwa ne da Allah ya halitta yana bubbugowa yana wucewa ba dare ba rana kuma ko mutane nawa na wanka a ciki. Wannan ruwa na wikki shine ya ratsa Iya gandun dajin ta kowace kusurwa yana zagawa  shi dabbobin da ke cikin dajin ke sha suna rayuwa a kowane Lokaci.

Habu Mammman ya kara da cewa Yankari ta kasance a karamar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi amma ta shiga har cikin jihohin Arewa maso gabas musamman Gombe da Taraba da Adamawa har ya shiga kasar Kamaru har zuwa wasu kasashen tsakiyar Afirka. Kuma dajin Yankari na kunshe da dabbobin daji kala kala kama daga giwaye da rakumin Dawa da karkanda da zaki da damisa da gwammaza da birrai kala kala wadanda duk Wanda ya shigo dajin har ya kammala zamansa yana makobtaka da wasu daga cikin dabbobin musamman birra. Kuma abin mamaki dabbobin daji a Yankari basa cutar da mutane ko an gansu lokacin da aka shiga dajin don kallo a cikin motocin da dajin ya tanada haka kowa zai gama shawagin sa cikin nishadi ba tare da barazana ba ya koma masauki.

Gandun dajin Yankari na kunshe da tsuntsaye kala kala wasu ma na fitowa ne daga gandun dajin wasu kasashen duniya su zo Yankari a yanayin da suke bukata daga bisani kuma su sake komawa Inda suka fito.

Bayan haka dajin Yankari na kunshe da itatuwa na bishiyoyi da wadanda ba bishiya ba da ciyayi kala kala da furannin kallo musamman a lokacin damina da sauran lokuta. Haka kuma akwai halittu kala kala wadanda ke da ban sha’awa. Kuma akwai gidaje na kwana da dakuna harma da dakunan kwana irin na dalibai saboda wadanda suke zuwa da yara Yan makaranta don kawo ziyarar gani da ido wannan wajen.

Shugaban gandun dajin Yankari injiniya Habu Mamman ya bayyana cewa tsarin da suka yi ya kara yawan masu ziyartar wannan daji don hutawa ko gudanar da hidimomin yau da kullum saboda an tanada wurin mataki mataki Iya kudin ka iya shagalinka. Bayan haka suna ragin kudi wa dalibai da kananan yara da wadanda suka zo daga wurare masu nisa don su ji dadin dawowa sake ziyarar dajin a kowane Lokaci.

Exit mobile version