Connect with us

Uncategorized

Martani: Ban Ci Kudin Marubuta Ba – Fadila Kurfi

Published

on

Kamar yadda na yi alƙawarin yin jawabina. Da farko zan fara magana game da Initiating Taron Ranar marubuta.

Wannan a bayyane yake cewa na yi initiating, amma hakan ba yana nuna na ƙirƙira domin kai na bane na yi ne don marubuta gaba ɗaya kuma Alhamdlillah kwalliya ta biya kuɗin sabulu an yi taron karo na biyu lafiya sai abun da ba za a rasa ba.

Kuma na yi ne domin kishina da Rubutu da Marubuta. Idan ba ku manta ba har a gaban Gwamnan Kano Chairman Yaya Ado ya tashe ni ya yi bayani a gaban Gwamnan har ya ke cewa “ni ce ƙarama, amma ni na ƙirƙiro wannan taro”. Akwai jaridu da dama da suka buga hakan kuma kun san hakan, Tarihi ba zai manta da wannan ba, kamar yadda duk da laifin Allantaka da Fir’auna ya yi tarihin bai manta da shi ba, haka su Abu Jahal da Abu Lahabi da su ka zama sahu na gaba wajen nuna ƙiyayya ga fiyayyen halitta. Har yau tarihin kafuwar Musulunci sai an ambace su. Tushiya mafarin dawa.

Ba na jayayya da duk yadda za a mayar da Taro ko sunan taro, kuma zan yi fatan alheri na shiga a dama da ni kan dukkan wani abu da zai kawo cigaban Rubutu da Marubuta, idan kuma hakan bata samu ba zan janye gefe na yi fatan alkhairi.

Tarayyar marubuta ba ta siyasa bace kar ku yi ƙoƙari haɗa biyun, ko kuma wasu su yi amfani da ku domin yi ma wasu yarfen siyasa, don gobe ake wankan dare.

Game da magana ta taron Katsina kamar yadda wasu daga cikin ‘Yan kwamitin su ka faɗi, hakika na sha kujuba kujuba da zarya wajen ganin tallafi daga gwamnati ya zo hannu, kuma ga al’ada babu laifi mutum ya ƙarɓi percentage a duk wani abu da ya zama ya sha wahalarsa. Idan ba ku manta ba, kafin kuɗin gwamnatin su zo, mun shiga lungu da sako wajen ganin mun tabbatar da taron da kuma fita kunyar mahalarta taron, musamman a abin da za a ci a sha a wajen taro, a rubuta na godiya bayan taro har kama sunayen na yi na wanda suka tallafa aka samu abinci da basusuka, kullum tsaye mu ke ba dare  ba Rana wajen nemo kuɗaɗen da za mu yi taro. Alhamdulillah  kuɗi sun samu kuma mun gabatar da taro kafin na gwamnatin su shigo hannu sai abinda ba a rasa ba na basussuka.

Na shiga na fita bayan kowa ya naɗe hannunsa an barni daga ƙarshe na fitar da kuɗi, kuma idan za a cire 30% na 5M nawa ne? Amma duk na haka na rufe idanu ban ɗauki hakan ba, NI BAN CI KUƊIN KOWA BA NA ƊAUKI MA FI ƘASƘANCI DA GA PERCENTAGE ƊINA NE, wanda kuma a shirye nake aje ko ina, marubuta na mora masu da ƙarfi da tunani da ƙwazo na, kuma duk abin da kuka yi na san za ku iya, da yawa wasu hassada ce kawai.

Ban ganin laifin duk wanda ke ganin an yi kuskuren ko ba daidai ba. Duk ɗan Adam tara yake bai cika goma ba, kuma duk wanda ke wajen nan zai iya yin abinda zai zama kure ko laifi tunda duk cikinmu ba ma’asumi sai wanda ubangiji ya kiyaye.

Ga zatona za a duba gaba a duba baya. Za a duba irin ƙoƙarin da mu ka yi, da kuskuren da mu ka yi, a ɗora bisa mizani.

A karshe duk Wanda ya ke ganin na saɓa ma sa ina ba shi haƙuri amma ni ban ci kuɗin kowa ba.

Kuma a shirye nake mu je duk inda za mu, kuna kwance haka muka yi ta wahala muka ciyar da ku tsawon kwanaki muka ba ku muhalli duk da haka kuka shiga media kuna tsine mana to wannan ma ban yi mamaki ba na san za ku iya, kuma wlh Ciki da gaskiya, yarfe ko ɓata suna baya tasa irin komai, ina da haƙƙi kan percentage ɗina duk da adalcin da na yi na ɗaukar mafi ƙasƙanci ba bu mamaki ai.

Abubuwan da ku ke yi ai harda yarfen siyasa, wasu na amfani da wannan damar domin su ci fuskar manya ne kawai. Nagode kwarai.

 

Fadila Kurfi ta rubuto ne daga Katsina
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: