Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home TATTAUNAWA

Martani Ga ‘Yan Biyafara: Idan An Raba Nijeriya Sai Me? – Ustaz Usamah

by Tayo Adelaja
June 21, 2017
in TATTAUNAWA
6 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Za a iya cewa a kwanan nan yakin cacar baki ya barke a tsakanin wasu matasan Arewa da na Kudu kan raba kasa. Wakilinmu, ABDULRAZAQ YAHUZA JERE ya tattauna da Imam Ibrahim Auwal don jin yadda ta bangarensu suke kallon lamarin. Ga firar:

Masu karatu za su so Malam ya fara da gabatar da kansa…

Wa bihi nasta’iynul hamdu lillahi wa kafa wa salamun ala ibadihil lazhi nasdafa. Farko dai sunana Ibrahim Auwal amma an fi sani na da Usama. Ni ne Imam ‘National Assembly, Zone B Moskue, Apo, Abuja’.

Kuna gudanar da harkokinku a Babban Birnin Tarayya Abuja, mene ne za ka bayyana wa masu karatu dangane da Nijeriya a yau?

Sha’anin Nijeriya abu ne mai fadi. Amma a yau babu wani abu da yake ci mana tuwo a kwarya kamar hayagagar da wasu zauna-gari-banza a Kudu ke yi kan a raba Nijeriya. Suna ta cin mutuncin mutane saboda sun ga an ja baki an yi shiru. Duk abin da aka ce an yi daya, an yi biyu, an yi uku mutane suna ta hakuri basu ce komai ba, to idan suka tashi ba da amsa sukan yi ne da karfi. Mutum ne ya zage ka sau daya, sau biyu kuma duk lokacin da ya yi sai kowa ya yi dariya, kana hakuri wata rana idan ka tashi ko ba ka yi duka ba, tabbas za ka rama zagin nan.

Tun a tarihi idan ka bi daga lokacin da aka samu ‘yancin kai za ka samu su ne suka ci amanar mu ‘Yan Arewa. Daga cikinsu akwai wadanda aka sa a soja kuma suna aiki a gidan Sardauna da Tafawa Balewa, basu da shamaki a gidansu; suna shiga ko ina. Amma su ne suka jagoranci raba su da duniya. Kuma har yanzu wannan bai zama darasi ga mutanenmu ba, domin galibin gidajenmu ire-irensu ne muke dauka su yi mana aiki. Idan ka dauki National Assembly, ‘yan majalisan da aka zaba daga Kano, Sakkwato, Katsina da sauran su na Arewa da ake ihun matasa basu da aikin yi, za ka iske galibin ma’aikatan da ke aiki a ofisoshinsu ‘Yan Kudu ne. Amma su ka je ka bincika, ba za ka taba samun nasu sun dauki ‘Yan Arewa ba.

Manfetur din da suke ta fasa mana kai da shi, da arzikin Arewa na noma ne aka gano shi har aka fara hakowa. Kenan babu wata fankama da za su yi mana. Mutum ne yake da abu a gidansa amma bai sani ba, ka zo ka taimaka masa ya gano kuma yana amfana da shi, ai komai butulcinsa ba zai ce kai makiyinsa ba ne. Idan bai saka maka ba ai ba zai zage ka ba. Toh haka muke da su.

Ba ka ganin tunda a yankinsu ne abin yake, watakila suna neman karin cin gajiyarsa ne a matsayinsu na ‘yan kasa?

Ai dukkansu da suke tada jijiyoyin wuyan nan hatta su kansu ba su da tabbas din cewa su ‘Yan Nijeriya ne. Don kamar yadda Turawa suka biyo ruwa suka zo, haka wasunsu suka yi har suka yada zango a nan inda suke. Har kuma gashi yanzu suna ganin sun yi kaurin wuya suna hura hanci tare da ikirarin cewa dukiyar Nijeriya tasu ce. Ka bi tarihi ka gani, asalinsu ba ‘Yan Nijeriya ba ne. Misali, ka dauki Dokubo Asari, da ya samu abin da ya samu a Nijeriya ina ce can kasar Afirka ta Kudu ne ya je ya giggina makarantu? Meye ya yi a Nijeriya? Ya shimfida abubuwansa ne a can domin koda ya hada fitina a Nijeriya yana da inda ya gina zai gudu. Duk wani cikakken dan kasa kokari yake idan ya samu arziki ya gina kasarsa amma ba ya kai waje ba. Don haka duk masu neman Nijeriya ta rikice ba ‘yan kasa ba ne.

Idan ba a manta ba, harin bom na farko da aka kai a kasar nan a Eagle Skuare su Henry Okah sun ce su ne suka kai. Amma Jonathan ya fito ya ce ba su ba ne. Idan da ‘yan majalisa da sanatocinmu sun nuna kishi a wannan lokacin babu yadda za a yi Jonathan ya kara awa biyu a kan kujerarsa ba tare da sun tsige shi ba ko kuma ya fito da hujjoji gamsassu da za su nuna cewa lallai ba su ne suka kai harin ba. Su dai wadannan tsageran har ila yau ya kwashe su ya kai su kasashen waje ana koyar da su abubuwa daban-daban da kudin kasa. Da suka dawo ka ji an ce ga ma’aikatar da aka dauke su aiki? Sun fake da wannan ne suka koyo ta’addanci iri daban-daban wanda da ‘Yan Arewa sun biye musu; ba za su taba kai labari ba. A Arewa akwai wadanda za su iya zuwa har inda suke su kamo su da hannu ba tare da makami ba. Amma mu muna biyayya ga magabatanmu, da sun ce a bari shikenan.

Yakin cacar baki ya barke a ‘yan kwanakin nan game da wa’adin da wasu matasa suka baiwa ‘Yan Kabilar Ibo su fice daga Arewa, yaya kake kallon abin?

Ai abin da ya jawo haka shi ne rashin kunyar da suke yi wai a raba kasar nan. Wai ma idan an raba Nijeriya sai me? Su ne za su fi cutuwa. Domin man da suke takama da shi nawa litarsa take? Mu kuma mangyadan da Allah ya albarkace mu da shi nawa litarsa take? Ka hada ka gani. Akwai arzikin da Allah ya yi mana a Arewa da za mu iya rike kanmu da shi. Babu abin da ya fi noma kawo arziki a cikin al’umma. Sannan idan an raba kasar za su fuskanci matsalar shugabanci irin yadda Sudan ta Kudu ta shiga a halin yanzu ko ma su fi hakan. Ba su da hakuri da imani da fawwala wa Allah lamari kamar yadda muke da su a Arewa. A kan wannan za su rika cin junansu danye.

Tunda dadewa sun buga kudinsu na Biyafara, sun yi ‘uniform’ na sojojinsu shigen irin na sojojin ruwanmu na Nijeriya. Kalli irin barnar da suka yi a ranar da suka yi bikin tunawa da Yakin Biyafara. Sun samu mutane a ma’aikatunsu sun bibbige su sun hana su aiki kuma babu wanda ya ce musu don me? Duk saboda a zauna lafiya. Wannan abin na Boko Haram da aka haddasa mana a Arewa ‘plan’ ne na raba kasar nan. An yi amfani da wasu ne a ciki amma asalin manufar tayar da rikicin shi ne a raba kasa. Kafin Boko Haram ana maganar ‘yan fashi a kasar nan amma tunda aka fara rikicin ya kazance ai an daina jinsu. Duk abin da aka yi sai a ce “Boko Haram” ne. Masu sace mutane suna garkuwa da su (Kidnappers) ba mu da su a Arewa daga can Kudu aka turo su. Galibin wadanda ake kamawa ba Hausawa ba ne na asali, yanzu ne ake kokarin cewa wasu bata-garin Fulani ma suna ciki. Ka ga mu idan aka raba mu da su ma alheri ne.

Wani zai yi mamakin yadda kake goyon bayan a raba kasar duk da cewa wasu masana sun ce idan aka raba akwai matsala…

Duniya zaman ‘yanmarina ce, kowa da inda ya sa gaba. Su a fahimtarsu kenan. Amma idan za ka bibiyi tarihin su ‘Yan Kudun da ke neman a raba kasar ai za ka ga rabawar ta fi alheri. Hatta su kansu ‘yan’uwansu da ke sana’a a Arewa ba su yarda da ‘yan’uwansu na can ba. Ko Kirsimati wani a cikin mazauna Arewan zai tafi can za ka ga yana dari-dari saboda fargabar makircin da za su iya kulla masa. Amma a nan Arewa babu tsangwama kowa a cikinsu yana zama cikin walwala. Ana sayar musu da filaye suna gina gidaje har ma idan suka yi yawa a wani wurin su ki yarda wani Dan Arewan ya zauna a cikinsu duk da cewa a Arewan suke. Misali, ba ka ga irin bala’in da aka yi ba na tsafe-tsafe da makirce-makirce don hana wani Bahaushe mutum daya samun rumfa a kasuwar kayan gine-gine ta Deidai, dan dole ne kawai suka bar shi. Ka fada mun hakan zai yiwu a wurarensu? Mun yarda a raba kasar amma duk Dan Arewa da ke Kudu ya dawo gida kar ya dauki koda tsinke daga can, su ma kuma nasu su koma kar su dauki komai daga nan, mu gani mu da su waye zai cutu?

Kai malamin addini ne, za a iya cewa wadannan kalaman sun yi tsauri da yawa a ji su daga bakinka…

Mutanen nan sun dade suna abin da suka ga dama babu wanda ya tanka musu. Kuma a yanzu ina magana ne ba kawai a matsayina na Malamin Addini ba, a’a, a matsayin Dan Nijeriya mai ‘yancin fadar albarkacin bakinsa. Ina kara fada da babbar murya, ban ga dalilin da zai sa a ce wai don matasanmu sun ce Ibo su tattara komatsansu su koma kurmin da suka fito ba a kama su. Mutane irin su Farfesa Ango Abdullahi duk a ce a kama su?. A da maganar bata dauki hankalinmu ba, amma da muka ji an ce a kama matasan nan sai na ji ni ina goyon bayan a raba Nijeriya dubu ma idan za ta rabu. Da suka samu mulki, sun kori mutanenmu a aiki, amma da wannan gwamnatin ta Shugaba Buhari ta zo ba ta yi musu haka ba. Har yanzu akwai mutanen da Jonathan ne ya nada su kuma Buhari bai kore su ba don dai a tafi tare a matsayin Nijeriya daya ce. Amma duk ba su ga haka ba. Babu wani abin da Dan Arewa zai yi a wurinsu ya nuna bajinta. A zamanin Jonathan aka sace ‘yan matan Chibok, ba a gano su ba sai a mulkin Buhari ka taba jin sun yaba da abin? Tsaron da muka samu sun taba yabawa?

Mece ce maslaha a halin yanzu?

Masalaha ita ce su yi ma kansu kiyamullaili su daina tada zaune tsaye a zauna lafiya a tafi tare. Su tuna cewa tunda Nijeriya ba ta rabu lokacin Jonathan ba sai dai su yi hakuri. Domin duk wasu shika-shikai na raba kasar nan sun tabbata a lokacin amma ba ta rabu ba.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Osinbajo Zai Gana Da Shugabanni Daga Arewacin Nijeriya

Next Post

Kasashen Waje: An Nada Yarima Mai Jiran Gado A Masarautar Saudiyya

RelatedPosts

NIRSAL

Shugaban ‘Yan Kasuwar Arewa Mazauna Abuja, Ya Yabawa Manajan Daraktan NIRSAL

by Sulaiman Ibrahim
3 days ago
0

Mataimakin shugaban yan kasuwar na Arewacin Nijeriya, wato ‘Arewa Traders...

Mun Aminta Da wakilcin Hon. Garba Datti Babawo – Alhaji Suleiman Yahaya

Mun Aminta Da wakilcin Hon. Garba Datti Babawo – Alhaji Suleiman Yahaya

by Sulaiman Ibrahim
3 days ago
0

Hon. Garba Datti Babawo na daya daga cikin ‘yan majalisar...

Bambancin Hon Sama’ila Yakawada Da Sauran ‘Yan Siyasar Kaduna – Mai Martaba Giwa

Bambancin Hon Sama’ila Yakawada Da Sauran ‘Yan Siyasar Kaduna – Mai Martaba Giwa

by Sulaiman Ibrahim
4 days ago
0

A cikin makon da ya gabata ne wakilinmu IDRIS UMAR...

Next Post

Kasashen Waje: An Nada Yarima Mai Jiran Gado A Masarautar Saudiyya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version